Chapter 70
Chapter 70
macijin sari ka noke ne, idan kika ga yadda yanmata suke sintiri a gurinsa, sai mamaki ya kamaki, farar fatarsa da tsayinsa ke rudar su". Halima ta cafe da cewa "itama Gogel din ai abin da ya rudeta kenan, banda haka Ina da kamar Alh Mamman da bazan yi kukan rasa komai ba, Ina zan tsaya kula wannan mutumin, kinsan Allah Safina! da Alh Mamman ta aura Ni kaina da tuni na jike da arziki, mu ture ta Alh Mamman, zata iya cewa ya mata tsufa, matashin saurayin nan da kasuwa ta daukaka ke shi chairman din Buji ventures, shima ya sota fa". Safina tace "Ina ruwanta da tsufansa? Lokacin da Dadin mu ya auri mom Dina, ai kamar ita da Alh Mamman ne, gashi nan har yau suna tare, ta yi lub tana cin arziki, har muma muna cikinsa,kawai rashin rabo ne irin na Gogel, ga kuma rabon Jawad da kanwarsa a jikin Uncle" "Ai kuwa rashin rabo ne na yarda da ke, Allah ya rabamu da rabon wahala". Halima ta fada tana Jin takaicin rashin auran Alh Mamman. Duk zuwansu basu da aikin komai sai kushe Mk, alhalin a gidan suke zuwa suci abinci mai rai da motsi, suna ci suna kushensa, barin ranar da babu wuta ko nama a abinci, sun dinga fadin mutum kamar Mk ya kasa kunnawa matarsa da dansa 'daya janareto su ji dadi, dole sai dare, daren ma sai ya fara nisa, Allah muna rokon ka tsari daga auren matsolon namiji. Haka har lokaci ya sake ja, basu fasa zuwa ba, yanzu kuma sun dauki sarar shanye mata kayan tea ta hanyar yin Yar gullisuwa, ko sai sunci abinci, suce za su sha tea, ko cornflakes. Suka sake cusa mata karya a ranta, bada komai take amfani ba, sai kaya masu tsadar gaske, yadda take tafiyar da tsarin rayuwar ta tamkar matar attajiri ba wai 'karamin lakcara ba. Gayun ta ya 'karu, komai nata daukan ido ya ke, saboda sai zababbe, a lokacin Mk ba abin da yake so irin farin cikin ta, shi da kansa har mamakin yadda yake tsoron fishin ta yake yi, komai take so haka yake mata, kusan albashinsa da kyar yake rike su, saboda hidimnar Sa'adah, kowanne wata da Abin da zata ce, tana so, haka zai yi mata jikinsa na rawa, mantawa yake yi da hidimar kansa, daga ya sallami Hajiya shikenan zai sa Sa'adah da Jawad a gabansa. Amma duk da hakan Sa'adah bata fahimci matsanancin sonta da take yi bane, da kuma sa'a da tayi mai son kyautatawa iyali ne, sai ta fara wuce makadi da rawa, bata cika nazari kafin ta aiwatar da komai ba. Suna cikin haka Jami'ar Bayero ta fara yanka fili manya tana rabawa Malaman makarantar, a hankali za'a dinga cira a albashinsu. Mahmoud da sai a wannan shekarar ya yi aure, kai tsaye biyu ya karba, da nufin idan ya tashi ginawa ya yi gini mai yalwa. Mk kuwa fargaban karban 'daya ma ya shiga, saboda a halin yanzu, badan shagon askin sa ba da sai ya hada da bashi a wata. Mahmoud ya yi ya karbi biyu, Mk na bude bakinsa sai cewa ya yi daya zan iya karba, shima sai na yi shawara da Sa'adah, kar nazo ta 'kuntata. Mahmoud ya yi galala yana kallonsa ya kasa hakuri yace " idan nace ka bari tafi karfinka kace ba haka ba, idan nace tsoron ta kake ji ka karyata Ni". Murumushi Mk ya yi tare da caewa "kowanne namiji da yadda yake zaune da matarsa, kowacce mace da irin alherinta, da irin kuskuren ta, Ni sonta nake da dukkan alherin ta, da kuma kuskuren ta, bana jin tsoron ta, amma Ina jin tsoron fushin ta, dan haka duk abin da zan yi ,dan na samu zaman lafiya da ita zan yi". Mahmoud ya tsinci bakinsa da fadin "Hakane". Mussaman da ya tuno, yadda ta iya girki, da kwalliya, gidanta kullum a gyare, hatta Jawad kullum fes za ka ganshi, sannan tana da kyakkawar mu'amala da jama'a, dan kuwa hatta amaryarsa yabon kirkinta da gayunta take yi! iya abin da ya sani na zahiri a kanta kenan, Ina kuma ga mu'amala ta sirri tsakanin ta da Mk, sai ya tsinci kansa da rashin ganin aibun yadda abokinsa ya yi deep a soyayyar ta, ya lalace a kanta, da yadda zai siya mata suturu na makudan kudade, shi ya siyi masu sau'kin kudi ya saka. Bai karbi filin nan ba sai da ya shawarceta, tace "ka karbi biyun mana Malam". "Idan na karbi biyu fa, hakan na nufin sai mun rage wasu abubuwan, tunda za a dinga yanke mini kudi ne". "Tunda dai wataran gini zaka mini mai kyau, gashi kace idan filin biyun ne har garden zaka mini, ai sai a ha'kura da wasu abubuwan har Allah ya sa ka kammala biyansu" Ya ji Dadi har ransa, da yadda ta fahimce shi,ya karbi filaye, Mahmoud na ta masa tsiyar Madam ta bashi go ahead kenan. Shikenan sai suka canja daga rayuwar luxury zuwa tsaka tsaki, sai dai ba a dauki lokaci mai tsayi ba, abubuwa suka fara canjawa saboda yadda su Halima suke mata shaguben yadda Mk ya canja mata, suka dinga fadin ba wani fili da ya karba, yanmatan banza yake kashewa kudin, Raina ki ya yi, shiyasa ya shirya miki wannan karyar, itakuma tana gaskata su, ta kasa gane gadar zare suke yi mata. Sannu a hankali sai suka fara kushe talabijin din falonta, alokacin plasma bata yawaita ba, sai irin ta falon wato LG slim tv. Kullum Suka zo sai sunce wannan tv kamar ba gidan ma'aikacin gwamnati ba, kusan shekaru hudu amma ya kasa canja miki komai, tunda muke zuwa kullum abu daya muke gani. Idan ta kawo musu pure water, sai sunce ruwan warin nama ko karnin kifi yake yi, suna fadin freezer da zai siya ta nama da kayan miyane yake ganin asara, gara yaje ya rabawa yanmata a waje. Tun bata yarda, har maganganun suka shigeta, mussaman da ta ga falon amaryar Mahmoud, sai ta sake rikicewa, ba tare da ta yi nazarin kayan da suke rainawa, ita ba'a Mata kamar su ba. Ta fara rikice masa, ya kasa gane kanta, ya zauna yana rarrashin ta, har ya samu tace ita tibin bango take so ya siya mata. Ya rikota cikin kwantar da murya yace "ki yi hakuri zan siya, amma ba yanzu ba, kinsan dai yanzu ba cikakken kudi nake samu ba, amma da zarar naci karfin biyansu, zan siyo miki, ba sai na kammala biya gaba'daya ba, ya kara da fadin wacce kamfanin kike so?" "Sumsung" "To ki daina bata ranki akan maganar tv, mecece talabijin kuma?" Ya lallaba ta da maganar tv. sai kuma wayar Black berry ta shigo, kullum su Halima hirar BB chart, Safina kam tuni ansiya mata, yayin da Halima take fatan saurayin ta ya siyo mata. A ranar da saurayin Halima ya kawo mata wayar, suka je gidan Sa'adah suka nuna mata, Halima na fadin " kina ganin saurayi ma, da bana daga masa kafafuwa, ya fidda kudi ya siyo mini, bare ke da kullum yake hakar ki". BB chart din nan ya matu'kar gigita Sa'adah mussaman da aka tabbatar mata, sai masu irin wayar ne
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157