Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 64

Chapter 64

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,198 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wata goma sha daya ne tsakanin su, ashe matar da tayi irin wannan haihuwar abin alfahari ne a gurinta, abin a mata barka ne, don kuwa albarkar diyar Ma'aiki ta samu". Haka ta dinga rarrashin ta har ta sami nutsuwa. Ta kara da cewa "Har addu'a nake miki kar ki yi irin haihuwa ta, ko irin ta uwar mijinki, kin ga dai shi ma su uku ne a dakinsu, da bakin ki kika ce mini sai da ya shekara goma aka haifi Ahmad kaninsa, ni kuwa tun a kanki aka rufe mini kofa, ki kwantar da hankalinki, idan Allah ya sauke ki lafiya, idan mijinki ya yarda zan daukar miki Jawad ke ki ji da jariri ko jaririya". Sai Azahar ta tafi, har girki ta mata, sannan ta tafi ta bar Jawad na kukan zai bi ta ya gan ta da Hijabi. Ba ta da'de da tafiya ba, Sa'adah ta dinga jin kwankwasa kofa, ta san ba Mk ba ne tunda da key a hannun sa budewa kawai yake yi shi yasa ba ta sa sakata. Da Jawad a hannunta, ta fita ta bude kofar, ta yi turus ganin Halima da Safina a tsaye, cikin kwalliya ta burgewa sai kamshi suke yi. Har suka shiga cikin gidan wani irin kallo suke mata, na uku saura kwata, suka zauna, ita kuma ta fice zuwa kicin ta zuba pure water mai sanyi, akan tray, ta kawo musu tana cewa "Sannun ku, daga ina kuke haka?" Safina ce ta ce "Daga makaranta kin san sai yanzu aka fara daukar sababbin dalibai saboda dogon yajin aikin da ASUU ta yi". Sa'adah ta ri'ke baki ta ce "Oh kuce da students nake tare, wane course kuke yi?" Still Safina ce ta sake cewa dukkan mu Diploma in Public Administration muke yi, ba mu samu degree ba, saboda points din mu ba su kai ba, amma a satin nan zamu cike JAMB tunda an fara za mu sake trying". "Ma Sha llah! Congrats, na muku murna, ni ma In sha Allah zan yi JAMB din, gara da na ji da wuri, amma ni Sociology ne zabina ko kuma English Language". Sai lokacin Halima ta ajiye wayarta da take ta latsawa ta dube ta sannan ta ce "A ina za ki yi wannan karatun da kike fa'da? Kai tsaye Sa'adah ta ce " B.U.K mana". Dariya Halima ta yi irin ta iyashege sannan ta kalle ta, ta kalli cikin jikinta, ta sake mahar da kallon ta ga Jawad, ta ce, "Sai dai idan a gaban Uncle za ki yi karatun, tunda shi ma harshen Turanci ya karanta, yake kuma koyarwa". "Ban gane ba?" Sa'adah ta tambaya da alamun karin bayani. Ba kunya ba komai Halima ta kalli cikin idonta ta ce "Na ga ya mayar da ke akuya ne, ke kuma kin biye masa, don Allah dubi yadda kika zama just one year da aure". Kalmar akuyar nan ta bugi Sa'adah, ta kasa hakuri ta ce, ni ce na zama akuya?" "To mene ne banbancin ki da ita? Ki kalli kanki mana, 'da a hannu, 'da a ciki". Idon Sa'adah ya cika da kwalla tabbas da gaskiyar Halima irin haihuwar akuya za ta yi. Kafin ta yi magana, Safina ta tsoma baki ta ce "Ni fa tunda na zauna mamakin Gogel nake yi, ta saki jiki za ta mayar da kanta tamkar irin jakunan matan nan na kauye da ba su san komai ba sai dai su ci, su haihu duk shekara, duk iyashegen da namiji zai musu ba yadda za su yi saboda sun tara garke da shi, yo a wannan karnin wacce macen ce za ta yi irin wannan?" Halima ta cafe da fa'din "Ba ki ga yadda ta susuce ba? tamkar ba Gogel fine girl din nan ba, duk ta tsofe, ta sakar masa jiki, shi ya tsotseta da daddare, dansa ya yini yana tsotsarta, duk kuma abin da zata ci sai anraba musu da unborn, in and out suke lasar ta, ba dole ta fita a hayyacinta ba". "Sai ikon Allah, ke da karatu, sai ya gama tsofar da ke, kin daina burge shi, kiga ya dallo sabuwar yarinya, da ilimi ya gogar da ita, tunda kullum yana ganin yan mata sabbin 'kyan 'kyasa". Hankali Sa'a ba karamin tashi ya yi ba, saboda yadda ta gasgata maganganunsu, mussaman da tasan kullum a cikin ganin tsala tsalan yan matan Jami'a ya ke. A sanyaye tace "ya zanyi ne? ni kaina ban shirya haihuwa yanzu ba, sannan kuma shine yaki yarda! da nace sai dai a cire" Dukkansu dariya suka sa mata, sai da suka tsagaita da dariyar! sannan suka ce, mai yasa da kika yi arbain, ba ki je asibiti an dora ki akan maganin tsarin iyali ba?" Kafin ta amsa, sun zarce da fadin " kar ki sake yin ganganci irin haka, idan kuma kin ki ji, ba Kya ki gani ba". "Tuwo Inna ta yi mana zaku ci ko na dafa muku indomie?" Shiru suka yi tamkar basu ji ba, sai can kuma Safina tace "Ni kam bana cin tuwo". Halima bata dago ba, tace yi Indomie din kawai, amma plz kisa mana pepper sosai". Haka ta dafa musu indomie da ta ji albasa da attaruhu, ta hada musu lemon Tang a jug ta fasa kankara ta jefa a ciki. Sai da suka ci, suka gyatse, suka yi la'asar sannan suka tafi bayan sun jefa mata wasiwasi a zuciyar ta. Daf da maghrib ya dawo gida, a gurguje yayi wanka ya tafi masallaci, sai da ya dawo, ya dauko musu abincin, suna ci, ya lura Sa'adah ba ta da walwala sosai, ya tambayi ko bata jin dadi ne! ta ce kalau take, ta isar da sakon gaisuwar Inna, da fara'a ya ce "Ina amsawa, ta biyo sawunki kenan? Ina fatan dai kin fa'da mata, bani da alhakin rashin ganin ki a gidansu?" Kai tsaye ta ce "ko ban fada ba, ai tasan kaine, tunda ka mayar da Ni Akuya". Maganar ta shige shi, amma sai ya ce ban gane na mayar da ke akuya ba?" "Eh mana wata biyu da haihuwa ka sake dirka mini wani cikin, ai akuya ce mai hakan". Ya kalleta soasai ya tabbatar wannan maganar ba daga zuciya da kwakwalwarta ta fito ba, ya kuma tabbatar ba a bakin mahaifiyarta ta ji ba. Ya numfasa yace " Inna bata yi farincikin ganin ki da cikin ba kenan?" "Hmm ita da take ta murna wai dama har addu'a take yi mana kar na gado rashin yawan haihuwar su ita da Hajiyar Bichi". Ya sauke ajiyar zuciya, hankalinsa ya sake tashi, tabbas akwai wacce ta zo take kokarin birkita masa zaman lafiya a gidansa. A zahiri sai ya murmusa ya ce " Ashe adduar Innace ta sauka akan mu, ba wai akuya na maida ki ba". Ta tura baki gaba, tana jin ba zata sake yarda ta yi irin wannan gangancin ba a gaba. A kicin ya ga tray din da aka ci indomie mai dauke da fork guda biyu. duk yadda akayi wadannan bakin da ta yi ne, suka kitsa mata maganganu, tunda duk boren da ta masa a farko, ai tunanin ta bai bata irin wannan kalamin ba. Bai sake shan mamaki ba, sai da suka kwanta, ya

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});