Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 106

Chapter 106

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,204 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yawaita masa cin kifi, a karanta masa cin nama mussaman Jan nama. Da kuma yawan motsa jiki da shan maganin da likita ya 'dora mai lalurar akan ka'ida, sai kuma rage kiba ga masu ita". Mk ya mika masa hannu tare da cewa"likita na gode sosai da lokacin ka da ka bani tare da mini cikakken bayanin da na gamsu, ina rokon ubangiji ya yiwa rayuwar ka albarka, ya kara maka ilimi mai albarka, ya sa sunanka ya yi fice a cikin 'kasa da waje". Babangida ya amsa da cewa "Amin Nima na ji 'Da'din yadda ka nemi bayanin likita, baka tafi kanka tsaye siyan maganin rage rad'ad'in ciwo ko kumburi ba, domin yawan shan irin waddanan magagunan na janyo ciwon ulsa da ma gazawar 'koda bagatatan, ubangiji ya bamu lafiya gaba'daya". Har wajen ofis din Dr Bojuwa ya rako Mk dan karramawa ga yayan abokinsa Akil, Mk yana ta masa fatan alheri da samun mace ta gari, tare da jinjina fasahar Babangida, yana hakaito sadda yake biyowa Akil makaranta, oh rayuwa gaibu ce, ba wadda yasan me gobe zata zo da shi. Yana tafe yana tunin bashi da matsalar gwajin rukunin jini, tunda tuni yasan Farida A.s ce yayin da ya kasance A.A basu da matsala, kawai fargabar sa daya ciwon da ta ke faama da shi ance ana iya gadarsa kenan akwai yiyuwar ta haifa masa mai irin ciwonta. Alatilas zai yi auren nan, ko dan ya nuna mata martanin soyayyar da ta wanzu tana masa ba gajiyawa amma a zahirin gaskiya kaso mai yawa na zuciyar sa da gangar jikinsa gaba'daya Sa'adah suke so, da ita suke son su rayu muddin rai, shi da kansa yasan hukunta kansa yake yi da rashinta. Yana tu'ki yana ayyano cikakken dirin jikinta bata da rama kamar Farida, duk da a yanzu ta tsiyaye, amma ya yi imani da zarar ta dawo hannunsa komai da ta rasa zai dawo mata tunda zata sami nutsuwa, ga iya girkin gargajiya tamkar Innarta, ga ga gayu, kullum tamkar mai Shirin shigaa gasar kyawawa saboda kwalliya. uwa uba ta kasance mace mai lafiya, A.A ce sannan O positive duk wadda ya san darajar lafiya ya san wadda ubangiji ya hada musu wannan nau'ikan ba karamin ni'imomin ubangiji suke ciki ba. Kalamanta na karshe ya fado masa wai idan ya sake tura mata kudi ba zai gama da uwarsa lafiya ba! Bai taba ganin inda abin arziki ya zama sharri ba sai a gurin Sa'adatu. Ba 'karamin bata masa rai wannan kalmar ta yi ba, bayan tasan ita mai laifi ce, ya tsani kaifin harshe, umm Kusan Wannan bacin ran da ta haddasa masa ya rage masa fargabar auren Farida da yake ji. Washagari asabar dai dai da 17/09 aka daura auren Mukhtar Kabir Bichi, da Farida Nasir Torondi. Daurin auren da ya samu halarta manyan mutanen na Nijer da Nigeria. Sosai aka yi hidima ta bangaren amarya, duk yadda Farida ta so ya halarci Dinner da zata yi a harabar gidansu ha'kuri ya bata, bai je ba, yana ji a ransa tunda bai yi irin wannan sha'anin a bikin Iyah ba, to yanzu ma ba zai yi ba da yake da shekaru talatin har da tara. Bangaren Iyah kuwa sai da aka daura auren ta gane Farida ya aura. Duk yadda ta so yin jarumtar boye yadda auren Farida ya bugeta kasawa ta yi, ta fito daga dakinta, daidai lokacin Baffanta ya dawo daga wurin daurin auren ya ci sabon dinki tamkar yarsa yake aurar wa. Tana tsaye tana kallonsa , sai kuma ta fara ganinsa bibbiyu, basu ankaraba suka ji tim ta zube a kasa. Dukkansu suka kai mata dauki, tsawon lokaci ana kanta har sai da aka kira Maman Ema wata kwararriyar nurse ce har ta kai mukamin metron, ita ta dinga dawainiya da ita har ta farfado, tana fa'da musu jininta ne ya yi kasa sosai adalilin rashin samun barci da kuma damuwa da ta sanya a ranta. Kwana biyun da suka biyo baya ba karamin tsauri suka yiwa Sa'adah da iyayenta ba, domin ba karamin wahala ta sha ba, har zabura take ta kwasa da gudu, gaba'daya ta gigice ta fita a hankalin ta, ba kuma komai ke damunta ba illah matsananciyar damuwa wato (Desperation). Yadda take zabura da suratai ya matu'kar tada hankalin ahalinta mussaman Inna da ta ke uwa, ansan kuwa raunin uwa akan danta. Bayan maganin asibiti har rubutu Baffa yake zama da kansa ya ke mata wadda na dangana ne da samun sukunin zuciya. A wannan lokacin Inna ta kudiri aniyar Mukhtar ko shine namiji tilo a duniya da ya hallata Iyah ta yi zaman aure da shi, to kuwa ita ta Haramta mata shi, wannan abin da ya yiwa Iyah ta tabbatar ya yi tsauri da yawa ya wuce laifinta, ta yi imanin 'yarta ba zata yi zina ko sata ko wani mugun kaba'irar da zai kasa yi mata afuwa ba, ta lura so yake ya susuta mata yarinya ya sa zuciyarta ta buga, tunda shi bashi da asara ya angwance da 'diyar masu kambun susa. Asalima Inna sai take ganin tamkar so yake ya shafawa Sa'adah kashin kaji. kuma raina arzikinsu ya yi. Kwanaki biyu suka ragewa Mk ya wuce, ya dauki Farida da hantsi suka je ta gaida Hajiyar Bichi, duk yadda Hajiya take jin dama Sa'a ya dawo da ita, ta karbi Farida da sakakkiyar fuska, yayin da Jawad ya ke ta murnar Malam ya ce zasu bishi Ingila a jirgi da wannan balabiyar Auntin. Dai dai lokacin shekarun Jawad goma. Kunyar Farida da sanyin ta yasa Hajiya ta dan rage 'kin data ke yiwa auren na su. A hanyar su ta komawa gida ta ga ya sauka daga kan titin da zai bi ta unguwar su, ya hau wani daban. Bata ce kala ba, ta zuba masa ido kawai. Bai tsaya ko ina ba sai a harabar hotel din Tahir. Jikin Farida ya yi sanyi sosai, ta shiga cikin rudani da fargaba, amma haka ta bishi, har dakin da ya riga da ya kama a safiyar yau, domin taga a aljihunsa ya fito da mukallin daki mai lamba 008. A dadare ta shiga ta zauna, shikuma ya juya ya fita, ba'a jima ba ya dawo da leda mai dauke da yougurt da gasasshen kifi, sai lemuka masu sanyi hadi da ruwa. Ka'dan ta dan ta'ba adalilin matsawar da ya mata, shi kuwa da dama yunwa yake ji sosai ya ci, sannan ya shiga ya yo wanka, ya fito daure da tawul iya kugunsa. Mk da kansa ya dinga mamakin kansa bai yi zaton zai ji sha'awar wata macen bayan Sa'a ba, bai yi zaton zai yi rawar jiki har ya kasa ha'kuri su isa Uk kafin ya tare da amaryarsa ba, amma abin mamaki jiya kwana ya yi yana juyi, rabon da ya shiga irin wannan yanayin ya manta, bai sani ba ko dan yasan bai da wadda ta halatta a gare shi ne. Ganin abin na neman kassara shi, shiyasa ya murje kunya ya je har gidansu ya daukota da zummar zai kaita ta gaida mahaifiyarsa sannan sisters dinsa na son ganinta sosai. Sanin mijinta ne yasa ba a nemi ba'asi ko fargabar fitar su tare ba, asalima kyakkawan shiri aka

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});