Chapter 45
Chapter 45
abin da za ki na fada mini ba na son kau'din baki." Duk yadda ya so ya tafi ya bar ta a gurin kasawa ya yi, ita kuma ta kafe akan ba za ta tafi ba, shi ya yi tafiyarsa ya 'kyale ta. Da kyar da jubin goshi ta yarda ya tarar mata Adaidaita, bayan ya rantse zai zo gida ya same ta, sannan zai 'dauki kiran ta. Yana tsaye yana kallon su har suka bar wajen. Wata ajiyar zuciya da bai san yana ri'ke da ita ba ta kwace, a fili ya ce "Wacce irin yar daru na kwaso wa kaina ne? Da motar nan ta taka ta, ina take son na sa raina? Me zan ce da iyayenmu idan aka gane muna tare ta sami wannan hadari? Ya dade a tsaye yana mamakin irin son da yake wa Sa'adah. Ya dauka idan ya gan ta ba zai ji komai ba, ya dauka kaifin son ta ya dakushe, ashe ya nan daram. Musamman da ya ga mota na shirin take ta sai ya ji zai iya rasa ransa don ya tserar da ita, ko muzuran da ya mata na karfin hali ne kawai da son kwatar kansa a idonta. Tana isa gida ana sallar La'asar, sai da suka yi sallah sannan ta ba wa Inna sakon da ta karbo, ta koma daki ta hau kiran MK. Sai da ta kira har sau uku bai 'daga ba, shi kuma ya fito a Masallaci ke nan kiran ya shigo, bai daga ba sai da ya koma dakinsa ya kwanta sannan ya 'kira ta. Har ta fara hasashen da ma zai iya rantsuwa akan 'karya? Sai kuma ta ga kiran sa ya shigo, da sauri ta dauka sai kuma ta yi shiru ta tura baki gaba tamkar yana ganin ta. Shiru ya biyo baya tamkar ba kudi ke bin iska ba. A shagwabe ta ce, "Na gode!" Ya ce, "Godiyar me kike yi?" "Ka cika al'kawari, don Allah ka yi ha'kuri wallahi na horu ba zan sake yi maka laifi ba." Ta fa'da da rauni a muryarta. Jikinsa ya mutu, wata irin kasala da ba ta da nasaba da gajiya ko barci ta lullube shi, murya a dakushe ya ce, "Kin bata mini rai, kin tayar mini da hankali, kin jefa ni cikin wasi-wasi mai yawa, kin janyo mini raini." "Ka yi ha'kuri!" Ta fada da sauri. Shiru ya yi ba tare da ya yi magana ba, saboda yadda ya ke fama da kansa, ji yake ina ma ya jita a jikinsa. Murya ba amo sosai ya ce, "zan fada miki, ba na son yaron nan. Ina bakin cikin tarayyarki da shi, wannan ne karon karshe da zan miki afuwa a kansa, ba don girman son da nake miki da kunyar Baffa ba da na ha'kura da ke Sa'adatu. Saboda kina cutar da ni, da ni kika gani da Farida da ban san kalar tashin hankalin da za ki mini ba. Amma saboda yadda nake son ki, na ke gudun bacin ranki haka na rufe ido na rabu da ita da dukkan lamarinta. Ni kuma kin kasa tsayawa gare ni ni ka'dai." Yanayin muryarsa da yadda ya ke maganar cike da rauni sai ita ma ya jefa ta cikin wani irin yanayin da duk mai lafiya ba zai iya kauce masa ba, tsikar jikinta har tashi take yi. "Am sorry!" Ta fada a gajarce tana jin ina ma inama... "Shike nan ya wuce amma kisa a ranki cewar yaune karon karshe da zan saurare ki na miki afuwa akan Khalil". "Na gode my love!" Mamaki ya kama shi, karon farko da ta kira shi da wani suna bayan Uncle. Ya ce, "maimata abin da kika ce?" Dariya ta yi "Thank you na ce!" Sai ya saki maganar ya ce, "Ba ni labari." Haka suka sha hirarsu cike da Begen juna, dukkansu sun tabbatar sun yi missing din juna, sun kuma yarda farincikinsu na hannun junansu. Washagari da yamma ya zo, ba Sa'adah kawai ba, hatta Inna sai da ta yi murnar zuwansa, hira suka yi cikin tattalin juna, har ya ba ta labarin irin gyaran da yake mata a gidan da za su zauna. Tun daga wannan lokacin Sa'adah ta yanke hul'da da Khalil saboda ba karamin tashin hankali ya janyo mata ba. Hankali ya kwanta sun shirya da MK amma ta 'kullaci kalmar ballagazancin da ya jefe ta da ita ba ka'dan ba, ta kuma ci alwashin maganar ba za ta bi iska ba, lokaci ta ke jira. Haka kwanaki suka yi ta zuwa suna wucewa, har watan azumi ya kama al'ummar Musulmai kowa ya koma ga Allah ana fatan dacewa da Rahamar Ubangiji. Zuwa wannan lokacin shirye-shirye ya yi nisa a bangaren MK, an kammala gyaran gida, gyaran da ya dawo da gidan tamkar sabo. Mahmoud ne ya hado wa Sa'adah kayan shan ruwa da kayan sallah masu tsada har set biyar da takalmi da jaka set uku sai tarkacen kayan kwalliya da turaruka. Tare suka kawo mata, da za su tafi kuma ya sake ba da kudin 'dinki wanda ta 'ki karba sai da MK yasa ba ki sannan ta karba. Yawan kayan da kuma tsadarsu ya dan rage mata damuwar rashin lefe musamman idan ta tuna tana da kayan wurin Alh Mamman a ajiye. Ana yin sallah da sati 'daya iyaye da 'yan'uwan MK suka hada kudadensu, aka sayo dukkan abin da za a bukata, tun daga kan gado da kujeru masu kyau da aminci suka sayo aka shirya gida ya fito sosai, labulaye da carpet suka ajiye sai satin biki za a zo a saka. MK da ya je ya ga irin kayan da aka zuba masa sai da ya yi hawayen farinciki, ya duba ya ga an 'kawata dakin Sa'adah da dan'kareren gadon da duk fariyarta ba za ta raina ba, ga kujerun ma masu kyau, ba irin gama gari ba, dayan dakin ne kawai aka malale shi da carpet aka bar shi empty, bai sha mamaki ba sai da ya shiga dakin dake tsakar gida wanda shi ne mallakinsa, an saka masa gado amma bai kai na dakin amarya ba, kowanne gado kuma da dimemiyar katifar Vitafoam a kai. Ya zauna a bakin gadon yana goge idonsa, yana mai yin addu'a ga dukkan ahalinsa, sun masa zumunci ba ka'dan ba. Ya zauna yana ganin TV da Fridge kawai ya rage wanda su kuma yayarsa Hafsatu ta ce ta aiko da su. Isowa ne ba su yi ba tunda a Lagos take. Alhaji Isa shi ya sake komawa wurin Baffa ya ce idan ba damuwa suna son a yi auren a cikin sati biyu masu zuwa. "Yadda ka ce ba ka bu'katar komai a gurinmu sai sadaki, mu ma muna ro'kon ka!Yarinyar kawai muke so don Allah!" Suka rabu cikin walwala, tare da addu'ar albarkar Ubangiji a cikin auren. Duk da Baffa ya ce ba zai mata kayan 'daki ba, kan dole ya karbi tsalelen gadon da mijin Sumayya ya aiko masa. Sumayya na zuwa ta nunawa Inna ku'din da za ta kashewa Iya, ita ma ta fito da nata ajiyar ta hada suka shiga kasuwa tare da Sa'adah, suka zabo kayan kicin na garari duk a 'ko'karinsu na kwantar mata da hankali, tunda sun san
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157