Chapter 142
Chapter 142
ni wallahi ki yi magana, bana so a kaini bango, ban so na fusata, dan kuwa komai yana iya faruwa". Mamaki ya kamata, ko da yake a halittar maza ne, idan suna son abu idonsu rufewa yake, ta yadda zasu iya murje kunya su yi abin da za'a dauki shekaru ana Jin nauyin abin da suka yi din". Ta rasa inda zata sa ranta don kunya, domin kuwa ta gama gane tsananin zakuwar da ya yi ya kebe da Sa'a. Amma sai ta ce "To tashi ka fitar mini, ai kaga fita zan yi". "Kwanciya zan yi, na huta, ki je ki dawo, bana Jin da'di ne da na Kai ki, ko ki zauna na Kira Abbas ya kai ki". "Wallahi ba zaka kwanta mini a gado ka mini sake sake ba, ko kunya ba ka ji, ko Jawad idan yana kwance wataran takura nake yi, bare kai, baka tashi zuwa mini sai ka yiwa yarinyar arziki rashin kyautatawa. Dan kawai kasa na ga bekenta, to nikam har yau banga laifin Sa'a ba, sai nauyinta da nake ji". Ya mata shiru ya dauki ledar zogalensa ya fice, tunda ta riga ta rantse ba zai kwanta ba. Ya fita yana fa'din "Na tafi Hajiya, Sa'a ta ri'ke ki gam, ta tattare komai a gunki, ai shikenan, nima sai na hada kai da Farida baiwar Allah". "Komai zaka fa'da, ka fa'da ni Farida bana ganin laifinta, bata mini komai na laifi ba, Nima kuma na sani bata kuka da Ni, sai dai kuma ko kai wallahi baka fi mini Sa'a ba". Ya fita yana cewa "ai shikenan sai ta zuba ruwa a kasa ta sha, ta nema ta samu fitinanniyar yarinya kawai". **** Sai da ta aka yi sallar la'asar sannan suka bude kayayyakin da Mk ya jido Mata, wadda kayan shayi, da sabualan wanka mai tsananin gyara fata na *OLAY* *(quench)* ya hado mata setin su har da bath gel dinsa, da mayukansu. Sai kayan ciye ciye na gwangwani kala kala tamkar zata bude kanti. Indomie da kwai suma ga su nan birjik. Inna ta yi galala ta ce " ban gane wannan siyayyar ba, kuna nufin haka zaku zauna, ba za ki tare ba? Dan na ga wannan kayayyakin yana nuna cewa ba yanzu zaki tare ba". "Eh Innah ni na ce ba yanzu ba, domin ai ban shirya komai ba". Ta nisa ta ce " Kika yanke hukunci babu shawarata, ko ta Yayarki saboda kawai kin zama uwar kanki! Ki sani to ba dabara kika yi ba, tunda an riga an daura aure, ai ba abin da shari'a bata bashi dmaa ba, bijirewar umarninsa kuwa ai kin san yana nufin tsinuwar mala'iku ne akan ki. Haka kawai sai kin janyowa kanki ya gama zumudin ki, a titi, ke dai naga sadda zaki yi aiki da lura". Kunya ta kama Sa'adah! Amma ta waske da cewa."To yanzu Inna sai a sake kai ni ba kayan d'aki alhalin yanzu Ina da kishiya?" Ta fa'da a shagwabe. Dake Innar mace ce nan da nan ta yarda da ra'ayin Sa'a na bai kamata ta je babu kayan d'aki ba alhalin tana da kishiya diyar masu kambun susa. Ta nisa ta ce " Bari Baffan ku ya zo sai a siyar da dayan filin da ya rage, sai ki hada da albashinki na watan nan tunda ya raba tsakiya, ki yi abida ya sauwaka ayi tariyar nan cikin girma da arziki". Ta turo baki gaba Inna ki bari dai nan da wata uku, kinsan ai na ce na barwa Baffah kyautar filin, yanzu kuwa ai ba zan koma na ce na fasa ba". To kayan Baffanki ai naki ne, Ina jiye miki tsiyar namiji Iyah! Muutar din nan fa na riga da na gane shi bashi da kunya ko ka'dan, ba abu mai wahala bane a gidan nan ma, ya yi abin da ya ga dama tunda Baffanku ya daukake shi ba ka'dan ba". **** Kwanakin mako da zuwan Mk wurin Sa'a har yau bai sake zuwa ba, bai kuna yi mata waya ba, abin da yake ta cin ranta kenan, ya sake tunzurota, idan bata tare ba, ai dai tana da hakkin ya duba lafiyarta, wato ya kawo mata kayan abinci saboda ita ci kawai ta sani da kwalliya. A na cikin haka wata waki'ar ta kunno a jahar Sokoto inda aka samu matasa sun kasa ha'kurin hukuma ta dauki doka, saboda an tabowa musulmi inda basa iya ha'kuri matu'kar aka tabo wannan matsayin. Dukkan hankalin musulmai a tashe yake an zuba ido, an kasa kunne domin aga irin hukuncin da za'a yiwa wadannan matasa. Kungiyoyin musulmai kashi daban daban sai kiraye kiraye ake yi akan akaiwa matasan nan dauki. Kungiyar lauyoyi musulmai reshen jihar Kano ta bawa wadanan matasa lauyoyi hamsin da suje su harci zaman kotun da za'a yi a gata, su kuma basu kariya. Cikin wadanda aka tura har da Sa'adah. Baffah da Innah sai murna suke yau ga yarsu zata je ta kare martabar Ma'aiki, ilimin Iyah bai musu da'di iri a wannan karon ba." Da murna Baffah ya ce " yaushe zaku tafi?". "Jibi zamu tafi, dan mu sami zaman kotun, tunda gata da sassafe za'a fara shari'ar". "To ki 'Kira mijinki, ki sanar da shi, tunda dai ba zaki yi tafiyar bai sani ba". Ta amsa da to badan ta so ba. Tun yamma take kiransa yana gani, amma ya yi biris, bai dauka ba,sai bayan magariba wadda hakan ya sake fusata, Sa'a ta botsara.😄 Ya dauka, amma ta yi shiru, sanin da ya yi dabi'arta ce ba zata fara yi masa magana a waya ba. Sai ya ce "Ina jinki, na ga 'kiranki rututu, kin gama mini shirin ne, na zo na dauke ki.?" Ba'kin ciki ya tokare mata wuya, wato shi a haka ya barta ma? Ta daure ta ce "Dama Sokoto zani". "Sokoto zaki je?" "Eh" ta amsa a ta'kaice. "To ba zaki je ba". Daga haka ya kashe wayar ya barta da waya a kunne. Ba'kin cikin da ya turniketa ba'a magana. Hawaye ya kwace mata. A hakan Baffah ya shigo ya sameta, ta fada masa abin da Mk ya ce. Baice komai ba, ya fita waje. Ya 'Kira Mk a waya, ya ce "lallai ka zo ina nemanka". Mintina ka'dan ya iso tunda dama yana cikin shagonsa. Ko gama gaisawa ba su yi ba. Baffah ya ce "Iyah ta ce wai ba zata je sokoto ba?" Ya sauya fuska ya ce "Eh haka na fa'da mata Baffa?" Ai kuwa Baffah ya dauki salati yana fadin "Lallai kuwa, ka bani mamaki, ana tsayawa garabitin mutane a gaban shari'a, balle a taba janibin Ma'aiki. Ai kuwa shine mafi tsayawa a kare darajarsa." "Da wata irin murya mai nuna mutun na wurin da zai yi shagwaba son ransa. Mk ya ce "Baffah sanar mini fa kawai ta yi, ba wai izini ta nema ba". A wannan karon ko ka'dan Baffa bai karbi uzzirin Mk ba, kawai umarni ya bashi akan lallai ya barta taje ta wakilce su, wurin bawa Ma'aiki kariya. "Shikenan Baffah zata je, amma ban yarda ta yi tafiyar nan cikin kungiya ba, ta jira zan zo na kaita, idan sun kammala na dawo da ita" "Yauwa Ubangiji ya maka albarka, ya kore
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157