Chapter 120
Chapter 120
A falonsa na waje ya tarar da shi bisa al'adar sa na zama ya gana da iyali, baya tashi sai 8 sai ya shiga ya kwanta zuwa goma sai ya tashi ya karya. Ganin da Alh yayi Mk na bu'katar yin magana da shi ya sa ya sallami iyalinshi, ya ce su basu wuri. Bayan sun sake gaisuwa. Mk ya sunkuyar da kansa kasa ya ce "Dama zuwa na yi, na fa'da maka, ina son kaje wurin Baffah ka tambayar mini auren Sa'adatu". Alh Isa ya yi shiru, yana jin wani irin bacin rai na taso masa. Mk ya sake yin kasa da kansa yana sauraronsa, amma tsawon lokaci bai ji Baban ya yi magana ba. Ya dago sai ya ga Alh yana goge hawaye a idonsa. A sanyaye Mk ya ce "lafiya kuwa Baba? Subhanllah! Ban san a cikin damuwa kake ba dana bari har ka samu nutsuwa". Sai lokacin Alh ya nisa cikin rawar murya ya ce "Takaicin yadda wannan ranar ta riske ni ne, Ni ka'dai babu mahaifinka, domin da yana da rai da bulala zansa na zane maka jiki don in tabbatar maka har yau din nan ina maka kallon yaro dan karami da bai kai yaronka Kabiru ba! na kuma ganar da kai irin isar da na yi da kai, don na lura ka manta. Amma tunda bashi da rai ai dole na yi ta ha'kuri da duk cin kashin da kuke mini tunda na san idan shine na mutu na barshi ba zai fita a cikin sha'anin ahalina ba". Hankalin Mk ya tashi, ya rasa inda zai tsoma ransa ya rarrafa jikin dattijon da girma ya sake kama shi ainun. Ya ce " Dan Allah Baba yanzu ma doke ni indai zaka huce! Ai komin girman da zanyi har gobe Ni yaro ne a gabanka dole na jira abin da zaka zartar". Hawaye ya sake zubowa Alh ya ce "Ai yanzu idan na dake ka kana iya daina zuwa wurina dan ka nuna mini abota ce kawai ta hada ni da ubanku ba jini ba, yau shekaru bakwai ina kwankwa'dar bacin ran jingine yarinyar dattijon arziki irin Malam Basiru, Ina fama da kunya da nauyinsa iri iri. Amma saboda Ubangiji ya zuba alheri mai yawa a zuciyarsa tunda nake jinyar nan da bana iya fita sosai duk juma'ah sai ya zo ya gaishe ni, ba tare da tunanin ina da halin da zan mayar masa da yarinyarsa dakin miji amma banyi ba. Ni kuma na san isane kawai ban yi ba, ka zo yin aure ka saka ni a maganar tsundum tare kuma da uban 'yar da ka saketa. Dan ya gane zan iya nemo maka sabon aure, na yarinyarsa ne ba zan gyara ba, Abin da baka sani ba na shiga lamarin aurenka ne dan kar na ji kunyar kushewa ne kawai! Sai yanzu kuma ka zo ka ce wai naje na nemar maka auranta, saboda kawai ka nuna mini amfanina a gurinka sai sadda ka so Abu akaran kanka, idan baka so ba kuwa da ni da wadda baka sani ba duk daya". Maganganun Dattijon ba karamin rikita Mk suka yi ba, ba karamin tayar masa da hankali suka yi ba. Ya kasa bude baki ya masa magana, sai ya hado kalmomi sai ya ga sun yi kadan su wakilci ba da nufin hakan ya yi ba, tsawon lokaci yana gurfane yana ta goge zufar da take yanko masa. Ya ciro wayarsa ya dinga lalubo lambar'karfi amma ya kasa saboda yadda kalaman Baba suka kassara shi, da kyar ya tsaida hankalinsa, ya samo lambar, Mahmoud! Ya na dagawa ya fara masa sababi ya dauka akan Sa'adah ne zai kira shi da sassfe, har yana cewa " Lokacin da ka rabu da ita menene ba'a fa'da maka ba akan ka yi hakuri amma baka ji ba". Murya a dusashe ya ce " Ina cikin masifa 'Karfi taimake ni ka zo ka same ni a gidan Baban Na'ibawa". A sukwane 'Karfi ya ce menene, ko jikinsa ne ya tashi?" A sanyaye sosai Mk ya ce"ka bar komai ka zo yanzu Dan Allah" sannan ya kashe wayar yana ta faman fadin innalillahi. Mintina biyar Mk ya kasa ha'kuri ya ce "Ka dubi girman Allah ka yafe mini Baba wallahi ba haka bane a Raina, amma na gamsu na yi laifi ban kyauta ba! ka mini afuwa fishin ka dafi ne. Baba abota babban al'amarine da ya wuce a kira shi da kawai, domin sai da Annabi ya jaddada mana mu ri'ke Aminan iyayen mu, mu sadar da ZUMUNTA da su domin ya nuna mana suma suna da Hakki akan mu, ina ba'kin cikin cewar da ka yi baka isa da ni ba". Alh baice komai ba, illah ajiyar zuciya alamun ya dade da abin yana cinsa a zuciya. Ya nisa ya ce "Idan ban yi hakuri ba yaya zan yi Muhammadu?" Dai-dai lokacin Mahmoud ya iso cikin tashin hankali, ya gaida Baba cikin girmamawa. Mk ya ce 'karfi laifi na yiwa Baba tsawon shekaru bakwai yake ta kallona da abin, Amma ya ce " takaicinsa daya da Baban Samira baya raye domin da a gabansa zai zane ni tamkar yadda za'a zane Jawad, shine nake so ka kawo masa dorinirka ta cikin motarka ka zane masa ni domin yanzu shi ko ya dake ni ma sai ya ji a jikinsa, tunda lafiyar lallabata ake yi, ka cire tausayi ka zane ni har sai ya ce ya isa haka". Da sauri 'Karfi ya juya mota ya dauko wata irin sharbebiyar dorina ta dukan dokinsa ce da ya mutu, shine yake ta ajiye da dorinar yana yiwa yaransa barazana da ita. Daga shigowarsa, yasa iyakacin karfinsa ya shammaci Alhaji ya zamba'dawa Mk dorinar nan, a kidime Mk ya zabura domin kuwa ba karamin kidima shi bulalar nan ta yi ba Ba dan tsananin jarumtar da ya saka a zuciyar sa ba, ba abin da zai hana ya zunduma ihun neman agaji. Alhaji ya ce "Ashha Mahmuda ai ba umarninsa zaka bi ba, ni zaka jira na baka damar yin hakan, maida bulalar ka dawo ka ji mai zance muku". 'Karfi ya fita, sai da ya ci dariyarsa mai isarsa ko banza ya rage zafin dukan da Mk ya yi wa zuciyar sa tunda amincin da ke tsakanin su ne ya haramta masa samun abin da yake so, da ya zurfafa tunani sai ya gane abotarsu ta yi karfin da zabin zuciyoyinsu ya zama iri daya. Duk da idan anbashi gida da mota akan a bashi Farida ba zai karba ba, kyan fuskarta da farinta bai zama abin burgewa a gunsa ba. Da alhini a fuskar sa ya koma falo ya gurfana a gaban Baba yana cewa "Ina rokawa Abokina afuwarka Baba, ni shaida ne akan yadda Mukhtar ya ke girmama lamarin ka". Dattijon ya miskuta ya ce " aminci na da mahaifin wannan yaron ya zarta karfin naku zumuncin domin ku da hankalin ku, kuka hadu amma ga shi nan kun zama tamkar cikinku guda! Ni kuwa tsakanin mu abota ne tun bamu wuce shekaru bakwai ba, da aka kaimu gabas almajiranci har zuwa yau din nan". Ya yi tari ya cigaba da cewa "saboda giraman abotarmu iyayen mu sai da suka zama tamkar shakikai ne duk
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157