Chapter 127
Chapter 127
rawar jikin kyautata masa adalilin taga sassauci a tare da shi fiye da wattannin baya da ko kallon inda take ba kaunar ya yi. Ta ji farin-cikin sauyin da ta gani a tare da yaron. Sai yamma lis suka fice da Babansa. Basu dawo gidan ba sai dare sosai domin har sai da Jawad ya yi barci a dakin Hajiya. Da ya zo yana tashinsa Hajiya ta ce "Barshi mana tunda ya yi barci". Da sauri ya ce " A a Hajiya bari kawai mu tafi lalla'ba shi nake yi ya daina gudun Farida, ta dora hankalinta akansa, amma yana gudunta tamkar kunama, yau dai na ga ya fara saukowa, gobe zan kai shi wurin uwarsa dan hankalinsa ya kwanta". Hajiya ta ce "dan hankalinsa ya kwanta, ko dan ka samu dalilin ganin uwarsa babu hijabi?" Mk ya ce "haba Hajiya" "Haba Hajiya ko dai haba gaskiya?" Washagari kuwa ya kai shi gidan da tarin tsaraba Niki niki tamkar wadda zai shekara, har da cake dinsa na murnar dawowar sa gida, bai ci ba, Mk ya ce ya taho da abinsa. har cikin gidan Mk ya shiga ya tarar da Innah na yin wainar shinkafa irin ta garin su Shafa'atun Bauchi ko da yake itama Innar ai daga Gamawa take kenan Inna Yar Bauchi ce. Sa'a na kicin na hada miyar cin masar. Ya dinga tuno yadda Sa'adah take yi masa waina da miyar ganye da yake santi, haka nan ya yi kewar dambunta, ya yi kewar farfesu mai daddawa, ya yi kewar kunun danyar gyada da shinkafa, da alkubus. Traditional dishes da ya yi kewar su ba za su lissafu ba, hatta shinkafa da wake har yau bai sake cin mai gardin ta Sa'adah ba. Haka nan kwa'don zogale da Rama. Yana matu'kar jinjinawa Inna yadda ta horar da Sa'adah nau'in abinci kala, kala masu dan karen 'dan'dano da kashe kowacce irin yunwa, ga kara lafiya. Sa'a tana jinsu ta rakube, ko kwakkwaran motsi ta ki yi dan kar a hangota. Baffa ya fito yana marabatarsu, yayin da hankalin uba da 'da ya karkata a son ganin Iyah. Lura da hakan da Baffah ya yi yasa ya kirata, ta fito sanye da doguwar riga ta atamfa, dinkin free ne amma ya matu'kar yin kyau. Da sauri Jawad ya ruga ya rungumeta yana fa'din "Daure ki gwada daga ni sama Mami". Baffah ya yi saurin cewa "wannan shine gangan Jawad, a gabana ka ke son ka kayar mini da uwa?" Mk ya murmusa ba tare da ya ce komai ba, bagarar da shi da Inna ta tsiri yi masa na matu'kar damunsa. Duk yadda Inna take jin haushin Mk bai hana ta zuba masa waina ba, ta zuba masa masar a ledar ta sake kara wata ledar, ta mike ta dauko flask ta shiga kicin ta zubo miya, ta kawo ta ajiye masa a gabansa, a hankali ta ce ga waina, ta koma ta cigaba da aikinta. Baffah kuwa fa'di yake "wannan tafiya zai yi da shi zubo masa wadda zai ci yanzu" Da sauri Mk ya ce "Na riga da na karya, na gode, a ransa kuma fa'di yake yaushe zan iya cin abinci a gaban ku?" Idon Baffa ya sa Sa'adah cewa Mk "Ina kwana". Ya amsa da sauri, cike da walwala. Ta shige dakinta Jawad ya bita, ya kwanta a shimfidarta, yana cewa "I miss your scent, I missed everything about you my Iyah". Ta ce "Ashe ban hanaka fa'dar Iyan nan ba?" Ya turo baki irin yadda ta ke yi ya ce "Iyah means mother, means uwa, Mami da Iyah all the same". Ta ce "To dai ban son sunan a bakinka barwa Baffa da Innah kawai". Mk suka fita tare da Baffah! Jawad ya fito da sauri ya bisu, daga kofar gida Baffa ya wuce inda za shi, yayin da su kuma suka tsallaka zuwa shagon Mk . Jawad ya yi mamakin yadda aka sake kawata shagon, komai na wurin na zamani ne, ya zauna yana cewa " Azo a wanke mini kafata". Harara Mk ya galla masa ya ce " Saminu ba ya nan, ina fatan ba Uncle Akil kake nufi ya wanke maka kafar ba?". Jawad ya yi shiru! Yayin da Mk ya zarce da fa'din, kullum ana idar da Sallar la'asar ka tabbatar ka zo nan kana koyon aiki, zan fa'dawa Akil duk ranar da baka zo ba, ya yi dealing dinka well well, kasan dai shi no nonsense ne baya wasa da yara, ba kamar Uncle Abbas bane da yake yi muku yadda kuke so". Jawad ya nisa ya ce"Malam ni bazan iya yiwa mutum aski ko wanke kafa ba, zan bata jikina ne kawai". Mk ya zuba masa ido yana kare masa kallo, a zahiri dai yaron kamarsa ya yi, amma dabi'unsa sak na uwarsa ne, gayu da pride dinsa na Sa'adah ne. Ya daure fuska sosai ya ce "Jawad ai baka kai a baka yin aski ko wankin kafa bama tukun, share wurin zaka dinga yi, kana wanke towels din da aka yi amfani da su, sannan ka dinga ganin yadda ake gudanar da aikin". Ya shagwabe fuska ya ce"Haba mana Malam a shagonka zan dinga irin wannan wahalar?" Mamaki ya kama Mk amma da yake yasan a iya shekarun Jawad da iya tunaninsa shi hakan abin kunya ne, a gurinsa. Sai ya sassauta ya ce, "Jawad Ni dai a tarihin Nigeria ban taba ganin wadda ya yi karatu mai zurfi ya mallaki jirgin sama ba, Amma na san yan kasuwa da suka fara da kananun business, a hankali business din y tunbatsa har suka sayi jirgin sama. Na san kai kuma burinka ka samu damar siyan jirgi, fa'da mini idan ba ka koyi business ba, how ur dreams will be reality one day?" "To zan dinga zuwa, amma plz Malam! tell Uncle Akil to be gentle, I really dislike his hershness" Mk ya sake daure fuska sosai ya kafe shi da Ido, har sai da Jawad ya dinga jin wani irin abu na ratsa shi, ya sunkuyar da idonsa kasa ya ce " very sorry Malam". Mk ya nisa ya ce "Akil din ka ke fa'din haka akansa? Kanina, kanina Jawad? ashe kuwa nima na shirya, domin Ni da shi ai daya ne a gunka! Ko Ahamad da yake karamin mu ban za ci zaka iya fa'dar wani abu da bai maka a tare da shi ba". Ya ru'ko hannun Mk ya ce "ba zan sake ba Malam! Plz forgive and forgot". Ya na fada yana leka waje, yana fatan Akil din bai iso ya ji me ya ce ba". Mk ya ce daina ma wani lekawa dan kuwa zan fada masa. Nan da nan kuwa ya fara kuka yana fa'din sorry Malam, ya tsorata sosai, domin Akil mala'ikan Yara ne, baya musu ta Dadi shine discipline master a family din nasu. "Ok stop crying! Ba zan fa'da ba, amma idan ka sake, ko idan ka zo ka ga baya shago ka ce zaka dinga yiwa su Saminu rudeness to ka tabbatar zai ji komai". Ya goge fuskar sa yana fa'din " Thank you! Komai suka ce na yi, yi kawai zan yi". Mk ya ru'ko shi yana fa'din "good boy! Sannan islamiyar nan ta safe zaka dinga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157