Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 58

Chapter 58

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

abinci da kuma abin sha, yayin da Sa'adah keta rawar jiki akan su, suna ta yatsina, hatta abincin ma ko hannu ba su saka ba bare su ci. Cike da murmushi Sa'adah tace "idon ku kenan, sai yau kuka tuna da Ni, ashe ma kunsan inda na ke! nema na ne baku yi ba?". Halima da tafi Safina ginshira ta ce " Akan mai zamu neme ki, inace kin dauke mu kin watsar a shara, shiyasa muma muka manta da ke, kin ri'ke miji kin manta da kowa! zuwan ma yanzu da muka yi ba naki bane, na 'Dan mu ne ko kin fada mana kin haihu?" Dariya sosai Sa'adah ta yi, tana fadin "shikenan yana godiya" tare da cire nono a bakin sa, a kafada ta saba shi, sai da ya yi gyatsa sannan ta nade shi a shawul da ke canja masa riga aka yi, ta mi'ka ma Safina da tafi makwaftaka da ita. Ido ta zuba tana yaba kyaun jaririn, ta ke ta ji sha'awar ta samu nata, ta jima tana ri'ke da shi, har sai da Halima tace " Ba za ki bani na ganshi bane?" Sannan ta mi'ka mata tana fadin "Babyn ne so mashallah". Halima na zuba ido akansa taga kamannin Uncle Mukhtar sak a fuskar yaron. A fili ta furta "Allah dai yasa kar ka kwaso mana halinsa". Da sauri Sa'adah tace "Uncle din kike cewa kar ayi halinsa? ai kuwa zan fada masa". Ta no'ke kafada, alamun ko ya ji Ina ruwanta. Har kusan maghrib sannan suka tafi, suka ajiye mata leda mai dauke da rigunan yaro masu tsada guda uku da Pampers mai 48, ta musu godiya. Zainab tana daga falo tace ku gaida gida! da kyar ta basu ledar da ta ke rabawa mai dauke da sunan jaririn!cikin kuma memo ne mai hoton Jawad. Kwana uku da suna dan kishiyar Umma ya rasu, daga ciwon ciki kawai sai mutuwa, dole ta tafi, ta taya yar uwarta zama da juyayi! mutuwar matashi akwai gigitarwa. Kwanaki biyu a jere Inna ke zuwa da safe ta mata wanka da sauran hidima, sai ta mata wankan yamma sannan ta tafi. Ganin zirga zirgar zata mata yawa kullum, yasa ta roki Baffa ya bari Sa'adah ta zo gida ko sati biyu ne, ta kula ta ita, ita kadai tasan me ta gani, da dukkan alama daki daya suke kwana da mijin ta, tunda Umma ta bar gidan. Bai tsananta ba, ya amince amma da sharadin idan mijinta bai amince ba, baza'a matsa masa ba. Tace "Ni ai da iyayensa zan yi magana, idan ka bani dama a daren nan zanje gunsu". Bai hana ba, itakuma bata yi sanya ba, tana idar da magariba ta tafi gidansu Mk, a falo duk ta same su har Hajiyan Bichi, bata bata lokaci gurin fayyace bu'katar ta ba. Dukkansu sun yi shiru!sai Hajiya Babba ce ta yi kundunbalar cewa "tunda har kika zo ba za'a hanaki ba, sai dai ki yi hakuri da kaina zan kawo miki ita, idan aka shirya". Godiya sosai Inna ta yi ,har kofar gida suka rakota suna ta yiwa juna godiya. Har ta isa gida tana mamaki! ko kishiyoyi nawa ne suka dace da kyakkawan zama irin na iyayen Mk? ko Ana samun adalar uwargida irin Hajiya Babba, mai hade kan ahalin gida babu banbanci, ko kai sukar wani ga wani, da sauran gutsiritsoma irin na tsofaffin mata masu kitsa munafunci da sunan kishi? Ko Ana samun amare masu kawaici da biyayya da sanin mutunci da alherin uwayen gida irin Hajiyan Bichi? sha'awar zamansu ya kamata tana jin inama, itama tana da abokiyar zama, ba yabon kai ba, da zata yi koyi da Hajiya Babba. Da murna ta bawa Baffa labarin yadda suka yi, shi da kansa sai ya zaku Iyah ta dawo kusa da shi duk da dai bai furta ba. Suna komawa gida, Hajiya Babba ta Kira Mk a waya, ta sanar da shi bu'katar mahaifiyar Sa'adah! ya yi shiru ya rasa mai zaice, jin shirunsa ya tabbatar mata da bai ji dadin maganarta ba, bashi kuma da niyyan amincewa. Dan haka sai ta kwantar da murya cikin hikima tace " Da na yi karambanin amincewa, har naci alwashin da kaina zan kai musu ita, amma ba zai zama komai ba, idan banyi daidai ba, sai na koma na lashe amai na". Cikin takaici iri iri yace "Ni bance ba, tunda kin amsa shikenan! amma dai sati daya za ta yi". "Akan mai zaka 'kayyadewa iyayen ta kwanakin da zata yi a gaban su, ba ka ga mutunci irin nasu ba? neman alfarma suka zo yi gaban iyayenka, saboda girmama hakkin aure. ba dan basa sonta, ko dan sun gaji da ita suka dauketa suka baka ba, yau kusan shekara guda. me zai sa ka shata musu layi dan su nemi su kula da lafiyar yarsu?" Ya yi shiru yana jin maganar na shigarsa sosai, ya nisa yace "Shikenan Hajiya duk yadda kika yi dai-dai ne" Dadi ya kamata! ta shiga jero masa addu'ar albarkar ubangiji a dukkan kasafin sa. "Tunda ka yarda da hukuncin da nayi, duk da ba ka so! Ni kuma zan fada musu sati uku za ta yi maimakon wata guda". Takaici ya sha'ke masa wuya, wai har sati uku, shi ya dauka anyi wuta ta yi sati biyu, to da fiye da wata ake nufi zata yi ko me? Sa'adah na zaune a daki tana shayar da Jawad, shi yana falo yana musu guga, ya tattara kayan ya kulle ya kashe iron din saboda yadda jikinsa ya mutu da 'bacin rai. ' Jiki a mace ya shiga 'dakin bai kalleta ba, ya wuce ya hau gado yana jin zazzabi na namen kama shi. A gigice ta dinga tambayar sa lafiya kuwa, me ya same shi? Jinsa shiru yasa ta shimfi'de Jawad! ta isa kusa da shi tana ta'ba jikinsa ta ji ko zazzabi ne yake san'darsa. Ras ta ji jikinsa, sai rashin kuzari, ta shiga tambayar sa, ya kasa bu'de baki ya mata bayani, amma ganin zata masa kuka, ya fisgota jikinsa ya kankameta, yana sakin ajiyar zuciya. Tsawon lokaci suna haka, cikin rashin kuzari yace "Tun yanzu na fara kewar ku" Gabanta ya fadi ta kalleshi ido a bude "Tafiya zaka yi ka barmu?" Sai kawai ta fara hawaye, ya kalleta yana jin sonta na sake daskarewa a zuciyarsa, shagwabarta, rauninta, soyayyarta na sake gigita shi. Ya sake kankameta sosai yace " Kune dai za ku tafi ku barni, yanzun nan wayar da kika ji inayi!Hajiya Babba ce, wai na shirya miki tafiya gida, ki yi wankan acan". Da'di ya cika 'kalbinta! ta ji tamkar ta tashi ta taka rawa, sai kuma ta ga yadda ya shiga damuwa akan tafiyar ta, idan har ta nuna murna! Tamkar ta baro bacin rai a tsakaninsu, dan haka sai ta hadiye dukkan murnar ta! Ta tattaro dukkan damuwa ta yaba akan fuskarta da jikinta. Cikin shagwabe fuska har da sake matso hawaye ta hau fadin " Ni dai ba zan je ba, ai kaima kana kula da mu sosai". Idan yace bai ji dadin kalamin ta ba yayi karya, ya shiga kissing dinta ba kakkautawa, ganin zai wuce iyaka, yasa ta katse shi, ta lura ya manta da halin

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});