Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 118

Chapter 118

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

service). Ido biyu suka yi da Khali cikin jerin mutanan da suke zaune suna dakon yadda shari'ar zata kaya. Rabon da ta su yi ido da ido idan har lissafinta dai dai ne, shekaru kusan goma sha hudu, tun ranar da suka je partin kammala sakandire a Hang out, ta tuno jidalin da Mk ya yi mata a lokacin. sai dai ta ganshi a hoto, sosai ya girma ya zama zabgegen saurayi na kece raini. Wani irin abu ya dinga ta so musu dukkansu. Da sauri Sa'a ta wuce gaba inda tawagar lauyoyi suke zaune. Shi kuma ya bita da kallo yana fata iri iri akanta ya kasa daurewa a fili ya ce "Ba zai zama illah dan na auri age mate dina ba, domin har yau din nan da yake da yanmata daban daban yana jin son Gogel din sa, yana tuno moment dinsu kafin kutsen Mk Bichi cikin soyayyar su mai cike da kuruciya da Sanya nisha'di. Sosai ta yi masa kyau, tafi Halima da ta ke budurwa komai da komai, domin ko a jiya sun hadu tunda basu da nisa . Hula da rigar lauyoyin nan ba karamin kyau da kwarjini suka kara mata ba, ga wani siririn farin glass a Idonta , kamshin ta na turaran Escada sentiment da ya santa da shi tun cikin kuruciya wadda a lokacin na Sumayya take daukowa bata san ma mai daraja bane, yauma kamshin ya shaka, tabbacin har yau da shi take tu'amalli. A yanzu mahaifin Khalil Sanata ne mai ci, Dan haka yan adawa suka dinga rubuce rubuce akansa har sai da suka ja hankalin hukimar E.F.C.C ta damke shi, wata biyu ana ta dauki ba da'di tunda shi ya kafe ya'ki daukar lauya, ya kuma hana a daukar masa, da yake yana da kyakkawan alaka da gwamnatin jahar Kano sai ta bashi lauyoyi har guda biyar dan su tsaya masa, tunda mai girma gwamna da kansa ya gamsu Hon Ibrahim Hassan bai ci wannan kudaden da ake ambatonsu ba. Manyan kwarrarun lauyoyi har guda uku masu mukamin (S.A.N.) sai guda biyu 'kananu amma hazi'kai, Bar Sa'adatu Bashir Gogel da Bar Mustafa Isa Gwaram. Kotu ta 'dage sauraren shari'ar Alh Ibrahim Hassan zuwa 28/6 a shekarar da muke ciki, wattanni biyu masu zuwa. Duk da adalilin Khalil ta rasa aurenta ta kudiri aniyar tsayawa mahaifinsa da dukkan iyawarta ko dan ta nunawa Khalil martanin kaunar da ya da'de yana yi mata da tarin hidimar da ya mata a rayuwa, ta tuno sadda suke FGC Kano ku'din break din Khalil akanta yake karewa, ta sake tuno sadda zai kwaso abaya da lace tsadaddu da mahaifiyarsa take siyarwa ya kawo mata. Har gate ta bisu ta gaisa da iyayensa tana jaddada musu su kwantar da hankalin su zasu yi aiki tukuru har komai ya zama tarihi. Suka yi musayen lamba da Khalil. A gajiye ta isa gidan Sumayya, amma haka ta yi wanka ta Fara shirin tarbar Anwar da zai kawo mata ziyara. Anwar bashi da mace amma ba saurayi bane, ya yi aure wata sha'daya da auren matar ta zo haihuwa ta rasu ta bar yaro yana hannun kakarsa wadda ta haifi marigayiya. Shekaru hudu kenan, tun akanta kuma bai sake kula kowacce mace ba, sai SA'ADAH da yake sonta sosai, duk da dai har yanzu bai samu cikakken hadin kai daga gareta ba, amma dai yana ganin cigaba. Anwar Ma'aikacine a ma'aikatar zabe(INEC). *Bayan wata Daya* Zuwa wannan lokacin Mk ya kasa gane manufar Sa'adah domin tun ranar da Baffah ya sa ya kaita gidan, Sumayya bai sake ganinta ba, a rana yana kiran layinta kamar sau biyar amma bata 'dagawa wani lokacin ma zai kira ya ji tana waya, amma da za'a jima ya sake kiran sai dai ta gama ringing ta katse, tun baya jin damuwa sosai har ya fara ji har cikin ransa. Ranar Talata yana zaune a bakin shagonsa kawai ya hango wata dalleliyar mota ba zato yaga Iyah ta fito sanye cikin shigar lauyoyi, kyau iya kyau ta yi daga nesa ya hangota amma ba karamin kwarjini ta yi masa ba. Bai gama hasashen da wa suke tafe ba, kawai sai ya ganin wani matashin namiji y fito cikin fararen kaya kal, ba shi da gajarta amma sa Mk zai jera da shi sai aga gajartar tasa tunda Mk dogone mai cikakken jiki. Ganin da ya yi matashin yana nuku nukun shiga gidan sai ya gane bazawarinta ne, domin sai da ta Fara shigewa sannan ya bita a baya, Mk bai san ya akayi ba sai ganin sa ya yi, ya tsallako titi yana leka gidan su Iyah, Bai gansu a zaure ba, kenan ciki suka shiga wani irin azabben kishi ya mamaye masa kalbinsa, ya matsa ya zauna a shagon faci na jikin gidansu, jikinsa ya dinga shaking wato har fa'da masa ta yi tana son namiji cikin fararen kaya? Shiyasa ya mata kwalliya da su. Duk addu'ar da ta zo bakinsa sai ya yi amma baya iya yinta cikakkiya, Karin tashin hankalinsa da Baffa ba ya nan yana Gogel, tunda daminace, shiyasa garin yake da dan sanyi, amma Mk sai zufa yake yi. Mintina goma ya ji fitowarsu ya yi maza ya juya gefe daya, yana kallon kyakkawan matashin da ba zai nuna masa komai ba sai tsayi da shekaru, a kiyasin Mk zai iya bawa Anwar shekaru talatin da bakwai, shikuwa shekaransu arbain har da biyu kawai dan yana yawan motsa jiki ne ake ganinsa tamkar Yana cikin early 30th ne. Ba bata lokaci Anwar ya ja motarsa ya tafi, Mk ya na zaune yana jin tamkar ya bi wannan matashi ya masa dukan kawo wuka, Sai ya ga wani saurayi da ba zai wuce sa'an Ahamad ba, ya zo akan mashin. Ya kafe mashin din ya fito da wayarsa Jim kadan ya Kara a kunne, ya ce "na iso". Ba jimawa ya ga Sa'adah ta fito cikin dogon hijab har kasa, ta karbi ledar ta mi'ka masa kudi, kafin ta juyo Mk ya yi wuf ya mi'ke ya isa kofar zauren nasu, tana juyawa ta ganshi, zuciyarta ta buga ta rasa gane wanne irin abu ne duk sadda zata ganshi sai ta ji wannan bugun zuciyar. Kai tsaye zata shige ba tare da ta nuna ta ganshi ba, ya jah Hijabinta tare da cewa " kina nufin Baki ganni bane?" Ranta ya baci sosai ta fincike, cikin gatsali ta ce " Mukhtar bana son wula'kanci ko da nake bin maza nake Ballagazaci, ai ba cikin gidan da ubana ya samar da ni nake yinsa ba, kar kuma ta'ba ni, iskancin da nake yi ba da irin ka bane, da yara ne sa'anina wato matasa irin Ahamad dinka". Ya kai mata wani irin bahagon mari, ta yi maza ta goce ta bar shi da marin iska, a kufule ta daga ido ta zuba masa nata, ta tsorata da yaddda ta ga idonsa ya yi jawur, zuciyarta ta sake bugawa Amma duk da hakan sai da ta yi jarumtar cewa "A da ne ka dake ni ka kwana kalau Mukhtar amma a yau ina rantse maka da Allah da ka mare ni da ka ga 'kwanjina domin kuwa sai na gurfanar da kai gaban Human Right". Ya juya tamkar tafiya zai

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});