Chapter 61
Chapter 61
irin ha'kuri da rarrashi da bai yi mata ba, yasa ya zuba mata ido, shi yake yin komai na gidan har girki, ya ki yarda ya biye mata, ya tabbatar tana cikin halin da za a tausaya mata, duk da abin nata har da rashin mutunci, amma da zarar ya tuna abubuwanta na alheri sai ya mata uziri, babban abin da ya dame shi, rashin shayar da Jawad musamman da yake ana ba shi supplement na yara mai sa su kuzari da saurin girma, akai-akai yake jin yunwa, don ma yana shan madara da fricso cream. Washegari da yamma ya dawo da ga wurin aiki tun daga waje yake jin kukan Jawad, a sukwane ya shigo cikin gidan, ya tarar da ita, tana zaune a falo tana ganin sa, amma ba ta dauke shi ba. Bai taba jin haushin ta irin na yau ba, ya jima yana tsaye ya zuba mata ido, yana kallon ta, yana jin tamkar ya rufe ta da duka. Kwafa ya yi, ya dauki yaron ya hada masa abincinsa, ya ba shi ruwa sannan ya kwantar da shi, yana ta shure-shuren 'kafa, tamkar ba shi ne mai kukan nan ba, da ma shi ba mai fitina ba ne, indai ka ji kukansa to dayan biyu ne, ko yunwa ko rashin lafiya, tunda ya yi kuka kafin su yi arbain shike nan ya daina kukan banza. Wanka ya yi, ya fito ya zauna a falo, ya dube ta ya ce "Na gaji fa da abubuwan da kike mini, na yi iya hakurin da zan iya, na ga abin naki babu mutunci ko kadan". Kai tsaye ta ce "Da ma ai so nake ka gajin, matu'kar kana son zaman lafiya, sai dai ka zabi daya cikin biyu, ko dai a yaye Jawad gaba'daya, ko a cire cikin nan". Ransa ya yi matu'kar baci ya kalle ta ya ce "Ni ban san inda ake cire ciki ba, ke da kika sani sai ki je, ai don kin ga na damu da ke shivyasa kike mini wannan iyashegen, mafi yawa idan mace ta samu ciki da wuri irin haka, daga wurin mijin take fuskantar kalubale, amma ke don samun guri ni kike yiwa wulakanci". Ya nisa sannan ya ce "Ba zan kai kararki ba, amma daga yau ba zan sake rarrashin ki akan wannan matsalar ba, idan kin ga dama ki bar cikin nan, idan kin ga hagu ki zubar a rariya, Jawad kuma In sha Allah yau an yaye shi, Ubangiji zai raya mini shi, ina ce idan mutuwa kika yi ma ba zai fasa rayuwa ba?" Daga haka bai kara cewa komai ba, ya tashi ya shiga kicin ya hada cornflakes ya shige dakinsa, bai dawo falon ba, yana kudire ba zai sake dafa abinci ba. Bai wani jima ba ya shigo, ya tashi Jawad ya canja masa riga, ya samo leda mai kyau ya zuba tarkacen da Jawad zai bu'kata, ya nade shi a shawul, ya saba shi a kafada ya fice, ba tare da ya kalli gefen da takep a zaune ba, bare ya yi mata sallama. Kawai sai ta ji kuka ya zo mata, bakin cikinta daya yadda bai dafa musu abinci ba, kuma yunwa take ji, ta kalli agogo biyar da kwata 5:15pm, kan dole ta shiga kicin din ta hada tea ta dauko biscuit din super2 ta hau ci. Gidan Samira da yake Dan'agundi ya tsaya ya ba wa yaro ya kai mata Jawad, sai da ya kira ta a waya ya tabbatar ta karbe shi, sannan ya tari Adaidaita ya wuce shagon askinsa, yana tafe yana tunani biyu, na yadda zai bullo wa Sa'adah, da na sayan motar da yake shirin yi. Tana zaune har taran dare ba MK ba Jawad, hankalinta ya tashi, ga wata muguwar yunwa na addabar ta, ta rasa inda za ta tsoma ranta ta ji dadi, kewar Jawad ta addabe ta. Sai goma saura ya dawo, a dakinsa ya ci burki, ya kwantar da Jawad da yake ta barci, tunda Samira ta masa wanka ya yi barci. Sai da ya gama komai tunda ga wanka, har shafa'i da wutiri, ya nufi gurin Sa'adah, tana zaune a falo ta rasa me yake damunta. Sallama ya yi bai jira amsawarta ba, ya shige daya dakin inda nan kayan Jawad suke, akwati babba ya dauko, ya hau zuba sabbin rigunansa da ba a kai ga bude su ba, sannan ya zuba na cikin drower kayansa, hatta bargonsa sai da ya saka cikin akwatin, da kyar ya zuge sannan, ya kashe fitilar, ya ja akwatin zuwa dakinsa, da ido ta bi shi, tana sake jin tashin hankali na kamata. Dakin ta shiga, ta hau dubawa, ta tarar ba kayan Jawad sai tsirarru wadda suka fara yi masa kadan, sai dryar shanya. Kuka ya kwace mata, tana raya duk bala'i, ba inda za'a kai mata yaronta. Tana fitowa shi kuma ya shigo, ya zauna a kujera ya ce "Zo ki zauna, magana za mu yi." Ba ta ki ba, ta zauna din, yana kallon yadda ta lalace tsabar fitinar da sanya a ranta. "Gobe zan yi Asubanci zuwa Lagos, jirgin karfe shida zan shiga, kafin sallar Asuba Mahmoud zai zo ya kai ni Airport, zan kai Jawad wurin Anty Hafsa." Kafin ya karasa ta fashe da kuka tamkar yarinya karama tana cewa " Billahillazi ban yarda ba, jaririn yaron za ka kai har Lagos?" Dariya ta so subuce masa, ya cije yavce, "Ba yardaki na nema ba, fada miki na yi, saboda kina da hakkin ki sani". "Idan na yarda Allah ya tsine mini, ai da ma na san yanzu ba ni da wani muhimmanci a gurinka". Ficewa ya yi ya bar ta, ba tare da ya ba ta amsa ba, yana jin farinciki, da dukkan alamu shawarar Mahmoud za ta yi tasiri. Kwanciya ya yi, bayan ya kashe fitila, addu'a ya fara yi, kawai ya ji ta shigo masa ba sallama. Tasa hannu ta kunna fitilar dakin, suka kalli juna, na tsawon sakwanni, wani abu na taso musu a zuciya. Shi ya fara dauke idanuwansa, murya ba amo ya ce, "Kin san dai ba na iya barci da haske a kaina ko? Yanzu kuma na gama fada miki Asubanci zan yi, don Allah ki bar ni na yi barci". "Ka tashi mu yi magana". "Ki adana maganar ki, idan Allah yasa na dawo lafiya, gobe irin wannan lokacin sai mu yi maganar". "Wallahi yanzu za a yi ta". Ta fada cikin rawar murya hadi da kuka. Ta zauna kusa da kafafuwansa, tana cewa " tsanar da ka mini har ta kai ka kaurace mini, sannan ka raba ni da yarona?". "Ni ban kaurace miki ba, ba kuma zan raba ki da danki ba, kin taba jin inda aka raba uwa da danta? ko'ina na kai shi, ina tabbatar miki wataran da kansa zai neme ki. Ke kika ce idan ina son zaman lafiya sai dai a yaye shi, zaman lafiyar nake so". "Wallahi ba zaman lafiya kake so ba Uncle, kawai so kake ka sake jefa ni cikin wani tashin hankalin, ai ba a nan kake kwana ba, sannan mene ne na kai wannan dan kilifin halittar har Lagos?" "Kin ga Sa'adatu ni kwana a nan dakin ba ina nufin wani
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157