Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 6

Chapter 6

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

shi "Abban Jawad!" Bai amsa ba, amma ya bude idanuwanshi da suka yi ja alamun ko barci bai ishe su ba ko kuma ana cikin damuwa. Ta sake nazartar shi a hankali ta ce, "Tunda ka dawo na kasa gane maka, na san akwai abin da ke damun ka amma ka'ki fada mini, ni kuma na san matsalar! Idan na yi rantsuwa cewar Sa'adah ke da ala'ka da wannan damuwar da kake ciki ba zan yi kaffara ba, mai yasa ba za ka yafe mata ba, mai yasa ba zaka daina wahalar da zukatanku ba, me yasa kake gudun gaskiya da gangan? Ni dai na san ', kullaci, da rashin yafiya ba halayyarka ba ce! Ban san me yasa ka aro ka yafa akan Sa'adah ba! yau shekaru kusan bakwai kana ta wahalar da zukatanku, sai yaushe za ka hutar da ku? ko makaho ya ji halin da kake ciki yasan kana sonta, balle ni da nake tare da kai, na ro'ke ka ka gaggauta gyara tsakaninku, tun kawaicina bai 'kare ba, tun ban fara kishi da ita kamar yadda take yi dani ba, na tabbatar idan hakan ta faru ba zaka samu nutsuwa ba!" Sai a lokacin ya bu'de baki murya ba amo ya ce, "Kece kike ganin haka duk yadda kike tunanin lamarin ba haka ba ne, kinsan kuma ban taba 'karyar ba zan dawo da ita ba, saboda Ubangiji ne ke jujjuya lamura, idan ya 'kaddara sake zama a tsakaninmu zan dawo da ita." "Zuwa yaushe za ka dawo da ita din? Ka fi shekaru uku kana wannan maganar, ba irin girman kanta da ba ta ajiye ta baka ha'kuri ba, ni kaina na sha ganin ta tsugunne a gabanka. haba Abban Jawad! Wanne irin abu ne haka da ba zai wuce ba?" Ta fada muryar ta na karyewa. Shi kansa bai san mai yasa ya shiga ru'du a dalilin halin ko in kular da Sa'adah ta mishi ba, da kuma yadda ta daki 'dansa a gabansa, alhalin kuma tun tuni ta san baya son ta masa haka a gabansa. Amma saboda da ta nuna masa ba shi da sauran gurbi a zuciyarta, ba shi da mutunci a idonta ta rufe Jawad da duka akan idonsa. Sannan a gaban jama'a ya tsaya dan ya taimake su amma ta wula'kanta shi, ta nuna masa iyakarsa, idan ya tuna wadannan abubuwan sai ya ji har zazzabi ne ke neman kama shi, hakan na nufin Sa'adah ta daina son sa, ta ha'kura da shi ke nan? Zuciyarsa na bugawa idan ta hasaso masa cewar ta samu wanda take so, ko kuma za ta sabunta soyayyarta da Khalil Ibrahim wanda yake jin komai na iya faruwa da shi idan hakan ta faru. Ya nisa ya ce, "Ke fa duk yadda kike tunanin lamarin Sa'adah ya kerewa tunaninki, yanzu bata so na, ba ta da burin sake zama da ni" A yadda ya yi maganar ta san akwai abin da ya gani a tare da ita da ya jefa shi cikin wannan yanayin. Wata'kila ta gaji da bin kansa, ta tattara ta jefa shi a kwandon shara, kamar yadda ya mata, shine kuma dan son kai irin na namiji zai ji an masa rashin kyautatawa, su dai sun fi son mace ta yi ta bin su, suna jan ta a 'kasa. "A hankali cikin son 'karfafa masa guiwa ta ce, "To ina ruwanka da soyayyarta? Ina tabbatar maka son da kake mata ya isa ya ri'ke auranku, muhimmin da za ka damu da shi mutuncinka a idonta, balle ma nasan nan duniya ba namijin da take so sama da kai, ba kuma wanda zai zarce ka a gunta. Wata'kila ta gaji da yadda kake tamaula da ita ne, ko ba ta ci albarkacin so ba, taci albarkacin Jawad! ko ka san Jawad, komai zan yi masa ba zai gamsu ba, matu'kar ba uwarshi ya gani a tare da kai ba" Idonta ya dan ciko, ta dan tsahirta sannan ta ci gaba da magana, "nan gaba Jawad zai tattara dukkan tsana ya dora mini, zai ga saboda ni ka 'ki zama da uwarsa, kai ma kasan tunda muka dawo 'kasar nan ya canja, na ro'keka dear kar ka ruguza farinciki da kwanciyar hankalinka da na 'danka" Janyo ta jikinsa sosai ya yi, ya ri'ke hannunta ya kalleta sosai ya ce ,"Farida ke din mai kirki ce, mai ha'kuri ce, mai sanin ya kamata ce, kina sona kina son kwanciyar hankalina, ina yaba miki, ina kuma fatan Allah ya fi ni yabawa, Allah ya ba mu zuria dayyiba!" Hawayen da take ma'kalewa ya zubo a kan fuskarta ta ce, "Ni da ban da lafiya ne zan haihu?" Cikin kulawa mai yawa ya ce, "To menene ya gagari Ubangiji? Son da nake miki wallahi ko ban taba haihuwa ba, zan zauna dake a haka domin ke nake so ba wani abin da zan samu a gareki ba, sannan rashin haihuwarki kullum ke sa na ji son ki da tausayinki na sake cika mini dukkan zuciyata, ina son ki da ke da dukkan lalurarki Farida!" Sai kawai ta fada jikinsa tasa mishi kuka, shi kuma yana dan bubbuga bayanta, yana jin ina ma zai iya bude mata 'kirjinsa dan taga 'kololuwar matsayinta a zuciyarsa?. Ya tabbatar bata san yadda yake jin ta a Zuciyarsa ba ne. ```Alkalamin SURAYYA DAHIRU```✍🏼✍🏼 [5/14, 11:03] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·• _GAISUWAR GIRMA GA_ *HAJ HAFSAT SODANGI* _(MIJIN TACE)_ 9-10. Tsawon lokaci suna wannan halin har ya samu nasarar dawo mata da walwalarta, "To kawo mini abincin nan mu ci don nasan ke ma ba ki ci ba". Ta yun'kura tana cewa, "Ina zan iya ci alhalin mijina bai ci ba!" Kicin ta nufa ta hada komi a kan faranti ta kinkima ta yi dakin nashi kamar yadda ya ba ta umarni, Sai da ta shimfida ledar cin abinci sannan ta zuba musu abincin a faffadan plate, shinkafa da miyar kifi ne, sai hadin Salad, gefe kuma zobo ne wanda ta sarrafa da tsurar sugar da cocomber sai flavour. Ba ka jin komai sai karo tsakanin cokali da plate kasancewar shi ba ya magana idan yana cin abinci. Suna gamawa ta kwashe komai ta gyara wajen sannan ta hada masa ruwan wanka ya shiga. Ta fice zuwa nata dakin, ta fito falo sukayi kicibus da shi, ya fito cikin lallausan yadi mai kalar sararin samaniya,(Skye blue) bai dora hula ba, amma ya taje sumar nan da ta cika kan fam! Ya dora farin glass a idanuwanshi, sai tsadden kamshin turaren Versace ne ke tashi a jikinsa. Kugu ta rike ta zuba mishi ido tana murmushi ta ce, "Na san mijina gwanin iya wanka ne, amma irin wannan kwalliya haka da La'asariyar nan! Sai ina? ko wurin Iya Basiru za a?" Ya fashe da dariyar tuna baya, sai ya ce, "Kinsan fa har yau fadanta na nan lalle idan ta ji wannan sunan kin san 'yan kallo zaku kwasa." Ita ma cikin dariya sosai ta ce, "Ai na san yanzu ta girma da fada, ka san me?" Ya

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});