Chapter 36
Chapter 36
ni ba zan bayar ba." Wucewa dakin Sa'adah ta yi tana dariya tare da cewa,"Oh Innah maganar Baffa tamkar hadisi take a gunki!" "Aljannata nake nema kin san kuwa aljannar mace ta fi samuwa idan mijinta ya yarda da ita." Cikin dariya sosai Sa'adah ta ce, "Sadaqati Inna! Kin yi gaskiya In Sha Allah har a aljanna ke ce uwargidan Baffah." Dariyar ita ma ta shiga yi tana fadin, "Allah ya shirye ki Iyah" Daidai lokacin kuma waya ta hau kuwwa tana dubawa ta ga MK ne, ta amsa, ya sanar mata ya iso. Ta mikawa Inna wayar tana cewa, "Ya iso." Daki ta koma ta sake gyara fuskarta sannan ta feso turare ta fito, ta dauki tabarma ta na fadin, "Ki tashi Inna ki kintsa, na ajiye miki Hijabin da za ki saka a kan gado." Harara ta galla mata tare da cewa ba zan saka wanda kika ajiye din ba 'yar fariya! Kin yi shigarki ta burgewa, amma kin tashi kin fesa turare." Ta yi kwafa tana ayyana dauke shi za ta yi ta boye. Murmushi ta yi tare da cewa, "Take heart mom!" Sannan ta juya ta tafi. Ta isa da sallama yana tsaye yana amsa waya, ya yi kwalliya da yadin kufta kalar ruwan kasa (brown), ya dora hular da ta dace da kayan. Sosai ya yi kyau, musamman yadda sumarsa da hula ba ta rufe ta gaba'daya ba tana ta sheki alamun ta sha gyara na musamman. Ya katse kiran yana zuba mata ido sosai sai kuma ya hau murza dukkan idanuwansa, ya sake kallon ta soasai, ya bude baki alamun mamaki tsawon sakanni goma sannan ya nisa ya ce, "Sa'adah ce kuwa, ko idona ne ya ke mini gizo?" Ta tura baki tana dan murmushi tare da shagwabe fuska. Hakan da ta yi sai ta sake burge shi ya ce, "Kin canja fa! Ba ki ga yadda kika yi kyau ba, ganin ki na yi tamkar 'yanmatan Ethiopia." Da'di ya kamata musamman yadda bakinsa ya yi daidai da na Innar ta, ya lura da yadda take murmushi, ya fahimci tana son a ce ita mai kyau ce, ko ta yi kyau. Ya ce "Ki fa daina wannan shagwabar ita ma tana sani a wancan yanayin!" Ta rufe fuskarta da gefen Hijabinta, ba tare da ta iya cewa komai ba. Ya sake cewa, "Idan ba so kike na zama agwagwa ba, to ki daina yin ta a yanzu. Ki tara mini ita zuwa lokacin da za mu tsinci kanmu a dakinmu!" Ta sake rufe ido sosai tana ayyana wai shi ba ya jin kunya ne? Ganin yadda ta rufe ido ta makale a bango sai ta ba shi dariya sosai. Ya dan juya dan ganin ba wanda zai ji shi, ya yi kasa da murya ya ce, "Ba ki ji yadda na ji ba, ina ma ni kika makale ba wannan bangon ba! Kunyar nan ma burge ni take yi, komai na ki is special!" Shiru ta yi ta kasa juyowa, bare ta tanka masa, tana ji a jikinta yadda idanuwansa ke yawo a kanta. Da kyar ta bar jikin bangon ta shimfida tabarma tana cewa, "Bismillah!" Ya yi kicin-kicin da fuska tamkar ba shi ne mai walwala yanzun nan ba. Ya ce, "Ba zan zauna ba!" Ta dago ta kalle shi a kunyace ta ga yadda ya hade fuska, gabanta ya fadi, tana tunanin me ya 'bata masa rai kuma? A hankali ta ce," Tafiya za ka yi?" Ya girgiza kai sannan ya ce, "Zaman ne ba zan yi ba, ki dinga shimfida wa Honorable." Ta yi shiru tana jin fargaba na taso mata! Ta nisa ta ce, "Amma dai ai na ba ka ha'kuri, magana sai ta wuce." Da sauri ya ce, "In dai sai na zauna a inda yake zama to kuwa magana ba za ta wuce ba!" Ya juyar da kansa gefe guda, ganin yana Shirin dawo mata da yanayinsa da ba ta so na nuna ko in kula ta kalle shi ta ce "Bari na dauko maka wani abin zaman to." Bai ce komai ba, ta nade tabarmar ta shiga da ita, ta dawo da kiret din lemon kwalba mai kwari, ta ajiye ta dora sallaya a kai, kamar ba zai zauna ba sai kuma ya zauna din. Ita kuma ta zauna a kan wani dutse da ya ke zauren. Ta kalle shi ta ga bai ware ba, ta daure ta ce, "Ba don fishinka na gigita zaman lafiya ta ba, da haka zan so ganin ka kullum. yadda ba yanmatan da za su ga fuskar tunkarar ka, saboda kwarjini da tsare gida." Dariya ta kwace masa, ya nisa ya ce, "Kina da son kai Sa'adah! Ba kya son na kula yanmata amma ke ba ki kiyaye kula wasu mazan ba." Ganin ta yi kasa da kai sai ya canja maganar da cewa, "Mahmoud ya na gaishe ki" A hankali ta ce "Na gode!" Sun jima suna hira bayan ya sha ruwa, suka shiga ya gaida Inna, ya ajiye mata kudi, sannan su ka koma zauren, ba su dade da zama ba Baffa ya dawo, ya tarar da su, a kunyace, MK ya sauko daga inda yake zaune ya tsugunna ya gaishe shi. Baffa ya amsa cike da farinciki, har ya wuce sai ya dan tsaya ya ce, "Da ma kuwa ina son ganin ka, idan ka samu lokaci ka same ni." Da girmamawa MK ya amsa da Fadin, " Koyaushe ina da lokaci." Baffa ya ce "To bayan La'asar gobe idan ranmu ya kai." Sai da ya shige sannan ya koma gun zamansa, Sa'adah na masa dariyar yadda ya takure. Ya kalle ta ya ce, "Idan akwai abin da ya fi haka na kunya zan ji tunda yarsa nake so ya ba ni, ya kuma san abin da zan yi da ita!" Shike nan ya rufe bakinta ruf. Ya zuba mata ido ganin yadda ta turo baki gaba alamun fishi-fishi. Ya waske kamar bai gani ba, ya nisa ya kira ta da alamun seriousness "Sa'adah!" Ta yi shiru, sanin halinta na shariya da sanin ta ji shi ya zarce da fadin, "Magana za mu yi ta gaskiya, ki nutsu ki ban hankalin ki." "A kan kunnenki Baffa ya ce za mu yi magana, ga zatona mafi karfi ina ganin zai yi maganar idan mun shirya kanmu na turo da magabatana." Nan ma ba ta ce kala ba. Ya nisa ya sake cewa, "Kina ji na kuwa?" Kai ta daga masa alamun tana tare da shi. Ya ce, "Tsakaninki da Allah ki fada mini gaskiya don na san yadda zan tunkare shi. Mun kai lokacin da ya kamata a ce mun fahimci juna, maganar aure idan manya suka shiga ta kare fa! Ba maganar canjawa idan dai ba mayar da iyaye abokan wasa za a yi ba. So nake yi, ki fada mini da bakinki idan Baffa ya tambayi mun shirya kanmu, me zan ce masa?" Ta yi kasa da kanta ta kasa cewa komai, tsawon minti guda sannan ya dora da cewa, "Kar ki ji nauyin fadar gaskiya na yi miki al'kawarin zan fahimce ki, zan kuma fahimtar da Baffah yadda ba zai ga laifinki ba." Ta kasa bude baki ta yi magana ita kanta ba ta san me
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157