Chapter 154
Chapter 154
kar kuma ka saba al'kawarin ni zan jagoranci zuciyarka". Ya kamu da tausayinta! Ya sani irin kayan alatun data gani an zubawa Farida shi ya sanya ta karaya. Ya matsa jikin gadon ya ru'ko hannuta ya ce "shekaru uku na yi da aure amma ba a kwace miki ni ba, sai yanzu da muke tare?" Ki daina shakku Malam 'din kine har yanzu, har kuma gobe". Hawaye ya zubo mata ta ce "Na gode sosai! Sai da safe". Ya ce ai ba zan iya tafiya ban ga murmushinki ba". Ta kuwa murmusa sosai, ya sunkuya ya yi pecking dinta yasa hannu ya shafa cikinta. Ya ce Good night and stay blessed". Ya kashe mata fitila ya fita. Ta dinga shafa daidai inda ya shafa cikin, tana Jin kaunarsa na ratsata. Ta nisa tana hakaito kayan da Mk ya siya ya zuba mata ta tabbatar duk yadda Ma'aikatar shari'a take da albashi mai tsoka, sai ta shafe shekaru uku zuwa hudu kafin iya tara kudin siyan irinsu, ta tabbatar Farida kuwa iyayenta suka yi mata. Ta share hawayenta tana Jin tabbacin ko a birnin Abuja ba za'a raina mata nata kayan ba. Satin da ya zagayo aka yiwa su Jawad hutu. A hanyar su ta dawowa ya ce "Malam". Mk ya amsa da cewa"Jawad". "Dama wannan hutun ma ka ce mini ina nake son yin hutuna?" Dariya ta kama Mk ya ce "Dama ka bari muje gida tukun". Suka wuce Gadon 'kaya Jawad ya ce "Malam zamu biya wani waje ne? Na ga mun wuce hanyar gida". Ya ce "Na manta wani file a office ne, shine zamu je na dauko". "Ok" Jawad ya fa'da a gajarce. Suka iso mai-gadi ya bude musu. Jawad ya kasa hakuri, ya ce Malam ko kun yi parking zuwa wannan gidan ne?" "Mun dawo last two weeks" Mk ya amsa masa. Farida tana wurin aiki. Kai tsaye bangaren Sa'adah ya nufa da shi, bata falo, Jawad ya fa'da kan kujera ko sandal dinsa bai cire ba. Ya ce "Wow falon nan so mashallah! Ya 'dago a zabure ya ce Malam amma ka san me nake ji?" Kafin Mk ya yi magana ya zarce da cewa! "Ina jin irin 'kamshin gidan Maman Gombe (Sumayya) sannan ina jiyo 'kamshin Mamina! Aunty ta canja turare ne ko kuwa kewar Mami da nake yi ne?". Mk ya zuba masa ido yana gasgata kaifin kwakwalwar yaron. Kafin ya bashi amsa Sa'a ta fito cikin tattausar yadin material doguwar riga bubu, ta yi kyau sosai. Jawad ya daskare a zaune, ya murtsuka idanuwansa yana son ya tabbatar ba Farida ce take yi masa gizo ba. Ya budesu sosai ya tabbatar itace mussaman da kamshinta ya sake cika gurin. Ya kuwa fasa ihu ya kwasa a guje zai wawurota. Mk ya yi hanzarin ru'ko shi ya ce "Wallahi ba zaka ka kayar da ita ba, tana fama da kanta. Da Jawad ya rasa yadda zai yi, sai kawai ya yi tsalle ya 'dane Babansa. Yana fa'din thank you world best Father! Ka cika promise, na dawo na tarar da Mami a gidanmu, thank u very much Malam". Ya sauko ya nufi uwarsa cikin nutsuwa ya rungumeta, haka kawai sai ya tsinci kansa da fashewa da kuka. Itama ta dinga hawaye. Mk ya kallesu da tarin 'kauna ya ce "To kukan kuma na menene, ban da dai kin 'bata shi da kukan shagwaba, maimakon ki hana shi sai ki taya shi kuma?" Bata kula shi ba, ta ja hannun Jawad ta zauna akan kujera shi kuma ta dora shi a cinyarta tamkar 'dan shekaru biyar. Da azama Mk ya mayar da shi kan kujera ya ce "Ban son haka! sai ya buge ki? Ai kinsan ba lafiya ne da ke ba, da zaki sun'kuma wannan 'katon yaron a cinya, garama a samo masa 'kanne da yawa, ko ke da shi kwa yarda ya girma". Tissue ta dauko tana goge fuskarsa tana fa'din "is ok, ya Isa haka". Sun dade kafin su samu kansa ya daina kuka. Sai da ya yi wanka a dakinsa da aka shirya masa da kayan katako irin na 'kasar Turkey Ya fito falon yana cewa "Dakin nan nawa ya birge ni, ya mini kyau". Mk ya tuna kayan da Farida ta siya ta zuba masa a dakinsa na gidan gadon Kaya, masu tsananin tsada, amma bai ta'ba nuna sha'awarsa ba, bare ya yaba. Ya sake hakaito a yanzu haka dakinsa na bangaren Farida ya ninka wannan 'kawatuwa, amma ya san halin Jawad sai ya fi son wannan saboda shine na side din uwarsa. Yamma liss Farida ta dawo, a ranar Sa'adah ta karbi girki. Da ke Jawad a Farin ciki yake da sauri ya je ya yi mata barka da zuwa. Sai da dare ya yi Mk ya rufe ido ya ce Jawad ya tafi dakinsa na bangaren Farida ya kwana a can. Akan dole ya tafi, Sa'a ta bishi da Ido. Washagari tun sanyin safiya ya dawo side din uwarsa haka kullum yake yi. Rannan Mk ya balbale Sa'a da fa'dan itace bata nuna masa ya dinga zama a wurin Farida. Murya na rawa ta ce "Kullum ina yi masa fa'da, ji ne ba ya yi". Yana fita ta kalli Jawad da yake rakube a gefe ta ce "Ka ji da'di, da ka janyo mini bacin rai". "Ni wallahi Mami na gaji! A U.k. ba ayin haka, kowanne yaro ana barinsa ya rayu a inda yake so, bare ni da nake so na zauna tare da uwata". Ya fa'da da bacin rai. Mk da ba nisa ya yi ba, ya juyo daukan wayarsa. Ya ji Sa'adah tana cewa "Ai shikenan tunda ba zaka dinga jin maganar da nake fa'da maka ba, idan wani hutun ka dawo kaga ba nan din na koma gidan Baffah, ai ka zauna dole a inda ya ce maka". A sanyaye ya jiyo Jawad ya ce "sorry Mami na daina, zan dinga zama, har sai na yi wanka na karya. Ya hango ta mika masa yatsa tana cewa "promise". Wato ya miko nasa yatsar su K'ulla al'kawari. Sai suka tuno masa da rayuwarsu ta baya. Wannan hutun ba inda Jawad ya je ya kwana, ko gidan Hajiyar Bichi yanzu ya'ki kwana ta dinga yi masa gorin tunda yana ganin uwarsa, shiyasa yanzu baya nemanta tamkar ba shine yake kuka idan ance ba zai kwana a wurinta ba. Haka hutunsa na sati uku ya qare, Farida da Mk suka mayar da shi. Sa'adah har ta shirya Mk ya murje idonsa ya ce ta zauna a gida ba zata je ba da Farida zasu tafi. Har sun shiga mota ya kasa tafiya ya kalli Farida ya ce a minutes please. Ya nufi side din Sa'a ya tarar da ita zaune a falo ko mayafin bata cire ba. Ya ru'ko hannuta ya ce "Na kasa tafiya sabaoda baki mana addu'a ba". Ba tare da ta kalle shi ba ta ce "Ku dawo lafiya". Ya kirata a tausashe, ta dago suka zubawa juna ido. "Fishi ki ka yi ko?" Ta kasa cewa komai. "Ki yi hakuri! Na sani kina son zuwa, amma tunda da ita muka saba kai shi da zuwa visiting bai kamata yanzu na canja ba, zata dinga jin damuwar rashin haihuwarta, sannan kema wahala zaki
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157