Chapter 123
Chapter 123
wurin su Baba umaru akan su zo, su bawa Baba Isa hakuri, sai kuma su zo wajenka, amma kowa ya ce shi ba zai zo mini ba, kunyar abin da na yi maka suke ji". A filin gurin Mk ya durkushe kan guiwowinsa ya ce "Ina sake bada ha'kuri Baffa! Ba zan ta'ba gajiya wajen neman afuwa da alfarmar kar ka kullace ni ba, kaddarar mu ce a hakan amma ba da gangan na yi hakan ba". Baffa ya dago ya ce" Tashi ka zauna kada ka 'bata rigar ka" Sai da ya nisa ya ce "kullum ka yi mini irin wannan rokon Mutari ina jaddada maka ba auren Iyah bane ya hadamu, ba kuma zai zama silar rabuwarmu ba! Yanzu kana tunanin har sai ka sake turo mini iyayen ka da na baka aure? Kawai wadda zai karbar maka ne zaisa na jira sai anzo tunda dai dole iyayenka da jini ya hada ku, sune a hakku akan ka, indai ba ina son na shiga al'amarin zumunci ba ne, ka kwantar da hankalinka ni sai na je na same su da kaina, a ko ina ni mai Nemo maka aure ne, ni so nake ka shawo kanta ko yaya ne, kasan tana yarinyarta ma cewa na yi ka nemi yardarta, to yanzu ma nemi yardarta ko ya ya ne idan ya so sai naga ta yadda zan bullo mata". Mk ya dinga godiaya yana cewa "Baffa gaskiya idan ba taya ni ka yi ba, ba saurarona zata yi ba". Farin-cikin Baffa ya kasa 'boyuwa saboda yanzu ya gamsu idan Iyah ta koma hannun Mutari zata yi daraja sabanin shekarun baya da ta koma din sai dai ta yi zaman hakuri da taka tsantsan. "Ya labarin Jawad kuwa?" Baffah ya tambaya. "Rana ita yau ne hutun su in Sha Allah". Murmushi sosai ya bayyana a fuskar Baffah har ransa yake jin kaunar Jawad fiye da ta su Khalifan Sumayya, wata'kila soyayyar uwarsa ce ta shafe shi. Ko da yake ai Mk ma na daban ne a wurinsa. Kamar da rada Baffa ya ce"tana cikin gidan dazun nan ta zo mini barka da zuwa, je ka ku gaisa mana". A kunyace Mk ya ce "Bata daukan 'kirana, har gidan Aunty Sumayya na je amma bata fito ba" Jeka dai yanzun! Ina hango ka shiga zaure zan mata waya ta fito kamar zata karbi sako". Mk ya rasa mai zai ce a duniya idan aka cire iyayensa biyu ba wadda yake sonsa yake karrama shi irin Baffan Sa'adah. A matu'kar kunyace ya ce "Baffah na gode sosai Ubangiji ya fini yabawa, in sha Allah komai Iyah zata mini zan yi ha'kuri da ita muddin rai, ina maka al'kawarin zan ri'ke ta fiye da ri'kon farko, ka bimu da addu'a". Da sakakkiyar murya Baffa ya ce " Bana jinka Mutari! Amma yau zan fa'da maka wani abu da ba wadda ya sani sai ni da ubangijin zuciyata. Iyah itace abu mafi soyuwa a gare ni, ban taba mallakar wani abu da ya fita a gurina ba, ko mutuwa na yi idan kana ayyana ina ma ina nan da ka mini kaza. Na ro'ke ka duk abin da ka raya a zuciyar ka zaka mini na kyautatawa to ka yiwa Iyah shi. Basu da 'dan'uwa namiji ka taimake ni ka zame mata miji kuma 'danuwa, ta wahala akan ka, ta yi kukan rashin ka, na ro'ke ka kar ka bari ta yi kukan ita ubanta talaka ne, amanarta nake baka". Hawayen tausayin Baffah ya kwacewa Mk ba tare da ya shirya ba, amma yasa dukkan karfin zuciya ya ce "Na karbi amana, na karba da dukkan zuciyata, zan taya ka sonta, zan jiyar da ita da'di, sai dai yau da gobe dole za'a samu sabani, mussaman da yake ita din Yar daru ce sosai. Wata'kila sai kana mata rubutun rage daru Baffah". Murmushi sosai ya yi "ya ce zungurar ta kake yi Mutari, amma yanzu ai ta girma ta yi hankali wani abin ba zata yi su ba! Jeka kar lokacin maghrib ya karaso baku gaisa saosai ba". Yana isa bai fi da minti biyu ba, ya fara jiwo takun dogayen takalmanta mai tsinin gaske, kamshin ta ya riga ta isowa. Kwalliyarta na cikin abubuwan da ba zata iya dainawa ba. Ta karaso cikin taku 'dai'dai tamkar wata hamshakiya sanye cikin Riga da skirt na atamfa kalar ruwan hoda da fari. Dinkin ya zauna tamkar a jikinta aka yi su. Farin mayafi ta sanya dan haka takalmin kafarta ma fari ne mai tsananin tsada, da Mk ya lura zai gane wanda Jawad ya sa shi siya dole ne, wadda fa'dan kudinsa a lissafin naira sai aga tamkar fariya ce zata sanya a zuba wannan ma'kudan kudin a siyi takalmi kafa daya. Sosai ta yi kyau domin ta zubawa fuskarta kwalliya, hakanan sabon kitsonta na shuku ya taimaka wurin kawata daurin dan kwalinta. A ransa ya dinga yabon kyaun halittarta. Ya dinga tasbihi da hamdalar yadda aka jefa soyayyarsa a zuciyar wannan halittar da take tsananin daukan hankalinsa, duk tsawon shekarun da ya shafe a duniyarsa bai ga wadda ta zarta Sa'a iya tsara kwalliya ba. Bai ga wadda take zuba ado iya ado ba tare da fita zata yi ba, ya fahimci tana samun farin ciki a cikin kwalliya, bata ta'ba bashi matsalar wai bai yabi kwalliyarta ba, yi take domin ta zame mata jinin jiki. Ta wuce shi tamkar bata ganshi ba, ta fita kofar gidan, ta shafe minti biyu a tsaye, yayin da zuciyar Mk take wani irin bugu, mayafin jikinta iyaka cinsa kafadarta wadda tunda ga kanta ta na'de shi, gata a tsaye skirt dinta ya matu'kar fito da zahirin surarta, ba namijin da zai kalleta ya tsaya a iya kallon sharia guda daya, dole sai ya sake yin kallon bawa ido hakkinsa. Mk ya dinga jin wani irin tashin hankalin yadda take tsaye a tiiti a hakan, anya akwai wadda ya saki matarsa a duniya amma yake dandana kudarsa kamarsa? Can ya juyo ta tana cewa" Baffa na dade da fitowa banga kowa ba" Ta juyo da nufin shigewa ta bar shi fuskar nan daure tamkar hadarin da ya gama tunbatsa. "Zo mana Dawisu sarkin ado, ni ne mai baki sakon ai". Ta yi kamar ba ta ji ba, ta doshi hanyar shigewa da azama ya sha gabanta, ya ce "kwanakin baya fa a gabana Baffa ya ce miki ko rago ya kawo ya kamata ya shiga rigarsa". Ta turo baki ta ce " Ai son rai ne yasa shi fa'din hakan, ya san komai yake so ina taya shi son abin ina kuma girmama shi. Amma kai Baffa ne yake sonka ya daukaka lamarinka ya girmamaka. Yayin da kai baka sonsa kana amfani da shi ne dan cikar burinka da zarar ka samu, zaka iya ture komai ka kunyata shi, ka cusa masa takaicin da yake fakar idon mutane yana goge hawayen ba'kin cikin ka". Idonta ya ciko da hawaye, ta shanye ta zarce da fadin " wannan karon wallahi har Baffan na shirya shayar da shi mamaki tunda baya kishina. Matu'kar Sharia ta damka mini zabin mijin aure a hannuna to ina tabbatar maka zan yi iyakacin yi na na dora hukuncin Sharia akan hukuncin Baffah. Ka rabu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157