Chapter 134
Chapter 134
kin nutsu ba. Mutari shi nake so ya zame miki miji a karo na biyu". Da rawar murya ta ce "To Baffah! Na ji, na kuma amince zan yi maka biyayya, zan yi ha'kuri na zauna lafiya da shi komai runtsi". Da murna Baffa ya ke cewa "Na gode miki in sha Allah ba zaki yi nadama ba, ubangiji ya miki Albarka, ya zaunar da ku lafiya, ya baku zuri'a mai albarka". Ya nisa ya ce " ku shirya gobe zamu je Gogel ki fa'dawa Yaya Ayuba kin amince ba dole na yi miki ba, Sannan ku samu lokaci ku gano Mutari domin yana jin jiki" Da sauri lya mike yana cewa "Bari na bi su Alhaji na fa'da musu wannan labarin mai da'di". Inna ta bi bayansa da ido har ya fice daga gidan, tana ayyana girman soyayyar da yake yiwa Mukhtar. Kai tsaye gidan Alh Isa ya dosa, a kofar gidan ys tarar da Dr 'Karfi zai shiga mota, ai kuwa ya ce "Mahmouda zo mu shiga, ba tafiya zaka yi ba". Baffa da murna yake fa'da musu "ai yanzun nan yarinya ta tabbatar masa ta amince, dan haka ku zama cikin shirin zuwa Gogel, a satin nan. Domin a son raina ku tafi da sadaki, a ranar da kuka je a daura auren a huta, kafin ta sake botsarewa saboda na lura kishin banza ta bari yake rinjayar ta". Daga Baba umaru har Baba Isa kowa ya yi shiru amma suma jinjina alherin bawan Allahn nan suke yi, da karfin son da yake yiwa 'dansu. Baba Isa ne ya yi karfin halin cewa "Malam Basiru ka dai matsa mata ta amince, gashi muma zamu sake yin son rai, mu amince da abin da ka zartar domin a samu lafiyar yaron nan ta dai-daita, bamu da bakin godiya, abin da zamu ce maka daya ne, da ikon Allah mu kabawa amanar yarinyar nan, mune iyayensa abin da ya faru a farko ba zai sake maimaituwa ba da ikon ubangiji. Kira mini yarinyar a waya" Baffa da ya san bashi da fargaba da azama ya fito da wayarsa. Bugu 'daya ta dauka, ya ce " Baban ku na Na'ibawa ne zai yi magana da ke". Kalaman kwantar da hankali tare da yabo da kuma girman mai hakuri Alh Isa ya dinga yi Mata, ya sake jaddada mata kar ta sake yin shiru har sai abu ya girmama, komai ya taso matu'kar yafi karfinta to ta sanar da shi zai magance mata da ikon Allah. Ya rufe maganar da cewa ko kina da korafi domin mun tsayar da kwanaki biyar masu zuwa na daurin auren ku". Zuciyarta ta buga sosai, cikin rishin kuka ta ce "Ba ni da matsala Baba! Amma zan ro'ke ka dan Allah a bari sai na kintsa sannan ayi tariya". Da sauri ya ce "Na miki Wannan laminin ki shirya a nutse, ai na san tutsiye Malam Basiru ya Miki ko na ce karfa-karfa, dan haka daga wata daya zuwa wattanni shida ki yi shirinki a hankali, bu'katar mu dama a daura auren hankalin kowa ya kwanta". A yammacin ranar suka je asibiti ita da Inna har da Sumayya. Har suka gama zamansu barci yake yi, wannan barcin shike daga hankalin kowa, ya rame kwarai da gaske. Har waje Hajiyar Bichi ta rako su, tana ta faman godiya, yayin da tausayin Hajiya ya lullube Sa'a, kallonta kawai take yi saboda yadda ta zabge ta yi zuru zuru tabbacin tare suke yin jinyar ita da Mk. Cike da rauni ta ce musu "Idan har zuwa gobe bai samu sassauci ba, zan tura Ahamad ya dauko Jawad ya zo ya ga ubansa don".. sai kuka ya kwace ta kasa karasawa. Jikin Inna ya mutu kwarai da gaske, ta dinga bata ha'kuri tare nuna cewa cuta ai ba mutuwa ba ce. Har suka isa gida ba mai cewa komai saboda ba su zaci haka jikin Mk ya yi tsanani ba. Washagari cikin ikon ubangiji jikin Mk ya yi sau'ki domin har cire masa oxygen aka yi, sannan ya yini idonsa biyu. Akan idonsa Inna da Sumayya suka iso, sosai ya ji da'din zuwan su tunda ya lura, sune kanwa uwar gamin wurin tunzura Iyah, sune suka hau dokin na ki, da tallafin su ta sami kwarin guiwar yi masa bore. Amma da ya tuna wai Sa'adah ya gani da Khalil sai ya ji wani irin kunci ya mamaye zuciyarsa! Tabbas ya yarda a duniyarsa bashi da wani kalubale irin Yaron nan, sannan yadda Khalil ya zama tsalelen saurayi na kerewa Sa'a ya sake tayar masa da hankali kwarai da gaske, domin kowacce mace ta ganshi zata so mallakarsa a matsayin miji. Ba komai ke nukurkusar Mk ba irin kishin Khalil, a sanadinsa ya rasa aurensa da matar da yake so fiye da kansa, gashi har yanzu basu rabu ba, ya tabbatar Khalil ne ke da nasara akansa, wani irin karfin zuciya ya shige shi, ya dinga kalubalantar kansa meyasa ya kasa mantar da shi a zuciyar Sa'a tamkar yadda ta mantar da shi soyayyar Farida a lokacin da suke tare. Ya saki ajiyar zuciya yana jin ciwo mai yawa a kirjinsa mafi girma a ciki haushin Sa'adah yake ji kwarai da gaske, a gaban kowa take fa'din bata sonsa, amma dan lalacewa tana soyayya da yaro sa'anta. Su Innah na zaune Farida ta iso dauke da kwandon zuba abinci. Tana kallon Sumayya ta gane sister din Gogel ce, duk kuwa da Sumayya fara ce tas. Har kasa ta tsugunna ta gaishe su. Hajiyar Bichi ta ce mata "Kakar Jawad ce da Yayar Mamansa" Da girmamawa ta sake gaishe su, a ranta sai take ganin Gogel da yayarta dan sun yi kyau ba zai zama abin mamaki ba, domin ko a yanzu da Inna take cikin shekarun tsufa, tana nan da kyaunta, mai kyakkawan jiki ce da yake boye tsufa. Wata'kila haka mahaifin su yake, dan ta lura ba kammanin Inna a tare da Gogel, Sumayya ta fi kama da ita, wanda hakan na alamta cewa mahaifinsu ma ba baya bane. Sumayya ta 'karewa Farida kallo tsab, takaicin Iyah na kamata da ta dinga kukan Mk ya auri Farida dan ta fita kyau ne, a yau da taga zahairin Farida ba hoto iya fuska ba, sai take ganin ba karamin kerewa Iyah ta yi mata ba. Kawai fararen mutane suna da kwarjini ne ta yadda ake ganin kyaunsu ko da kuwa masu 'karancin kyau ne. Farida bata dade da isowa ba, su Inna suka yi sallama suka tafi. Suna isa gida suka tarar da Sa'adah cikin kwalliya ta birgewa, amma tana kwance a falo tana kallo. Inna ko zama ba ta yi ba, ta hau ta da fa'da "Iyah cewa ki ka yi zaku tarad da mu a asibitin tare da Zainab, ashe karya kika yi mini?" Cikin rashin damuwa ta ce "na shirya jiranta nake yi". Kafin Inna ta sake magana Zainab ta kira wayarta, sannan suna jiyo horn dinta tabbacin ta fita, ba shigowa zata yi ba. Ta mike tana fa'din "gata nan ma, sai mun dawo". Sumayya ta ce Yanzu irin wannan kwalliya tamkar kin manta asibiti zaki ba gidan biki ba?". Dake Yan darun akusa suke ta ce "Anty ke kika manta cewa ni wannan ban
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157