Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 33

Chapter 33

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Kano a kwatas din 'Yan Majalisu na Farawa. Da daddare Sa'adah na kwance a daki tana hira da Khalil, cike da nishadi take amsa wayar don kuwa tabbas tana jin son Khalil, kawai sanin ba za a masa aure yanzu da kuma soyayyar MK da ta danne tasa ne! Amma tana son sa yana burge ta ya dace da tsarinta na Luxury Life. Tana ganin kiran MK sai shigowa yake yi amma ba ta katse ba, tunda ta san shi ba wani lokaci mai yawa zai dauka yana lallabar ta ba, sai daga baya ta katse kiran Khalil bayan ta dauki excuse akan ya ba ta mintina biyar tana zuwa. Tana kiran sa ya katse ya kira ta bai mata complain din da wa take waya ba, hakan ma yasa ta sake jin haushinsa, ya tambayi lafiyarta, ya kuma sanar mata cewa gobe zai zo abokinsa na son ganin ta, to kawai ta ce, a ranta kuma tana cewa abokinsa ne yake son ganina ba shi ba. Washegarin kuwa suka zo shi da amininsa Mahmoud Karfi, wani abu mai kama da almara Mahmoud na dora ido a kan Sa'adah ya ji son ta ya cika zuciyarsa, ta zo masa a yadda yake burin samun matar aurensa ta kasance. kwalliyarta, yangarta, shan kamshinta duk sun tafi da shi, amma sai ya yi yaki da zuciyarsa ya danne ta yana nanatawa kansa MK ya wuce ya hada soyayyar mace da shi, ya tabbatar idan MK ya gane yana son ta to tabbas zai bar masa. Idan kuwa haka ne shi ne ya kamata ya haramta wa kansa wannan yarinyar da a yau ya dora ido a kanta, a daddafe aka yi hirar Mahmoud ya ba ta kyautar kudi dubu biyar suka tafi yana ta neman tsarin shaidan da zuciya da suke sake kawata masa Sa'adah. Madalla da aboki irin Mahmoud wanda yake daraja abota da kuma sadaukarwa, ba wanda zai zagaye ya yi wa abokinsa kafar ungulu ba. *BAYAN WATA UKU*. Zuwa wannan lokacin Sa'adah ta canja sosai domin ba karamin kudi Alhaji Mamman ke sakar mata ba, ta mallaki zobunan Dubai Gold a boye har guda biyu. Ta mallaki waya mai kyau Sliding 'kirar Nokia da SIM a ciki, wayar dai Inna ta sani amma zobuna ta kife ta musamman da Innar ba ta san Gold ba. Tun MK bai lura da canjawar Sa'adah ba har ya fara ankara da yadda kwallliyarta ta karu, ta daina dokin amsa masa waya, ta daina mitar rashin zuwansa, sannan dan flashing din da take masa ta daina idan zai kwana ya yini bai kira ta ba, baya taba ganin text ko flashing dinta. Duk da bai san tana da waya ba har zuwa wannan lokacin shi da layin Inna ya ke kiran ta, so yake ya mata bazata jiran fitowar results dinsu yake yi, idan har ya yi kyau, waya zai siya mata, idan ma bai yi ba dai zai siya mata. Ashe shi bai san ta kerewa rike kananun wayoyi irin wanda yake harin siya mata ba. Jikinsa ya fara sanyi don haka ranar wata Laraba ya kasa jiran Juma'a ta zo, ya shirya ya nufi gidansu da yamma. Sai dai yana zuwa ya tarar da Alhaji Mamman zaune a kan tabarma, yana tsayawa a bakin zauren ita kuma ta fito daga cikin gidan ba ta 'karasa isowa zaure ba, amma idanuwansu sun sarke da juna, bai ce kala ba ganin Alhaji Mamman bai ganshi ba sai kawai ya yi murmushin da babu nisha'di a cikinsa ya juya abin sa. Sai ta tsinci kanta da diriricewa, ta ji tamkar ta ruga da gudu ta ce masa ka dawo, kai nake fatan ace kai ne a zaune ba wannan mutumin ba, amma ba damar yin haka, a daddafe ta gaishe shi, ta gabatar masa da uzurin zazzabi take yi don kar ya ji ba dadi ne yasa ta daure ta fito. Ya gamsu a yadda ya ga duk jikinta ya saki ta yi wani iri, tashi guda, don haka ya fita ya je mota ya kwaso mata sayayyar da ya jido mata, bayan ya ajiye mata rafar yan 200 sabbi kal. Tayi godiya ta shiga gidan zuciyarta daya tunda Inna ta je cikin Unguwa yinin biki don haka ta rage wasu kayan ta boye akan sai wani zuwan ta nuna mata. Jikinta na rawa ta shiga lalubo lambar MK, amma har ta katse bai dauka ba, ta sake kira har sau uku nan ma bai dauka ba. Alkalamin *SURAYYA GWARAM* ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan, ba tare da iznin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *Fatan alheri ga* *Asma'u Sani* *Aisha Lagos* *(Mrs Dan manya)*. *Shafin na ku ne ku yi yadda kuke so da shi*. 38_39. Haka ta ci gaba da kiran har ta gaji, tana 'kiyasta adadin kiran da ta yi masa ya kai ashirin, jikinta ya mutu tamkar marar laka, zuciyarta ta cunkushe da fargaba, tasan tana son MK sosai amma a yau ta sake sanin son da take masa marar adadi ne, duk da kasancewar ba lokacin zafi ba ne sosai, amma zufa sai karyo mata take yi. Waya kuma na hannunta, tana ci gaba da kiran sa. Tunda ya bar gidansu Sa'adah Masallaci ya nufa da 'kyar ya karasa saboda yadda zuciyarsa ta daure, ba abin da yake bukata sai kadaici. Ya Jima a zaune yana ta ambaton Allah har ya sami sassauci sannan ya dauki Qur'ani ya fara karatu a fili, a hankali, duk kiran da Sa'adah ke yi masa yana gani, duk da a silent ya mayar da wayar. Bai bar massalacin ba sai da aka yi Magariba zuwa wannan lokacin ya samu saukin daurewar da zuciyarsa ta yi a dalilin kishi, ya fito daga Massalacin ke nan kiran ta ya ci gaba da shigowa ba kakkautawa. Gefe sosai ya samu ya zauna ya fito da wayar ya katse kiran nata sannan ya kira ta. Jikinta har rawa yake yi wurin amsa kiran wanda ta dade ba ta ji zakuwa da dokin amsa kiran sa ba kamar a wannan lokaci. Muryarsa ba amo sosai ya mata sallama tare da cewa, " Sorry Sa'adatu! Kin kira na bar wayar a caji ne tun dazu sai yanzu na ga tarin missed calls." Wani nauyin jiki ya kara kama Sa'adah, ta rasa kalmar da za ta furta saboda abubuwa biyu, na farko bai nuna ta masa laifi ba tunda da ban ha'kuri ya bude maganarsa bugu da kari ma katse kiran ta ya yi, ya Kira ta. Na biyu ya ambace ta da Sa'adatu rabon da ya kira ta da hakan tun lokacin suna yar tsama, ita kam ya binneta, ha'kuri za ta ba shi ko kawai sharewa za ta yi kamar yadda ya yi? Da kyar ta bude baki ta ce "Ai na dauka kana sane ka 'ki amsawa." Tana rufe baki ya ce "Ko daya to mai

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});