Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 132

Chapter 132

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,196 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

amince mini, wallahi na sha wahala, na azabtu, yanzu haka ina daf da kamuwa da ciwon zuciya, ba komai bane ya janyo mini ba, illah ganin ki da wasu mazan". Ya sauko ya dur'kusa a gabanta karon farko ya ce "Ga ni akan guiwata, ki yi hakuri, ki yafe mini, ki sake bani wata damar, ni na san kina so na. Plz Sa'adah let Gone by gone, ba zan iya wannan rikicin ba, na horu hakanan, ki fa'dawa Baffa mun shirya, na kuma kawo miki Baba Isa gaban ki, ki fa'da masa mun shirya, kin yafe mini, Ni kuma na miki al'kawarin zaki rayu cikin soyayya mai wuyar samu a Yau". Ta dago ta kalle shi a durkushe a gabanta, da'di ya kamata, amma sai ta waske ta ce "Ni fa ba zan yafe ba, matu'kar ba wani ne ya aure ni ya ta'ba ni kamar yadda kake ta'ba wata macen ba". Ya mike da sauri ya ce "shikenan, dama ke ai ba'a taba rarrashin ki, kin gamsu cikin da'din rai ba, kaddara ce ta hau kaina ban kuma isa na kauce ba, tunda kin kasa fahimta shikenan, amma ki sani idan fa 'kaddara ta gwada iko akan ki, kika dawo mini, ba zan gamsu kin mini uzziri ba". Ta tura baki gaba sosai ta ce " Da ikon ubangiji ma ba zata faado kaina ba". Ya koma ya zauna a inda yake zaune tun farko yana tunanin mai kuma zai yiwa wannan yar darun ta fahimce shi, shi tashin hankalinsa daya ya ganta da wani, ba dan haka ba, da ya daure ya kyale wannan yarinyar da take neman manna masa ciwon zuciya. Sun Jima a zaune ba um bare um um. Ya mike ya ce "zan tafi ina fatan idan na kira wayar ki, ki dauka. Allah ya huci zuciyarki". **** A cikin wannan yanayin shari'ar Sanata Ibrahim Hassan ta sake zagayowa, bayan doguwar muhawara da tarin hujjojin lauyoyinsa, kotu ta wanke shi daga dukkan tuhumomin da ake yi masa. Sa'aadah ta bukaci a bashi naira miliyan hamsin a matsayin diyyar bata masa suna da lokaci. Jajircewar da Sa'a ta yi a wannan shari'ar yasa sunan ta ya shahara, ta yi farin jini. Har gida Mai girma Sanata ya aiko mata da dankareriyar mota kirar Toyota Camry new modern. Direbansa da wasu yaransa ne suka kawo, suka danka a hannun Baffah. Bayan sun yi godiya a madadin Sanata. Washagari asabar Khalil ya mata wayar zai zo ya mata godiya tare da ban gajiya. Saboda jidalin Mk ta masa kwatancen gidan Sumayya dan kar ya zo shago ya hango ta da Khalil, duk da a gidansu ta kwana. Sai bayan azahar ta tafi gidan Sumayyan tunda ya ce sai bayan la'asar zai zo. Aikuwa ana idar da Sallar la'asar ba jimawa ya iso, sosai suka sha Hira, wani lokacin kuma suyi ta jifan junansu da kallon kauna sai kuma a waske da murmushi, tabbas soyayya bata tsufa sai dai masoyan su tsufa. Amma Sa'a ta 'kudire ba zata auri Khalil ba, domin ta san komai na iya faruwa da Mk a sanadin hakan. Da zai tafi ya ajie mata envelope mai dauke da dalar amurka, wanda idan a kiyasin naira zasu iya kaiwa dubu dari biyar. Ya yi ta mata godiya tare da cewa "Na so kwarai ace na aure ki, sai dai jiya Mum 'dina ta tabbatar mini Yar kanwarta ta zaba mini, bijirewa ta kuma na nufin lalacewar al'amurana, na sani har na mutu ba zan daina son ki ba, sannan tsayiwar ki, kadai kan mahaifina ya tabbatar mini da cewa tabbas baki manta ba, duk irin kaini 'kasa da Mk yake ko wa, da ya yi" Tana dariyar wai ya manta sunan Mk ta rako shi har wajen da ya ajiye motarsa, Suka sake tsayuwa a wajen adalilin ya ce zai shiga gidan Madugu wurin abokin karatunsa a Egypt. Suna tsaye motar Mahmoud ta tunkaro su, zuciyar Sa'a ta buga, kafafuwanta suka dinga barazanar kada ita. Mk dake gaban motar ya ji tamkar ya sume, mussaman da ya tabbatar Khalil ne wannan zabgegen saurayin ya girma sosai. Suka hada ido amma Khalil sai ya dauke kai bayan ya galla masa kallon raini tamkar shekarun baya. Har zuwa yau bai ji zai iya kallon Mk a matsayin malamin sa ba, sai dai a matsayin dan fashi a soyayya. Wannan kallon ya sake rikita Mk, domin yasan na rainine tsantsa. Yayin da Sa'a bugun zuciyarta ya tsananta, tana raya ina ma motar Mahmoud ce mai tint? Mai gadi ya bude musu gate Mahmoud ya ja suka shiga, ya juya ya ga Mk yana wani irin numfarfashi, tamkar ya samu attack na asthma. A farko 'karfi ya dauka abin Wasa ne sai da ya ga Mk ya sume sai kawai ya ja motar a kidime zuwa asibiti. SURAYYA DAHIRU. ✍️✍️ *HALIN YAU*! *NA* *SURAYYA DAHIRU*. *Lafazee writers* *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* *GAISUWA GA DUKKAN MAMBOBIN* *HALIN YAU FANS* *_Na gode sosai da yabawar ku, comments din ku na matu'kar sa ni Nisha'di, Allah ya bar zumunci_*. 102-103. Suna tsaye suka ga mai gadi ya bude musu kofa, Mahamud ya fito a guje kana ganin tukin da yake yi kasan babu sukuni a tare da shi. Hankalin Sa'a idan ya yi dubu ya tashi, Khalil ya kula da yanayinta ya ce, ina son ki sosai, ke kuma kina son wanccan wicked man din. Ya'ke kawai ta yi, ba tare da ta ce komai ba. Ya juya ya fara tafiya yana cewa" sai wani lokaci, muna godiya, kwarai da gaske". Da azama ta juya itama tana jin tamkar ta yi ta zunduma ihu, ya ya zata yi ne? Ta san ganin Khalil tare da ita means alot a wurin Mk. * ** Suna isa Asibiti aka shiga da shi dakin agajin gaggawa wato (emergency). Likitoci suka rufu akansa ana kokarin shawo kan matsalar, tsawon lokaci kafin a samu numfashin sa ya dawo, sai dai ba dai dai ba, Dan haka dole aka saka masa na'urar sau'ka'ka zukar numfashi (oxygen). Sai dare 'karfi ya sanar da Farida da Abbas halin da ake ciki. Dukkansu sun yi jigum jigum a asibiti suna kallon Mk a kwance bai san wanda yake kansa ba. Farida sai fama take da tissue tana goge hawayen da ya kasa tsayuwa a idonta, ta dade da sanin mijinta bashi da lafiya, ta Dade tana jiye masa shiga irin wannan halin, adalilin kullum yana cikin rashin sukuni, ta dinga jin haushin Sa'adah na kamata, ta tabbatar ita take son kaishi barzaku dan kawai ta musu biyu babu. Hajiya kuwa sai da gari ya waye aka sanar mata, ta isa asibitin cikin tashin hankali, ta kalli yadda ya ke shimfide akan gadon asibiti, ya zabge sosai, dama ya dade a rame Amma yanzu ramar ta bayyana karara. Haka suka tasa shi a gaba masu addu'a na yi, masu share hawaye na yi. Sai da aka kwana biyu Baffa ya samu labarin ciwon Mk adalilin Bai ganshi ba, bai ga Mahmoud ba, haka Abbas, har shagon su ya je, anan ya samu labarin ai yana asibiti an kwantar da shi. Akeel ne ya raka shi asibitin, ba karamin damuwa ya shiga da ganin Halin da Mk ya ke ciki ya yi ba.

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});