Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 37

Chapter 37

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yasa harshenta ya yi mata nauyi ainun ba? Tsawon mintuna yana dakon ta magantu amma shiru. "Ina ta magana kin yi mini shiru kuma kin san ba na son ina magana kina ji amma ki yi kunnen uwar shegu." Ta sake yin kasa da kai, da kyar kuma a hankali ta ce, "Ni to me zan ce?" Bai ji dadin yadda ta ce ba amma sai ya ce, "kinsan me za ki fada mini da zai nuna kin aminta da Ni ko akasin hakan". Ta kasa fadar ko daya, ya gaji da sauraronta ya ce "Shirunki yana nufin na yi hakuri, na sha kaye a hanun abokan takara". Yana gani ta bude wayar dake hannunta wacce ta Inna ce ta fito da ita. Ba zato ya ji wayarsa ta yi kara kadan, alamun shigowar sako (message) bai duba ba ga zaton sa MTN ne. Ganin ta share ta hau daddana waya sai ya sake jin rashin dadi sosai, a tunzure ya ce, "Silent again?" A kunyace ta ce, "Ka duba wayarka!" Bai yi musu ba ya dauko wayar sa ya shiga ma'adanar sakwanni (inbox) ya ga text din da ya shigo ita ta turo shi. Da sauri ya bude, harrufa uku kawai ya gani. "*YES*" Kawai ta rubuta wani irin dadi ya mamaye zuciyarsa da sauri ya ce, "Kin amince mini na turo Sa'adah da gaske?" Kai kawai ta daga masa don ta sake ba shi tabbaci. "Alhamdulillah!" Yake ta fadi tare da cewa "Na gode!" Ya bude murya sosai ya kira ta, bai jira amsawarta ba ya zarce da cewa, "Idan fa kin zabe ni har na turo aka nema mini aurenki, hakan na nufin kin rabu da Honorable, da wannan tabbataccen yaron! Da ma kowa da kowa, sai ni kawai. Kin ga saboda na san kina da damar ki zabi wanda ya miki shi yasa nake danne kishina, amma tsakani da Allah idan har maganar aure ta kullu tsakanin manya dole ki rabu da kowa kin amince?" Ba wani dogon Turanci ta ce, "E!" Farincikinsa ya karu ya hau fadin, "In Sha Allah ba za ki yi nadamar zabe na a matsayin mijin aurenki ba." Shauki ya debe su ba su ankara ba har aka fara kiran sallah sannan ya tafi yana cewa, "Duk yadda muka yi da Baffa za ki ji." Alkalamin *SURAYYA DAHIRU* ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *TALLAH*! _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ 41-42 A Daren ranar Baffa ya sake zaunar da Sa'adah tare da mahaifiyarta, ya ce "Ina sane na bar ki kina sauraran wasu bayan Mutari. Saboda na ba ki damar da shari'a ta ba ki, na kar na aurar da ke bisa dole, duk da shari'ar tace ni na fi cancanta na zaba miki mijin aure kasancewar ki budurwa. Amma tunda muna wani irin zamani da 'ya'ya suke ganin sun fi iyayensu sanin abin da ya dace da su, ya sa na ba ki damarki, na sha fada miki aure zan miki, ba kuma zan miki auran dole ba, sai dai na dora ki akan shawara mai kyau. Alhamdulillah lokaci ya yi, don haka ki fada mini a cikin masu zuwa wajenki wa kika zaba? Ina son ya turo mini magabatansa a tsayar da magana guda daya." Ta yi shiru kanta na kasa, Inna ce ta tanka , "Ai na ga alamar sun daidaita da Muutar din." Hannu Baffa ya daga mata alamun ta yi shiru, ya bude murya ya ce, "Iyah tsakanin Alhaji Mamman da Mutari wa kike so?" Ta sake yin shiru, ya nisa ya ce, "Dole fa ki yi mini magana saboda duk hukuncin da zan yanke, ya kasance da yardar ki, ba na so daga baya ki ba ni matsala, kwanakin baya da Alhaji Mamman ya same ni ban ba shi amanna ba, amma na ce ya nemi yardar ki, saboda shi ma mutumin kirki ne, ya samu yabo a wurin mutanen da suke kewaye da shi. Yanzu kuma lokaci ya yi da zan sallami daya a cikinsu." Inna da ta ke sauraran su ta ji tamkar ta ce Alh Mamman zai sallama amma ta yi shiru saboda bai ba ta damar yin magana ba. Ya sake kiran ta a karo na biyu, "Iyah!" Ta amsa murya a dakushe. "Wa zan sallama a tsakaninsu? Ko kuma dukkansu ba ku shirya ba?" Ta jima kafin ta bude baki ta ce, "Dazu Inna ta fada ai." Da'di ya kama dukkansu, ya ce, "Kina nufi da Mutari ku ka shirya?" Kai ta sake yin kasa da shi ba tare da ta amsa ba, Inna ce ta yi fit ta ce "Ka san ba za ta iya amsawa ba, amma na lura da Muutar ne za'binta." "ALHAMDULILLAH!" Baffa ya furta a fili. Ya zarce da fadin, "Shike nan da kaina zan ba wa Alhaji Mamman hakuri, Allah Ya sanya alkhairi a tsakaninku, ki yi ko yi da uwarki wurin biyayya, Allah Ya tabbatar da alherin da muke zaton sa tsakaninki da yaron nan." Da haka ya sallame ta wanda da kyar ta iya tashi. Washegari kuwa bayan La'asar MK ya samu Baffa, zatonsa ya tabbata domin kuwa maganar turo magabatansa ya yi bayan ya tabbatar masa ya yi magana da Sa'adah ta ce shi ne zabinta. Godiya sosai MK ya yi tare da cewa, "Za su zo ba da jimawa ba." Baffa ya nisa ya ce, "Ka yi shirinka a hankali sannan zan fada maka ni ba a kawo mini lefe sannan ni ma bana yin kayan daki, don haka ka shirya dakin da za ka ajiye ta da iya abin da za ka iya, ni ma zan hado ta da yan tarkacen da zan iya. Daurin aure kawai za a yi sai kuma uwarta za ta dan yi taron mata a gida, zuwa yammaci da kaina zan kai ta dakinta, Ban yarda da wani taron maza da mata da sunan fati ko wani abu na daban ba! Idan kun tare kuna da ra'ayi,

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});