Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya ci amanar aikinsa. Tsawon lokaci tana kuka, ta koma ajiyar zuciya tunda dama tun safe take yinsa. Da kyar ya shawo kanta ta yi shiru, sai da ya ga ta nutsu sosai, sannan ya samu sukuni a zuciyarsa, yana mamakin yadda yake jin matsananciyar soyayyarta na ratsa dukkan jikinsa gaba'daya. Cikin murya marar amo saboda shauki ya ce, "Jiya na ce miki zan zamu yi magana ko?" Bai jira amsarta ba ya ci gaba da fadin, "Ban yarda ki fada wa wani ko wata cikin makarantar nan abin da ke faruwa a tsakaninmu ba, wannan sirrinmu ne ni da ke da ba zan so ya shiga kunnuwan students ba." "Sannan bana bu'katar, ki nuna wata alama da students za su fahimci akwai wani abu a tsakaninmu, lastly ki rabu da fitunannen yaron nan (Khalil), ki fita harkarsa in dai kina bu'katar kwanciyar hankalina". Ta yi shiru tana nazari maimakon ta fahimci inda ya nufa sai ta karkace, zuciyarta ta shiga kissima mata ai saboda Farida ne yasa zai ce bai son aji yana sonta banda haka mene ne na boyewa tunda dai aure za su yi ba wata 'barna ba. Ya gaji da shirunta, ya ce, "Kina tare da ni kuwa?" Nan ma shiru ta yi, bai ji dadin shariyar da ta mishi ba, amma sai ya waske, ya san dama haka take, bare kuma yau ya ta'bo ta. 'Kasa ya yi da murya sosai ya sake cewa, "Magana fa nake miki, amma kin yi mini shiru". Cike da fishi sosai ta ce "To ni me zance?" Zuba mata ido ya yi, yana kallon yadda take ta cika tana batsewa har wani huci take yi, jikinsa ya yi sanyi bai cika son mace mai fusata sosai irin haka ba, sai dai son da yake mata ya riga ya yi bunkasar jurewa duk wani kalubale daga gare ta. Wannan karon ido ya zuba mata, tare da bude murya sosai ya ce, "Ina ta miki magana amma kina jina kin mini shiru, kar ki bari na ji a zuciyata son da na ce ina yi miki shi ne dalilin da za ki fara raina ni". Kawai sai ganin hawaye ya yi yana tsere a kan kuncinta, tana ta yunkurin bude baki don ta yi magana amma ta kasa. A ransa yake fadin akwai aiki a gabana, a kankanin lokaci ya gane shagwababbiya ce ta gaske, banda haka mene ne kuma abin kuka a maganar da ya yi? kan dole ya yi ta rarrashi akan ta fada masa abin da yasa ta kuka cikin maganganun da ya yi. Cike da kukan kuwa ta hau cewa, "Ai an sha fada mini duk saurayin da yake boye kanshi kar a san yana son mace, to ba da gaske yake ba, yaudarar ta zai yi". Ta 'karasa maganar cike da gunjin kuka, mamakin ta ya kama shi sosai ya ce, "Amma na sha fada miki gidanku ba gidan da zan yi wasa ba ne, tunda kina shakku a kaina a satin nan zan gabatar da kaina a gaban Baffa shike nan?" Ta goge Hawayen da ya'ki tsaya mata, a hankali ta ce "To saboda kar Farida ta sani ne kake son a boye?" Takaicinta ya kama shi, amma kuma ya kasa yi mata jan ido, sai ma lallaba ta da ya shiga yi, ta hanyar fadin. "Sa'adah ya kamata ki dinga fahimta ta, inda Farida nake so, nake burin aure ba abin da zai kawo ni gunki tunda ba dole aka mini ba! Ribar me zan ci idan na zo don na miki karyar ina son ki? Mahaifinki mutumin kirki ne, na san shi, tun kafin na san ki, akan me zan yaudari yarsa? Ina son ki yarda da ni, yarda ita ce matakin farko a soyayyar gaskiya, abin da yasa nake son mu bar maganar a tsakaninmu ba komai ba ne illa don na kiyaye dokar makaranta! Ba makarantar da ta yarda malami ya yi soyayya da 'daliba, ni kuma zan yi iyakar'ko'kari na kiyaye kowacce irin dokar makaranta, ta kowacce fuska wannan shi ne gaskiyar magana". Ta yi kasa da kanta, tana jin nutsuwa da maganganunsa. Ya nisa ya ce, "Kin yarda da manufata?" Kai kawai ta 'daga mishi alamar eh, sai ya ce "To ba ki ce komai akan wancan yaron ba" Ta sake yin kasa da kanta ta ce, "Ai ni ba saurayina ba ne". Da sauri ya ce "Magana muke ta gaskiya fa Sa'adah! kin san har letter da kika masa wacce na dauka tana nan, kawai idan kin amince kina sona, to ki fita harkarsa, kin san dai yaro ne karami, da ba zan iya hada soyayyarki da shi ba, ga shi dama ba tarbiya ce ta wadace shi ba". Kanta tsaye ta ce " To! na ji zan rabu da shi, kai ma kuma ban yarda na dinga ganinta tare da kai ba, kodayaushe tana hanyar staffroom saboda kai, kai ma da ka motsa sunanta ne a bakinka, to ba ita kadai ba ce mai 'kokari ba, ire irenta suna nan, wasu da yawa ma a cikin makarantar sun fita kokarin, ita zubin Sadakar Yallah da kuke gani a tare da ita yasa kuke ga kamar ta fi kowa". Mamaki da dariya suka kamashi lokaci guda, amma ya dake bai bari dariyar ta fito ba, ya ce, "Amma ai na tabbatar miki ba son ta nake ba, sannan kin san dole wani abin zai hada mu tunda dai ni malaminta ne, abin da za ki yarda da shi shine wallahi ba budurwa ta ba ce, ba ni kuma da niyyar auren ta". "Amma da bakinka kace mini za ka iya maye gurbina da ita". "Tabbas na fadi hakan amma ki sa a ranki sai idan ke ce kika so faruwar hakan, ina nufin kika juya mini baya, sai na yi maleji da ita a rashin ki, kin san Bahaushe ya ce a rashin uwa, akan yi uwar'daki". Da'di ya kamata har murmushi ya subuce mata, shi ma ya taya ta murmushin tare da cewa, "Na rantse miki ban taba ganin wacce ta fi ki kyau a duniyata ba, musamman idan kika murmusa". Kunya ta kamata tasa dukkan hannunwata ta rufe ido tana jin kamar su tabbata a haka. Ganin sun dan fahimci juna ka'dan ya ce "To muje ki tafi gida kar aga kin dade da yawa, tunda ba za ki yarda na kai ki ba". Sai da ya sa ta cikin Adaidaita Sahu ya biya kudin, sai da ya ga sun tafi sannan ya koma ya hau mashin dinsa yana jin shauki na shigarsa, yana kuma jinjina kishin Sa'adah. WAYE MK BICHI? Haifaffen karamar hukumar Bichi ne, a jahar Kano. Mahaifinsa Alhaji Kabiru Wadata, Bafulatanin Bichi ne, mai arziki ne a lokacinsa, don zai shiga cikin jerin attajiran Bichi shi yasa ake masa la'kabi da Wadata. 'Dan kasuwa ne mai sana'ar fata, yana fataucin ta zuwa jahohin Arewa. Mukhtar shi ne babban dansa na namiji, shi ne kuma na biyar a dukka gidan, an haifi mata hudu kafin shi. Matan gidan biyu ne Hajiya Babba (Indo), tana da yara bakwai wadda ukun farko dukkan su mata ne, Zainab, Khadija, Amina, kuma duk sun girmi MK, sannan Abbas, Akil, Sameera, da auta Bilkisu. Sai dakin amaryar gidan wacce

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});