Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 147

Chapter 147

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya dinga rarrashinta ya samu ta daina kukan. A hankali ta ce "Akan me zaka mini dariya bayan abin da ka janyo mini?" Da sauri ya ce "me na yi miki? "Abin da ka yi mini a Sokoto mana". "Oh sorry Sa'adah! na dauka abin ya wuce ai". "Ina ya wuce tunda kullum yini nake da yawu a bakina, ga idan Innah na girki sai dai na rufe daki, na yi ta amai ban son ta gane mai nake ciki." "Ya waske, da cewa to ana boye ciwo ne? Tashi muje ki ga likita". Ya kalleta gaba'daya ta yi laushi, ya san laushin da ta yi dan ta samu yadda take so ne. "Ni ba inda zani". Ya kuwa mike da sauri ya ce "shikenan na fita hakkin ki, mu yini lafiya". Tana daga zaune tasa hannu ta ru'ko rigar farar shaddar jikinsa. Ya juyo suka ha'da ido suka dinga kallon juna, suna jin wani irin tsumin soyayya yana tsuma su. Sa'adah ce ta yi saurin dauke kai. A hankali ta ce "da gaske na gama". Ya juyo ga'ba daya ya ce " Sa'a ba zai yiwu na tare da ke a hakan ba, kina musguna mini, ban isa ki mini yadda nake so ba, ban isa na ce ga yaddda zaki yi, ki ce to ba, haka kawai fa kika ce ba zaki tare ba, sanin kanki maganar ba a hannuna take ba, tunda Baba Kika fadawa, shine kuma ya bani umarnin na lamince miki ki kammala shirin ki, yanzu kuma cewa zai yi na nuna bai isa da ni a karo na biyu ba". Ta tura baki gaba ta ce "Amma ai da ka ro'ke ni akan ka kira shi , na fa'da masa zan tare da bakina". "Eh na fa'da amma sai na ga bai kamata na matsa miki ba, shekaru bakwai na yi ina kuakan rashin ki, Kinga kuwa duk dadewar da zaki yi kina shirin ba zaki kai irin wannan lokacin ba. Ki Bari ko wata uku ne, nan gaba sai mu san yadda za'a tunkare shi. Kuka ta fara tana cewa" ba wannan maganar, wallahi ba zan yarda Innah ta fahimci Ina da ciki ba, tunda ba za su gane da bada son raina hakan ya faru ba". Ya zauana ya fuskanceta sosai, sai kuma ya tafi ya yi sujjud shukur, ya dago yana cewa "Alhamdulillah, ubangiji ya raba ku lafiya, na dade ban ji farin-ciki irin na yau ba". "Tashi muje ki siyi abin da kike so a matsayin tukuici". "Ni ba inda zani". Ido kawai ya zuba mata, jikinta ya yi sanyi ta sunkuyar da kanta kasa. Ta mi'ke tsaye, tana tura baki gaba, irin wadda take yi masa a shekarun baya, mai ha'de da wani irin ta'bara da shi kawai take yiwa irinsa. Nan da nan jikinsa ya hau tsuma da sauri, ya matsa kusa da ita, ya rungumeta sosai, dukkansu sun shiga wani irin yanayi mai tsuma jiki da gangar jiki gaba'daya. A kidime Mk ya saketa ya shiga waiwayen inda zai ga hijabinta, can ya hango wani a ninke akan akwati. Da kansa ya ware ya fara kicinyar saka Mata. Tmda taimkonta hijabin ya daidaita. Ya kalleta sosai ya ce "Bari na fita, sai ki fito muje asibitin a duba ki, daga Nan sai ki raka ni unguwa". Ta kasa yi masa musu, tana tsaye tana jin yana yiwa Inna sallama, ya fice ya barta tana faman tauna maganar da zata fa'dawa Innah. Haka ta fito rataye da yar 'karamar Jakarta, ta kalli Inna da take kofar kicin a tsaye, ta ce "Inna zanje asibiti, daga nan kuma zan wuce gidan Maman Khalifa". Ido Innah ta bita da shi tabbas tana ganin kasala a tare da ita, kuma ba kasafai take cin abinci ba. Ta ce "wanne asibitin zaki je?" "Ban san wadda zai kai ni ba, Ni ba dan ya dage bama, da ba wani asibitin da zani, na san zazzabin cizon sauro ne". "To sai kin dawo, amma kar ki kwana gidan su Khalifa, Baffan ku baya gari, gara ki dawo mu kwana tare". Sa'adah ta amsa da cewa "To Innah". Innah ta sake cewa "ki kula da kanki, ki lalla'ba shi, kar ki yi abin da zai ja hankalinsa akan ki, har sai anyi tariya. Ni ba gaskiya ba zaki mini wata uku a gidan nan da auren ki ba, wanan watan da wani watan ya isa, koma kudin bai isa ba, kina dakinki sai ki dinga siyan abin da kike so, tunda dai ai ansan mu masu karamin karfi ne". A sanyaye Sa'a ta ce "Hakane Innah! Ni idan kin ce ma a wannan watan na tare zan yi biyayya ba dan Ina so ba, sai dan na nuna miki na fi girmama ra'ayin ki akan nawa". Sosai Innah ta zuba mata ido tana son ta gasgata maganar Iyah, amma bata san meyasa take ganin tamkar akwai wani abu da yasa ta sauko haka da wuri akan tariyar ba. Ta tafi, Inna ta bita da addu'ar dawowa lafiya. Suna tafe yana ta yawo da su akan titi, shi kansa tunanin inda zai kaita yake yi. Can ya kalleta ya ce "wanne asibitin kike zuwa yanzu?" A hankali ta ce "Ni fa na je asibitin an duba ni, ta butde jakarta ta fito da magungunan da aka bata tana nuna masa. Ya ce "To sannu My Sa'adah". "Yanzu bari ki raka ni unguwa" Basu zame ko ina ba sai gidansa na rijiyar zaki. *Ina ta shan korafi daga makaranta cewar yanzu yanga nake yi, ko kadan ba wannan maganar, a farkon fara posting Ina da pages masu yawa a 'kasa, a yanzu kuma babu, sai na yi typing kafin na turo, kowa ya san akwai hidimomi irin na yau da gobe akan kowanne bawa.* *Ni Kuma har da ciwon idon da yake sani rauni a typing din, Ina fatan za'a yi hakuri, saura kiris ma mu kammala, ban yi tsammani labarin zai yi tsayi haka ba* *Zan sanar da cewa ba kullum zaku ga update ba, amma ba zai dinga daukan lokaci ba* *Na gode sosai da yabawar ku kan rubutuna*. Surayya Dahiru ✍️✍️. *HALIN YAU*! *NA* *SURAYYA DAHIRU*. *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *TAIMIYYAH*❤️ Ina kuke ne masoya kuma makaranta littafan Hausa,me kuke jira baku afka cikin wannan tafiya ba? ko kuna da labarin cewa shahararriyar marubuciyan wato Ayshat Ɗansabo Lemu,marubuciyan👇🏻 *LAIFIN ƁOYE* *HAMAL* *HURAYYAH* *BURIN ZUCIYA* *ƘALUBALE* *NAILAH* *INA DA HUJJA* ta sake yinƙurawa domin tazo muku da zazzafan labarin ta me suna asama,domin faɗakar da ku da kuma nishaɗantar da ku,haɗi da koyar da ku dibarun girkunan zamani da gwangwaje ku da salon soyayya me tsayawa a zuci,duk acikin wannan shahararran labarin nata me suna *TAIMIYYAH!* Labarin da yazo da wani irin salo me cike da ban tausayi do motsa zuciyan me karatu,duka wannan zai zo muku akan farashi me sauƙi,da kuɗin ki 500 kacal zaki mallaki naki don gujewa shiga hakkin marubuciyan,zaku biya kuɗinku ta wannan asusun kamar haka👇🏻 *0504192664 Aisha Ibrahim Dansabo GTbank.Sai ku aiko da shaidan biyanku ta wannan layin 08167768704.* *Masu turo katin waya zaku

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});