Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 68

Chapter 68

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,195 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

fadin "kice cin fuska ya miki? banga laifin ki ba, dole ki guji magani, ko nice haka zan yi". Shi dai Mk ya zama tamkar gunki, yana kallon shari'ar son rai a wurin Hajiya. Ba zato Hajiya ta ce yaje ya siyo wasu maganin. Ya ce " Bafa su bane, tunda take wannan bala'in na zubar da su, na siyo masa wasu, amma ta "ki bashi" Da rawar murya ta ce "Billahillazi, baka canjo wasu ba, duk abin da ya fito ta hannunta, na tsane shi, zan kuma gane". Jin haka yasa Hajiya fadin "Bar Wannan gadddamar je ka siyo wasu a bashi ya dan sami sauki" Bai q musa ba, ya mike, ya dauki ledar maganin, ya fita. Sai da ya fita Hajiya ta dinga mata nasiha, tare da cewa "ki rage nuna masa kishinki a fili, sai ya samu dalilin da zai dinga musguna miki". Ta kalleta tace "tunda da wuta jona ruwan zafi kuyi wanka". Ta mike ta cika buta ta jona, mintina kalilan ta kashe kanta, ta juye, ta sake maida wani, kafin ta fito, Hajiya ta wanki Jawad a bandakin tsakar gida. Ta dama musu kunu, ta juye a flask din shayi, ta zubawa Jawad a kofi, ta bashi, ya shanye tas har da kari, ta tabbatar shima har da yunwa ta sake gigita shi. Sa'adah ta fito sanye da riga da zani na atamfa, dinkin ya zauna sosai, mussaman da bata cika daura zani ba. Ta mikawa Hajiya kayansa, sai da ya koshi ta koge masa baki sannan ta saka masa kaya, dai dai lokacin kuma, Mk ya dawo dauke da magungunan, leda biyu, ya mikawa Hajiya, sai da Sa'adah taga na wurin Farida, ga kuma wadda ya sake siyowa, sannan ta saki ranta, a ransa fadi yake masifaffiya kawai. Take Hajiya ta bude ta bashi, ta shafa masa na shafawa, barci ya dauke shi mai nauyi. Sosai Hajiya ta musu fada, kuma duk na Mk yafi yawa, jan kunne 'daya, ta yiwa Sa'adah, kar ta sake saka Jawad a cikin fa'dansu, ta ki cin abinci, shi akan mai zata hana shi? Ta cika kofi, da kunu ta mika wa Sa'adah tace "Shanye ki bani kofin". Ta karba, ta fara sha, ya mata dadi sai kamshin kayan yaji yake yi. Shi dai Mk yana kallon ikon Allah, anbawa Jawad, da Sa'a, shi ko oho. Sai da Sa'adah ta shanye sannan Hajiya ta mike ta ce "zan tafi nasan ki da jin magana, na kashe wannan magana kar a kuma tada ta" Da sauri ta amsa da "in sha Allah ta wuce". "Na gode Miki Sa'a, Allah ya miki albarka". Sa'adah ta amsa da "Ameen Allah ya kara girma" ta tashi tana mata rakiya hanyar waje. Tare suka fita da Mk zai kaita, a hanya tana sake masa fa'dan, lallai ya kiyayi zungurar Sa'a, ta dora da cewa "Kana ganin irin yadda take mutunta ni, tana haba haba da yan'uwanka, iyayenta mutanan kirki, lallai ba zamu shirya da kai ba, idan kace zaka wulakanta ta, mussaman ma akan wacce bata zo hannun ka ba". Har ya kaita gida, kashedi take masa iri iri. Da za ta sauka ya ce "kin basu kunu, amma Ni baki bani ba". "Ina sane, kai Sa'a ce mai ba ka". Murmushi ya yi, tare da cewa "Hajiya kar kisa na fara kishin yarinyar nan, naga tana neman zarta ni a gunki". Ta yi murmushi tace " maza ka juya ka sake rarrashin ta, ka tsaya a hanya ka siya musu dan wani abin, kunu kadai bazai ri'ke ta ba, ta tara yunwa". Haka kuwa, ya biyo ta titin Hausawa bawo road ya siyi wainar shinkafa da ake yi mai dadin gaske, a falo ya tarar da ita, tana zaune tana kallo. Bata dago ta kalle shi ba, ta amsa sallamar sa, daga haka bata kara magana ba. Ya tsaya ya ce "Ba ki mini sannu da zuwa ba fa". Ba tare da ta kalleshi ba, ta ce "inace ka ce kowa ya yi harkarsa?" "Na fa'da! amma dai Hajiya ta kashe maganar, ta ce kar a kuma tada ta". "Ita maganar maganin Jawad ta kashe". Ya zauna, yana cewa "ga waina na siyo miki, tashi ki zubo mana". Kanta a kasa ta ce" ci abinka". Ya kai kicin ya adana, ya zubo wadda zai iya cinyewa, tare da kunu a kofi, yaso ya shiga dakinsa, sai kuma yafi zumudin zama kusa da ita. Ya zauna yana fadin "dan Allah sauko ki taya ni ci". "Ba zan sake cin abinci da kai ba, tunda muka yi aure, baka taba kaini restaurant munci abinci ba, amma ka dauki wacce kake so kun je! ba ruwana da sabgarka". Ta fa'da hawaye na balle mata, ya yi shiru, yana jin sabon tashin hankali, ya rasa da bakin da zai kare kansa. Ya yi shiru, ya kasa cin abinci, ko kaffara ba zai yi ba, su Safina ne suka kawo mata wannan labarin. "Ki yi hakuri kin ji Sa'adan Uncle". Kamar ya watsa mata garwashi, ta zunkudo ta ce " ta Ina ka zama kawuna?" Kai ba 'kanin Baffa bane, bare na Inna, daga jiya ba zaka sake jin bakina ya kiraka da Uncle ba, ita dai da kuka hada dangi, sai tayi ta fa'da na bar mata" "Ashe lokacin da kace min dole kayi kishin mace, idan ka ganta a gaban motar wani da ba Muharraminta ba, 'karya ka fada tsagwaronta? To ita mai kuka hada daka dauketa a gaban motarka?" Kansa ya kulle, ya kalleta ya ce "Na yarda ban kyauta ba, ki yi hakuri, ki bani wata damar, ko banci albarkacin komai a gunki ba, naci albarka cin mahaifiyata da tazo ta baki ha'kuri, ta kashe maganar". Jikinta ya yi sanyi, ta ce shikenan na ha'kura". Da'di ya kama shi, ya matsar da kwanon abincin kusa da ita, ya ce to sauko muci". Ta girgiza kai, "Na hakura, amma ba zanci da kai ba". Ya tura mata, "to ci wannan, bari na zubo wani," ya mike ya fita da sauri. Cikin sa'a ranar bashi da lakca sai 'karfe daya, dan haka, bai fita ko ina ba, yan tare da ita, yana ta kokarin wanke mata zuciya, shi da kansa ya tabbatar a duniya ba abin da yake so sama da Sa'adah da 'danta, idan aka cire Hajiya. Sai dai duk nacinsa bata yarda da shi ba, kan dole ya 'kyale ta. Kwana biyu tana mai yawo da hankali, kafin ta ha'kura ta sallama masa kanta, cikin rawar jiki yake komai, yana ayyana distance fa yana da amfani, domin ji yayi ta dawo masa sabuwa. Yana samun kudi kuwa, ya dauke su ita da Jawad suka je restaurant din Royal Tropicana suka ci abinci, suka yi hotuna, irin wadda ake wankewa a take, take & wash, suka zarce country mall, ta zabi abin da take so. A hanya ya ce "shikenan yanzu na dawo Uncle?" "Hmm! magana ta wuce ka daina dawo mini da ita". Ya shagwabe fuska ya ce " idan har da gaske ta wuce, then called me Uncle". Ta fara dariya, tana cewa "ashe son girma ne da kai ban fahimta ba?" Shima ya taya ta dariyar sannan yace "tsakanin ki da Allah! Idan nace Miki Sa'adatu ba kya jin

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});