Chapter 88
Chapter 88
cikin sanyin jiki ta kalli yadda ta ke kuka jikinta har 'bari yake yi, ga wata irin rama ta yi, har ba'ki ta ga ta sake yi mata sosai. A hankali ta;ce "kin tasa ni a gaba kina irin wannan kukan mai tayar da hankali, amma kin 'ki bu'de baki ki fa'da min mai ya same ki, ba Kya jin tsoron ciwo ya kada ni, kinsan fargaba da zullumin da nake ciki?" **** Mk na zaune a shago, amma jinsa yake tamkar a cikin rijiya saboda tsananin yadda ya takura ga wani irin matsanancin kishi ya matse kofofin numfashinsa, ya sababa masa azabben ciwon kai mai tsananin. Yawun bakinsa ya kafe sai daci yake ji har makoshinsa! ya ciro wayarsa ya kira Mahmoud ya sanar da shi, yana cikin matsala ya zo gidan Hajiyan Bichi ya same shi. Ya fito kai tsaye ya tari mai acaba(A lokacin ba a hana ba) ya kai shi gidansu, dan bashi da sukunin da zai iya tu'ki, domin al'amarin na nisa damuwar sa na 'kara girmama, wani abu ne mai tsananin ciwo ya tokare a 'kahon zuciyarsa mai azabtarwa. Yana isa kai tsaye can cikin dakin Hajiya ya shige ya wuce ta a falo tana yanka kankana. Mamaki ya kamata, ba zata iya tuna yaushe rabon da ya shigo ya ganta a falo amma ya zarce uwar daki ba. Ta yi jim, tana sauraronsa ganin fitowarsa, amma abin mamaki mintina fiye da goma sun shude bai fito ba, dan haka sai ta mike ta bi bayansa dan jin ba'asin wannan sabuwar dabi'a. Yanayin da ta tarar da shi ya tabbatar mata akwai matsala, da azama ta isa gareshi tana cewa lafiyar ka kuwa? A hankali ya ce"kaina tamkar zai fashe Hajiya" Da jimami ta ce "Ai da Abbas ko Akil ka kira wani ya raka ka asibiti, a kwanta da ciwo ne ba a sha magani ba?" Dai dai lokacin Mahmoud ya iso suka gaisa da Hajiya da ta fito falo tana masa iso. "Shiga! yau zuwa ya yi ya mini sake sake a gado da sunan ciwon kai". Mahmoud na dariya ya mike yana cewa " Hajiya ai gara ya kwanta ya more da zarar kunga mun yi aure shikenan sai ku dora mana dukkan girma alhalin matu'kar kuna raye mu yara ne 'kananu". Ya shige cikin dakin. Kallon Aminin nasa ya yi ya tabbatar yana cikin tashin hankali babba. Yasan karfin zuciyar Mk duk abin da ya bayyana a jikinsa tabbas ya yi tsamari ne. Da gaggawa ya shiga ya zauna a gefen gadon, ya na fadin "me ya ke faruwa ne?" Cikin rawar murya Mk ya dinga yunkurin magana amma ya kasa yi, ga mamakin Mahmoud sai ganin kwalla na gangarowa ta gefen idon Mk. Take hankalin Mahmoud ya yi tashin gauron zabi, murya kasa kasa cike da tsantsar aminci da kulawa, ya ru'ko hannuwansa ya ce "Yi hakuri Mukhtar! Fada mini damuwarka in sha Allah I will stand for you". Da rawar murya Mk ya dinga ambaton Sa'adah, Sa'adah". A hanzarce Mahmoud ya ce" me ya same ta, me ta yi?" Da 'kyar ya bude baki ya ce "mun rabu, na saketa Mahmoud"! ya karasa da murya mai cike da tashin hankali. Wani irin zabura Mahmoud ya yi ya mike yana cewa"How comes, akan me? subhanllah!" Shiru ya ratsa dakin! kowa tunani, na katantanwa da shi. A kasan makoshi Mk ya ce " ka fa'dawa Hajiya, tashin hankali na yadda zan fa'da mata, da yadda za ta karbi lamarin". Mahmoud ya zuba masa ido, yana kallon irin yadda Aminin nasa ke zu'ko numfashi da 'kyar tamkar mai fama da cutar asma. A hankali ya koma ya zauna yana jin tashin hankali shima na ziyaryartar sa. Tausayin Mk ya ratsa shi ya sake ru'ko hannuwansa a karo na biyu ya sassauta murya ya ce," Ina fatan sakin sunna ka yi, ina fatan mu gyara wannan matsalar kafin su Hajiya su ji, yanzu ina ita Sa'adah ta ke?" Cike da rashin kuzari ainun ya ce "Na kaita gidansu, saki daya na yi mata, abin da nake so ka fahimta, da abin zai gyaru da ko kai ba zan raba 'bacin ran da kai ba". A hankali Mahmoud ya muskuta ya ce "Kar ka yi haka, ka yi hakuri mana, da wanne irin ido za ka kalli dattijon arziki irin Baffah?" Wannan karon Mk ne ya tamke hannun Mahmoud ya zarce da cewa "shine babban tashin hankali na, fiye ma da yadda nake jin fargabar da Hajiya za ta shiga, amma kuma bana jin zan iya cigaba da zaman mu tare, iya adadin zaman da 'kaddara ta hukunta za mu yi kenan, ka fa'dawa Hajiya sai muje ka raka ni wurin Baffah, duk da bana jin dadin jikina". Ya fada a sanyaye cike da yankewar Buri. "Mukhtar Nima ba zan iya fa'da mata ba, da wanne baki zan fadi wannan 'bakin labarin?" "Cike da rauni ya ce " daurewa za ka yi Mahmoud". Shiru ta ratsa dakin a karo na biyu, nazari soasai Mahmoud ya ke, yana tunanin wacce irin 'kaddara ce mai zafi ta raba Mk da Matar da ya shaida yafi sonta akan kansa? Yana son jin menene ummul aba'isin wannan matsalar, amma kuma tunda Mk bai bu'da masa ba, shikuma ya yi al'kawarin ba zai tambayi komai ba, zai kuma yi dukkan mai yiyuwa dan ya sulhunta tsakanin su. A dabarance Mahmoud ya 'daga murya ya ce "Sam bazan iya fadawa Hajiya wannan tashin hankalin ba, kai da ka yi, kaine mai fa'da ba Ni ba". Ai kuwa wannan kalamin na Mahmoud ya janyo hankali Hajiya, da azama ta fa'da 'dakin tana fadin " menene ba za ka iya fada mini ba Mahmoud! wanne tashin hankalin ya rakito?" Dukkansu suka yi shiru aka rasa mai bakin magana, ta zauna da'bas a 'kasa tana salati, da fatan ba wani rashin gaskiya Mk ya aikata ba. Ganin irin damuwar da ta shiga yasa Mahmoud yin 'kundunbalar fadin "Hajiya ki yafe mu, ina ba'kin cikin sanar da ke yau Allah ya 'karar da zamansa da Sa'adatu". Salati mai 'karfi Hajiya ta rafka, tana cewa "Kar ka jinginawa Allah'karar zamansu, jingina masa, dama ya da'de yana fatan rabuwar, ganin ya kasa samun damar shine yanzu ya murde zaman da 'karfin tsiya." "Oh ni Rabi'atu ina ganin tasku, da wanne 'bakin ciki zan ji? da wadda yan'uwanka suke guma mini, ko da naka? Alhaji da Hajiya Babba sun mutu sun barni da ku, kuna neman kashe ni da ba'kin ciki". Ta fara hawaye, tana gogewa da hannun zaninta . Da ga Mk har Mahmoud sun yi laushi tubus da jin kukan Hajiya, hankalin su kuma ya sake tashi matu'ka, da rawar murya Mk ya ce "Na roke ki, ki daina zubar da hawayen nan dafi ne a rayuwa ta, da kinsan azabar da nake 'dan'dana na tabbatar da sai kin sassauta mini, ki yi hakuri Hajiya ba yadda zan yi ne, abin ne ya fi karfina, ki mana addua ki kuma yafe mini". "Yanzu ina Sa'a din ta ke?" Mahmoud ya ce "tana gidansu, yanzu ma komawa zamu yi dan bamu sami Baffan ba". Hajiya ta sake sa salati tana tafa hannu, tare da cewa "yanzu idon ku, idon tsohon nan ku iya fa'da masa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157