Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

girgiza kanshi, "Ada idan mun hadu sai na faki idon mutane naga ba kowa, sai na ce mata Sa'ade ko na ce Iya Basiru, sai na ga ta fara sababi, kawai sai na sulale na bar ta a wajen." Ya sake sakin dariya "Ashe ke ce kike tsokanar ta duk mu hadu a ba ta rashin gaskiya?" "E to ai haushi nake a lokacin, ta dauke maka hankali, har sai da ta kwace mini kai!" Ya nuna ta da yatsa, "ke ko! kin san irin su Sa'adah suna dadewa kafin a gane cutar su da ake yi, saboda hayaniyarsu sai sun dade kafin a gane a fahimci gaskiyarsu. yau kwana biyu ban je gidan Hajiya ba can na nufa idan kuma za ki dauko mayafinki, Bismillah". Kai ta girgiza alamar a'a tare da cewa, "Na fi son na je na wuni, ka gaishe ta da kyau!" Ya fice ita kuma ta bi shi da addu'ar dawowa lafiya. Da sallama ya shiga gidan, a tsakar gidan ya same ta zaune kan tabarma tana jin radio, kusa da ita ya zauna. suka gaisa tana tambayar Farida, daga nan kuma tayi shiru da bakinta. "Hajiya wai har yau fishin rashin zuwanki wurin Jawad din ne? Ni ma fa ban ji da wuri ba, ina Bauchi ya yi mini waya daga can na zarce amma ki yi mini uziri, kiyi hakuri." "Ni abin da ya dame ni, ba a kai masa abinci da 'yar miya ba!" Dariya ya yi sannan ya ce, "Ai yanzu ba a barin su su tafi da shi hostel, iya wanda suka ci a wajen shike nan, saboda kwalara sannan kuma a can na tarar da uwarshi ta je masa da abincin". Shiru Hajiyar ta yi tana jin takaici rashin Sa'adah cikin ahalinta, ba karamar asara ba ce. Tunda ita kam a iya zamanta da yarinyar ba za ta ce ga ta'kamaiman laifinta ba, sai yan 'kananun kura-kurai da ko 'danka na cikinka wani lokacin zai yi maka. Duk artabun da ake yi tsakanin uwar miji da surukan zamani ita ba ta san shi a zamanin zaman Sa'adah ba, yarinyar ta iya zama da manya. Komin fa'da da rashin ha'kurinta, ita dai ba ta ganin su, tunda dai mafi yawa akan kishi take fadan. duk mace kuwa ba a raba ta da kishi, sai dai wata ta iya dannewa wata kuma nata mai zafi ne. Sannan abu mafi dadi a halayen Sa'adah yadda ta yarda ta isa da ita, duk yadda ta murde, da zarar tasa baki za ta ha'kura ta bar maganar. Amma ga shi nan, shi da ta haifa ta kasa sarrafa shi, akan komen yarinyar, shi yasa take jin kunyarta, take jin nauyin iyayenta, duk da aure rai ne da shi, Ubangiji idan ya 'karar da zama ba yadda za ayi. Ta kalle shi, "Kuma kun gaisa da ita?" Tausayin uwarsa ya tsirga mishi ya san babban burinta Sa'adah ta sake zama surukarta a karo na biyu, ya yi 'dan murmushi "Hajiya ai da ma muna gaisawa" Harara ta galla mishi tare da cewa, "Ina ce nan da ta zo duba Jawad akan idona ba ku gaisa ba?" "An yi haka Hajiya amma ai ba ni zan gaishe ta ba ko?" "Kai ne namiji, Kai ne zaka fara magana tunda gidanku ta zo, kuma uwar dan ka ce!" "To ni Hajiya ba uban 'dan nata ba ne?" Kwafa ta yi, "Wallahi ba ka ta ba bata mini rai na ji zafinka sosai ba sai akan Sa'adatu." Kai tsaye ya ce, "Na ba ki ha'kuri Hajiya! yanzu ma shi zan ba ki, ki yi ha'kuri ki yi mana adddu'a." "To tun yaushe nake adduar?" Niyya ce dai da ba ka yi ba!" Ya katse mata fadan nata ta hanyar cewa, "Da kyar fa Jawad ya sa ta gaishe ni, kuma na taho a hanya na ga motarsu ta lalace, wai ni da abin arziki, na tsaya na ce su zo mu taho amma yarinyar nan a gaban jama'a ta tsinka ni! Ko kallon tsiya ba ta mini ba, bare na arziki." Ya nisa sannan ya ci gaba da fadin, "Amma kullum sai ki yi ta dora mini laifi, ki yi ta ganin ni ne marar kirki, alhalin tsiyarta tafi ta tsohuwar mota. Inda tana son sake zama da ni ai lallaba ni za ta ci gaba da yi, tunda dai ta san ba na son rashin kunya." Tunda ya fara magana ta zuba masa ido tana nazarta shi, tsawon shekaru bakwai da rabuwarsu, yau ne ya bude baki yake magana mai tsayi a kanta. Ta kuma lura da sassauci da afuwa mai yawa akan lamuranta a yau, ta tuno farkon rabuwarsu da ta nuna iko irin na uwa, akan sai ya mayar da ita tilas, yasa mata kuka riris lamarin da yasa ta janye takunkumin dolen da ta mishi. Yana rufe baki ta ce, "To saboda Allah wanne irin ha'kuri ne bata ba ka ba? So kake ta tabbata tana bin ka kana walagigi da ita? kuma ko don ka nuna na isa da kai, ka ji abin da na ke fada maka, saboda rayuwar 'danku ta inganta, yau yaro ba abu mai dadi a wajensa irin ya bude ido ya gan shi a tsakanin uwa da uba. Amma ku iyayen yanzu ba ku cika duba wannan matsalar ba." Ajiyar zuciya ya saki, "To shike nan Hajiya In sha Allah zan je na yi istikara ba za ta gagara ba!" Nan da nan Hajiya ta hau murna har da hawaye take sharewa tana kuma fadin, "Na gode, Allah ya tabbatar da alheri, da ikon Allah akwai alheri tsakaninku. Duk ba'kin cikin da na kwashe shekarun nan a cikinsa, wannan maganar kadai ta sanyaya min zuciyata, Allah ya yi maka albarka." Ta mi'ka hannu ta dauko wayarta, "Kira mini Yayar ku". Ya karbi wayar yana cewa, "Me za ki ce mata?" "Na shaida mata wannan abin arz'kin mana, duk wannan bacin ran ai da ita muke yinsa!" Ya kalle ta, "Amma Hajiya na ce sai na yi istikara fa, idan kuma ban sami nutsuwa da abin ba, a zo a ce na yi baki biyu? Ni dai na ro'keki, ki yi shiru da bakinki, mu yi addu'a nan da kwana uku muga mai Ubangiji zai rinjayar mana a zuciya." Ajiyar zuciya ta yi ta ce, "Da ikon Allah ma alheri ne, jiya mun gaisa da Ahmad." Ta fada cikin jin dadi,"Ai ni tun ina Bauchi rabon da mu gaisa ya ce mini wai satin sama zai zo." Addu'a ta bi shi da ita kamar kullum, ya mi'ke, "Hajiya bari na tafi Magariba ta kawo kai" "To ka gaida Farida, ya jikin nata dai?" "Da sauki da na ce ta zo mu taho tare, ta ce yini ta ke so ta zo ta yi miki." "Ina zuba ido Allah Ya kawota lafiya." Ya amsa da "Amin!" Ya fice yana fadin, "Allah Ya tashe mu lafiya." Ta bi shi da kallon 'kauna zuciyarta fes! Tamkar wacce aka mayar da aurensa da uwar dansa haka take ji. Ta san shi kansa sai ya fi samun nutsuwa idan yana tare da Sa'adah saboda ita shaida ce na tsananin son da yake mata. ta tuna jinyar da ya yi a dakinta a dalilin rabuwarsu.

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});