Chapter 126
Chapter 126
bazai yiwu kullum kina barin aminina shi ka'dai a gida ba, dole zamu lalubo wadda zata zauna ta kula da shi. Tababa da ke mai kunyace ta fice ta bar Mk na yi musu sha'kiyancinsa da baya gajiya. Za su tafi ta kawo turare ta bawa Jawad, da wata kullin leda mai dauke da man shafawa da na zafi ta ce na Hajiyar Bichi. Mk ya tsaya cak yana fa'din" Tababa ta Malam ki ji tsoron ubangiji, ita kuma Farida ina nata sakon, gaba'daya kin saka son zuciya a lamuran ki, saboda ba kawar ki ba ce ita" Da sauri ta koma daki ta dauko kyawawan mafitai guda biyu ta ce ga shi nan, ta yi maka fifita ni bana son sarhutunka". Ya karba yana fa'din kin fanshi kanki, yayin da mijinta ya yi gaba yana fa'din ranar da za'a mata amarya ai ban san irin boren da zata yi ba, idan ka ga yadda ta yi kukan aurenka sai ka yi mamaki, ta taya Sa'adah kuka irin wannan ina kuma ace ita za'a yiwa?' Mk ya murmusa ya ce ai kuwa dai Tababa kwantar da hankalin ki, daga yadda na ga kin iya karrama ba'ko , zaki dade kina jan zarenki, muma kaddara ce ta fado mana, Ina fatan idan kuma kaddarar ta fa'do muku ba zaki yi watsi da kyawawan dabi'unki ba". Ya damkawa yarinyarta karama kudi, Yana ta godiya da karamacinsu, ya tafi ya barta da sanyin jiki tana addu'ar kasancewa ita ka'dai. Har la'asar Mk na Wudil domin tare da aminisa suka je ainihin gidan su Baba Isa ya ziyarce su, suka dinga sa masa aalbarka ya ajiye musu buhun shinkafa da katon din taliya, har da ku'di a kanin Baba Isa Wanda shine babba a gidan yanzu. Sai da suka fito ya ajiye Aminin nasa a kwanar gidansa, suka yi sallamah. Sun tsallake gadar Wudil ya samu wuri ya tsaya. Ya ce "Jawad dawo gaba kusa da ni, kana mini hira". Hakanan kuwa aka yi, sun zo dai dai Yar gaya, Jawad ya ce "Allah sarki Muhsin Yargaya! ko yana ina yanzu?" Ya dinga bashi labarin Muhsin da irin halin da yake ciki da matar Babansa. Nan Mk ya fahimci inda Jawad ya samu dalilin juyawa Farida baya, ya dinga jin tausayin yaran da suke fuskantar kalubalen rashin rayuwa tare da uwarsu. Cikin hikima ya ce "Ashe Muhsin ya fa'da maka u have to be careful with Aunty saboda kar ta raba mu?" "Eh mana Malam! Saboda na san kai baka san hakan zai iya faruwa ba". Mk ya yi murmushi ya ce "Jawad kowa da halinsa! Da zata raba mu da tuni ta yi hakan, fa'da mini ta ta'ba dukan ka lokacin da muke Uk?" Ya girgiza kai alamun a a, Mk ya zarce da fadin "abinci ne bata baka ko?" Da sauri Jawad ya ce "Ah Malam tana ba ni, every day sai ta cika mini lunch box dina, abincina ya fi na kowa yawa, kullum sai na dawo da shi". "Ka ga kenan ba halin su daya da Waccan da abokinka yake baka labarinta ba". "Amma Malam ai ita kake so ba Mami ba". Jikin Mk ya yi mugun sanyi a shekaru sha uku Jawad ya yi wannan maganar? Al'amarin yaran yau idan kana daukar maganar su tabbas zasu raba tsakanin ka da jama'a ne, ka yi ta ganin tamkar kitsa musu magana ake yi. Ko kuma ana koya musu iyashege ne alhalin kuma abin a jikinsu yake, sai dai ayi ta nuna musu kyakkawar turba cikin azanci da nasiha. Mk ya nisa ya ce "wa ya fa'da maka bana son Mami? Ita ce fa ta haifa mini kai! Kasan kuma u are my only son, dole kuwa ta zamo very precious to me". Da'di ya kama Jawad ya ce " To yaushe zata dawo gidan mu, tunda we are Muslims, polygamy is allowed, above all ma ka mini al'kawarin zan dawo hutu na ganta a gidanmu ba a gidan Baffah ba". "Eh na yi maka ban kuma manta ba. Amma matsalar itace bata mini magana, bata gaishe ni, har Baffa yana mata fa'da amma still bata ji ba". "Ni zan fa'da mata ta daina yin haka tunda kullum sai ta ce mini arogance ba kyau, ba dabi'ar mutanan kwarai bane". " Yauwa sannan ka fa'da mata, kana son ganinta a gidanmu, if not jirgin nan da zaka siya mata zai zama nawa". Dariya Jawad ya dinga yi yana cewa" Malam ka damu da jirgin nan, amma ai yanzu na ce har da kai zaka shiga. Ni ban san me yasa ta daina son dawowa ba, bana manta sadda take kukan so take ka zo ka dauke ta mu koma gidanmu" Jikin Mk ya yi sanyi ya ce "tafiyar da muka yi, muka barta ne, amma idan zan sake komawa da ita zan tafi, kai kuma ka zauna tare da Anti a anan". "A a Malam gaskiya ba a yin haka, da ni za'a tafi" " To na yarda da kai zamu tafi, yanzu idan ka je gurinta sai ka yi ta bata hakuri ta dawo ta zauna da mu". Murna tamkar Jawad ya zuba ruwa a kasa ya sha, wani irin farin-ciki ya bayyana a dukkan jikinsa Sun iso kano Mk ya kalli Jawad cikin uniform dinsa sai ya dinga tuno shima lokacin da yake makarantar su ta 'Karaye. Haka yake tamkar Jawad, sai dai da alamu Jawad yana iya zarta shi tsayi domin a yanzu ma ya kusa kamo shi. Tsayin Jawad da saurin da karatunsa ya yi sai ake ganin tamkar ya zarce shekarunsa. Da tarin kauna ya ce " A ina kake son yin hutunka?" Kai Jawad ya sunkuyar ya ce "gidan Hajiya". Mk ya ce "Antinka fa tana can ta shirya maka something special". "Zan je amma ni gidan Hajiya zan zauna". "Me yasa to ba zaka je unguwa uku ba?" Ya marairaice tare da cewa " Na san idan na ce can zani ba zaka yarda ba". Da sauri Mk ya ce na yarda Jawad! Ka yi hutunka duka acan idan kana so". Jawad ya kalle shi da mamaki! ya ga seriousness a fuskar Baban nasa ya kasa gasggatawa ya ce " please Malam are you serious, are u sure?" Da sauri Mk ya kada kai ya ce very sure Babana! Yanzu zamu je gida kaa ci abin da Anti ta shirya maka, daga nan sai mu zo ka gaida Hajiya, sai mu koma ka kwana tare da mu, tomorrow morning da kaina zan kaika gidan Baffah ko gidan Anty Sumayya ko ina kake so nan zaka je". Ya dinga murmushi irin murmushin Sa'adah, wurshiryar da ya samu daga gareta ya sake kawata murmushin nasa". Da farin ciki sosai Mk ya ce "kyaun ka na bayyana idan kana smiling my boy". Jawad ya sa hannunsa ya rufe fuskarsa wai shi kunya. Da murna sosai Farida ta karbi Jawad ta dinga ina ka saka da shi, karshe ya shige dakinsa da komai na ciki blue ne, irin kayan alatun da aka shirya masa duk dan a hilace shi ya daina gudun gidan basu yi tasiri ba. Wanka ya yi, ya shirya ya fito ya tarar da kayayyakin da aka tanada dan shi kala kala. Farida ta dinga
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157