Chapter 42
Chapter 42
daki wallahi gori za a yi mini, ko a yi ta zunden sadaka ta ka bayar." Ta karasa cikin gunjin kuka. A zuciye Inna ta ce, "Watau ke ba za ki bi shi ba, sai shi ne zai bi ra'ayinki, ke kullum sai an yi artabu da ke? Kin taba ganin wanda ya bi iyayensa bai ci ribar rayuwarsa ba? Ashe ba za ki koyi da yayar ki ba?" Ta sake kara sautin kukan ta ce, "Ai samun irin mijinta da yan'uwansa sai an tona a wannan lokacin, sannan kuma ni da ita akwai banbanci." Takaicin ta ya kama Inna ta ce, "Banbanci kuwa a bayyane, ita ta yarda duk talaucinmu, mu ne iyayenta, za mu yi iko a kanta ba tare da ta ga gidadancinmu ba, sannan karatu kadan ta yi amma mai cike da ladabi da biyayya, in sha Allah Ubangiji ba zai kunyata ta ba." Tana fadin hakan ta fita ta bar su da Baffa. "Iyah!" Ya kira ta da muryar da bai saba mata irin ta ba, tunda shi kullum a cikin lallashi da tausasawa yake mata magana. "Na riga da na zartar da maganar nan a gaban Mutari da iyayensa, ba zan koma na ce na fasa ba. Ko a fuska kika nunawa yaron nan tsarina bai miki ba, ki tabbatar kin nuna ban isa da ke ba, ba kuma zan sake yin iko akan ki ba." Ya na rufe baki ya juya shi ma ya fice abinsa, sai ji ta yi kukan ya tsaya mata cak! Amma wani irin ba'kin ciki take ji ya shake mata wuya da zuciya. Da 'kyar ta fita ta yi alwala ta yi sallar Maghrib da Isha wanda ba nutsuwa a cikinsu. Da rarrafe ta isa kan shimfidarta, hawaye na bin fuskarta, ta ya ya za a mata irin wannan auren sai ka ce mutanen da? Ai ko shi Baffan da zai auri Innarsu, ya mata hidima, ita ma kuma da kayan dakinta aka kawo masa ita har yanzu gadonta na aure ne a dakin, duk kuwa da auren zumunci aka musu, shekaru kusan talatin. Amma sai ita a wannan lokacin za a mata irin wannan auren, kuka ya sake balle mata.😭 Tsawon lokaci tana kuka har kanta ya fara ciwo, a ranar dai ba ta yi wani cikakken barci ba, ba ta tuna matsalarta da MK ba sai da Asuba. Tana idar da sallah ta ciro wayarta a caji ta lalubo lambar MK ta kira, har ta katse bai dauka ba, ta kira ya fi sau biyar amma bai amsa ba. ta ja wani dogon tsaki tana furta "Sai ka yi ta yi." Ta kwanta ta yi shiru, amma sai ta kasa hakuri, ta sake kiran sa, nan ma bai dauka ba, ta yi ta kira har ta gaji, takaici ya sa ta yi jifa da wayar. Har rana ta fito tana kwance ta ki fita, fishi sosai take yi, ga idanuwanta sun kunbura saboda tsabar kuka. Inna kuwa ko ta kanta ba ta bi ba, ta yi dukkan ayyukanta, ta yi abin karin kumallo suka karya da Baffa amma ba ta nemi Iyah ba bare ta ba ta. Sai da Baffa zai fita ne ya tsaya bakin kofar dakinta ya kira ta. Ta fito sanye da hijabi duk fuskar ta a kumbure, ta tsugunna ta gaishe shi, ya kalle ta cike da kulawa ya ce, "Iyata yau ban ji motsin ki ba ga shi har zan fita, kin san idan ban gan ki ba yini zan yi ba kuzari". Ta sake yin kasa da kanta hawaye na cika mata ido, "maza fito ki yi wanka, ki sami abinci ki ci idan zan dawo zan taho miki da indomie har da Sadine na gwangwani, da ma kwanaki kin ce mini indominki ta 'kare, yau zan sayo miki ki ajiye a dakinki har da madara." Cikin kuka ta ce, "Na gode" Ya tafi yana jin kukan ta har cikin ransa, ya na raya yadda Sumayya ta zarta ta biyayya da gudun zuciya amma Iyah tafi shiga ransa matu'ka da gaske. Ko da ta koma dakin sai ta sake dasa sabon kuka mai cike da kururuwa, yin sa take iya karfinta, fishin da MK ya dauka ya sake dagula mata lissafi. Tun Inna na danne bacin ran ihun da Sa'adah ta cika mata kunne da shi, har ta kasa jurewa. Don haka ta shiga 'daki ta samo wani danko mai kauri ta nada a hannunta, ta nufi dakinta, tana shiga kuwa ba bata lokaci ta shiga zabga matata ko ina, da iyakacin karfinta, da kyar Sa'adah ta kwace ta fice a guje, ta nufi hanyar zaure ta tsaya tana kuka sosai. Ta dade kafin ta dawo gidan, tana rabe-rabe, Inna ta kalle ta rai a bace ta ce, " Idan kin san za ki ta sani a gaba kina mini kukan iyashege ki juya ki tafi duk inda za ki shiga, watau ni kika raina? Kin ga Baffanku ya fita shine za ki 'bude mini wannan ja'irin bakin naki da bai iya komai ba sai 'kulla karya da munafunci kina mini ihu. Wai har kin yi wayon da yafi nawa, ni za ki yiwa karyar Zainab za ki raka unguwa? Ashe da wannan shedanun kawayen naki masu yi wa Babba kallon raini kuka fita, har kin yi lalacewar da za ki shiga gaban motar namiji ya kawo ki har kofar gidanku, ki fito akan idon jama'a, oh ni Salamatu wacce irin yarinya nake tare da ita ne haka?" Ta Fadi hakan tare da tafa hannu tana salati. "Wai kuma don ki bata ni a gunsa shi ne zaki ce nasan zaki fita, to don uwarki daga yau kika kuskura kika ce mini za ki fita da sunan zuwa unguwa wallahi sai jikin ki ya fa'da miki. Na daina raga miki tunda ke rarrashi baya bi da ke, kafin nan kafin ki bar gidan nan sai na miki tabbuna ba ma tabo ba. Tunda nake da Baffanku bai taba ganin kasawa ta ba sai akan ki, jiya da daddare ba abin da bai fada mini ba, bayan an tabbatar masa a mota aka kawo ki." Jikin Sa'adah ya yi sanyi kalau, ta yi shiru amma hawaye bai daina zubo mata ba, tana jin tsanar Khalil sosai a ranta duk shi ya janyo mata wannan tashin hankalin, da ya ajiye ta a hanya ai da ba wanda ya ganta, ga fushin Uncle MK, ga fishin Baffa duk da dai shi mai yawan yi mata afuwa ne. Amma yau har zane ta Inna ta yi, ba za ta iya tuna yaushe rabon da Inna ta dake ta irin haka ba. A darare ta shigo ta shige dakinta, ta fito da shirin wanka, sai da ta fito ta shirya, sannan ta je ta tambayi abincinta, ba tare da ta kalle ta ba ta ce, "Ban yi dake ba tabbatacciya! Kina kwance na tashi na yi komai saboda zuciyarki ba imani balle tausayi, amma har ki iya cewa ina abincinki? Saboda ga baiwa kin ajiye, to ga tuwo can da kika raina sai ki hada wuta ki 'dumama, idan kuma kin fi nan sai ki zo ki dora abincin rana idan kin gama sai ki ci." Tana kaiwa aya ta ja bakinta ta tsuke. Cikin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157