Chapter 96
Chapter 96
ke da asarar rashin mahaifi, amma ita Hajiya tana da Ahamad, haka nan Sa'adah zata auri wani ya iya mantar da shi a ranta, amma Jawad fa? Duk yadda yake da tabbacin Abbas da Ahamad har ma da 'Karfi baza su bar tilon 'dansa ya yi kukan maraici ba, ya tabbatar Jawad ba zai rasa uba ba, amma tabbas zai yi asarar rashin mahaifi da ba a samun biyu. A hankali ya ja motar yabi bayan su Hajiya. Tsawon lokaci yana gurfane gabanta, ita kuma ta yi 'diban karan mahaukaciya da shi. "Hajiya Dan Allah ki gafarce ni, ban san me na yi miki ba, fishin ki dafi ne a rayuwata, ki mini ha'kuri dan Allah". Karo na hudu kenan yana maimaita wannnan kalamin, ta kalle shi ta ga duk ya sake firgicewa, da gaske tasan yana tsananin gudun zuciyar ta, amma dole ta nuna masa ita ba UWA bace irin Agwagwa ba, yaranta a gaba ita tana binsu a baya. Ita kaza ce da ta ke gaba 'ya'yanta na bayanta, sannan idan ta ga 'da ya yi rashin 'da'a ta take shi ba dan bata sonsa ba sai dan ya zama nagari abin so da kwatance a ckin alumma. A raunane ta ce "Kai ne da ha'kuri da na yi laifin da zaka iya mini fishi, har yaushe ka yi motar? da zaka dauko ni ka hade mini fuska tamkar wadda ka mini alfarma, ka sani ai ni ba bakuwar mota bace, idan ana sako wadda suka fara mallakar mota a Bichi da kewaye sai ansako gidanmu. sannan tun kafin a haifeka duk inda zani a mota ake kaini, bude ido ka yi ka ga mota a gidannan bare ka mini wani iyashege". A matu'kar gajiye Mk yake fa'din "Na yi kuskure, ki yi hakuri abin ne yafi 'karfi na, ki mini uzziri Hajiya, ki sake dagewa wurin yi mini addu'a". Ya Dora hannunsa daidai setin zuciyar sa ya ce, "zuciyata ciwo take mini sosai, tana mini zafi, wataran har numfashi bana iya yi, dan Allah ki yafe mini kar mutuwa ta zo mini kina fishi da ni, zan roke ki, komai na miki, da wadda zan miki nan gaba ki dubi Allah ki yafe mini, Ina rayuwa ne kawai amma wani lokacin bana sanin me nake ciki". Tausayinsa ya kama Hajiya sosai, ta zuba masa ido tana nazarinsa.ta sassauta murya tace kana son ka warke daga ciwon da keke 'dan'dana, kana son nutsuwa ta zo maka, ka dinga sanin halin da kake ciki, kana son nutsuwar da ta yi maka tutsu ta dawo maka? Ya ri'ke hannun ta muryar sa na rawa ya hau cewa 'ina so Hajiya, bana iya barci fa, ko abinci da na fara ci sai na ji ya tokare mini a wuya shikenan sai na kasa ci, kuma ina jin yunwar". Hajiya tace "fada mini laifin da Sa'a ta maka na san shine yake neman kassara ka, rashinta kusa da kai ne yasa kake rasa gane halin da kake ciki domin kana sonta, farincikinka na 'damfare da ita ne". Bai musawa Hajiya ba domin kuwa yasan gaskiya ta fada, amma sai ya saukar da kansa 'kasa ya ce 'kaddara ce ta rabamu Hajiya". Cikin rarrashi ta ce "Ni uwarka ce, duk wadda zai ri'ke maka sirrinka a bayana yake, me yasa kake gudun abin da ka ke so da gangan?" Sai lokacin bacin rai ya sake taso masa cikin fitar hayyaci ya ke firzar da maganganu " Ina sonta sosai, Ina son na rayu da ita, komai Ina yi mata, har da wadda ya fi 'karfina yi mata nake yi, amma kullum cikin zullumi nake zaune da ita, fa'da mini Hajiya me na gaza da ban cancanci na sami kwanciyar hankali da ita ba?". "Ba ka gaza ta ko Ina ba, itama ai kullum cikin damuwar take tunda kishin rashin hankali ta 'dorawa kanta". "Yanzu fa'da mini abin da ya kawo musabbabin rabuwar dan nasan irin hukuncin da zanyi, na kuma daina zarginka da manta alheri, da kuma rashin ha'kuri". "BA KOMAI QADDARAR MU CE". Ta zuba masa ido ta ce "Ko dai Ni ta zaga ko mahaifinku ko Hajiya Babba?". A hankali ya girgiza kansa ya ce "Haba dai, ai komin tsiyarta ba ta isa ta mini hakan akan idona, na barta haka salin alin ba, sannan fa Hajiya yadda kike sonta haka take son ki, Ina mata shaida ko giyar wake ta sha ba abin da zan yi mata ta zage ku". Ta kalle shi tana tuna fa'dar gaskiyarsa tun yana Yaro yana cikin abin da ya janyo masa soyayya a zuciyar mahaifinsa. "To Ni dai indai ba wannan laifin ba, banga me zata yi ka 'ki yafe mata har haka ba". Zuciyar Hajiya ta kasa daurewa tace "ko dai kama ta ka yi da wani?" A zabure ya mi'ke yana fa'din subhanllah! haba dai Hajiya me yasa za ki yi wannan hasashen, har abada Sa'a ba zata yi hakan ba, in sha Allah ba zata yi hakan ba duk lalacewar *HALIN YAU* SA'ADATU ba zata yi hakan ba". *SURAYYA DEE* ✍🏼✍🏼. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A kiyayi ta'ba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *Fatan alheri ga* *UMM ASGHAR NOVELS*. *NOVEL ONLY GROUP*. *Da dukkan grops din da ake tura wannan labarin ake sharhi tare da fatan alheri, ina ji ina kuma godiya da fatan Allah ya bamu damina mai albarka*. *Gaisuwa ga* *Fati Eshaik(Ummu Asghar)* *Zalhatu Umar(Yayar mu)* *Hauwa Umar(Mrs Nasir)* *Zainab Abdullahi(Beneficial group)*. *Fatima (Maman Aslam)* *Aunty Ai'nau* *Hauwa'u Umar Gwaram* *Balki Sani*. *Rahma Shu'aibu Kankara*. *Kulsum Baffah Azare*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 83-84. Sosai Hajiya ke nazarinsa, sannan ta sami nutsuwa da ya kasance ba abin da shaidan ke kissima mata bane. Dan haka sai ta ce "idan kuwa hakane banga menene mai zafi da ba zaka yafe mata ba, wallahi ta gane kuskuren ta, ka bata wata damar Ina tabbatar maka lafiya lau za ku zauna". A hankali ya ce "Dan Allah Hajiya na ro'ke ki, ki bar wannan maganar, ki mini afuwa, ki kuma yi mini alfarmar daina yin wannan maganar, kawai fatana ki mini addua". "To shikenan Allah ya yi zabin alheri". Ta fa'da jikinta a sanyaye. Ta bangaren Sa'a kuwa, har lokacin tana yawan 'kiransa a waya ta bashi ha'kuri, ko ta yi text, har ta kai har makaranta ta bishi, ta tsugunna a gaban sa cikin cire girman kai, tana bashi ha'kuri, a irin haka Farida ta fa'do ofis 'din ta tarar da su a hakan, ta juya da mugun sauri tana fa'din "Sorry excuse me" Ganin da Farida da ta yi mata gurfane a gabansa ya matu'kar dukan zuciyar Sa'a, da muryar kuka ta kalle shi tace "yanzu ita ka ke so shiyasa ka rufe mini 'kofar afuwa ko?" Kai tsaye ya ce "kinsan ba haka bane ,amma idan haka zuciyar ki ta rinjayar miki to bazan 'karyatata ba! Kar ki kuma zuwa mini nan, idan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157