Chapter 87
Chapter 87
ta, ya gigita ta sosai. Tausayinta ya cika zuciyar dattijon, ya kalli Mk ya ga shima a gigicen yake kwarai da gaske. Duk da hakan sai yace "zo kusa da ni 'dana, Mk bai 'ki ba, hakan nan ya matsa kusa da shi ya tsugunna, a tausashe yace "ka yi hakuri ka ji! da gaske Allah na tare da masu ha'kuri, ba a biye sha'anin mata, yanzun nan za su rufe ido su yi abin da za su shekara suna nadama". Mk dai baice masa komai ba, bai ji kuma zai janye sakin nan ba, tabbas sai ta je ta banbance tsakanin zaman gidan miji da rayuwar da take hari wannene 'yanci? A hankali tsohon ya kuma fa'din "na tabbatar ko iya haka ka barta ta gane bakin Rijiya ba wurin wasan makaho bane". Murya ba sauti Mk ya ce "Baba kar ka sa na yi abin da zan zalunci kaina, ina ro'kon ka, ka yi ha'kuri, al'kawari 'daya zan maka, matu'kar zuciyata ta huce da lamarin yarinyar nan, to kana cikin wadda zata ci darajar su na yafe mata, amma a yanzu idan ka tirsasani na mayar da ita, auren namu zai iya lalacewa gaba'daya, ka yi ha'kuri ka fahimce Ni". Kafin Dattijon ya yi magana Sa'adah ta zabura ta sake kwasa a guje ta shige gidan. Tausayinta ya cika zuciyar wannan tsohon, ya riko Mk sosai ya ce " Na fahimce ka 'dana, ba kuma zan maka dole ba, mai 'daki shi yasan inda yake masa yoyo! Amma ina son ka ri'ke a ranka cewar yarinyar nan tana sonka sannan uwar ya'yan ka ce, dan haka kar ka yi amfani da zato wurin hukunta ta, ka boye laifin ta, Allah ya muku albarka gaba'daya, ya kuma huci zuciyarka". Da ga haka ya saki Mk ya juya, ya tafi, ga mamakin Mk sai ya ga cikin sakwanni mutumin nan har ya yi tafiyar da ya bacewa ganin sa, ya dinga wasiwasi anya kuwa wannan mutum ne? a tsufansa ba zai iya irin wannan sauri haka tamkar walkiya ba, ya shiga gida yana ayyana ko dai aljanine cikin aljanun Sa'adah.😂 A bakin motar ya tarar da ita, tana tsaye hawaye ya ki tsaya mata. Ya bude gate din, sannan ya karasa ya bude motar suka shiga, sai da ya rufe gidan sannan suka tafi. Ta by pass hanyar 'Dorayi ya bi dan haka hanyar ba yawan motoci, sun zo daidai Wailari ya ga ta fara wata irin jijjiga tana cewa "Laifina bai kai wannan hukuncin ba, kar kasheni da raina, Baffa ba zai bar Ni na zauna masa a gida ba, ina ka ke son na tafi?" Sai kawai ya ga ta sume. Kan dole ya gangara gefen titi ya bude ruwan roba na Highland da ke gaban motar mai dan sanyi, daga gidan Mahmoud ya taho da shi, ya watsa mata, ajiyar zuciya ta saki tare da rushewa da kuka sosai har muryar ta fara dashewa, fadi take yi "Ka ji tausayina mu koma gidanmu, Jawad zai yi kukan rashi na, komai ka ce na yi bazan kuskure ba, na yarda ka 'Kara aure, ka sake 'karawa, ka sake 'karawa, ya fi mini sau'ki da na rasa ka". Idan ya ce jikinsa bai yi sanyi ba, ya yi 'karya, idan yace maganganun ta basu yi yunkurin karya masa zuciya ba ya yi munafunci. Ya zuba mata ido yana kallon yadda tashin hankalin awa daya rak ya susuta ta, yaci gaba da kallonta yana so ya samu dalili gamsasshe da zai mata afuwa, amma da zuciyarsa ta hararo masa cewa "Hai'ntarsa take yi shiyasa ta 'ki bari ya ga ta'addacin da ta ke yi da aurensa akanta, sai ya ji zuciyar sa tana zafi tamkar ana gasa burodi. Ya zuba mata ido ya ce"Sa'adatu kowanne bawa da irin kaddararsa, Allah ya sani na iya bakin kokarina na mu zauna lafiya, kuma shine shaida akan son da nake miki, matu'kar gaskiya zan fada miki, zuciyata ba za ta nutsu da ke a yanzu ba! Al'kawarin da zan miki daya ne, ba wadda zai ji mai ya ha'damu, Ina tabbatar miki zan dauki laifin a idon kowa, kema kuma kar ki fa'dawa kowa ko da Baffa ne kuwa". Ya yanko tissue yana goge'kwallar da ta cika masa idanuwa. Ta zama very speach less, bugun zuciyar ta ya karu, wani irin zazzabi mai zafi ya fara kokarin kai mata caffa. ta koma ta kwanta a jikin kujerar tana jin duk wani tashin hankalin duniya yau ita aka ha'dawa shi. Tsawon lokaci suna haka, shiru ya ratsa, sai fama suke da radadi a zukatan su. Cikin 'karfin hali ya tayar da motar ya hau titi, karon farko da Sa'adah ta yi fatan inama su yi hatsarin da zai zama ajalinta, ta huta da azabar ciwon da ke damun zuciyar ta. Bai tsaya ba, sai a kofar gidan su, gabanta ya yanke ya fadi, ta tuno maganganun Baffa a ranar da zai kaita dakin aurenta. Ta kalle shi ta ce "Baffa korata zai yi, kar ka barni anan, mu tafi gidanmu Malam, na yi al'kawarin ba zan sake ri'ke kowacce irin waya ba". Ta ru'ko hannunsa ta sake fa'din " Na amince ka yi amarya ka tafi da ita karatun da za ka tafi, Ni ka barni zan jiraka, fatana kar ka barni". Magana ta ke yi ba kuka, sai tsananin bacin rai da tashin hankali. Ya kalleta sosai "a karon farko da ya ganta cikin NADAMAR gaskiya, sai dai nadama marar amfani ta ke yi domin ta riga ta yi a 'kurarren lokaci. Baice komai ba, ya bude motar ya fita, haka ta bude itama ta fita sanin akan titi suke, a zaure ya tsaya ya ciro wayarsa ya 'Kira layin Baffah, ya sanar masa ya zo yana zaure. Cikin rashin sa'a ya ce "dazun nan na tafi Gogel, sai jibi kuwa zan dawo, ko akwai matsala ne?" Kai tsaye Mk ya ce "akwai Baffa Amma zan zo na sameka anan din" "Ba sai ka zo ba Mutari, in sha Allah zan juyo a yau ba sai gobe ba". Ya yi godiya, sannan suka kashe wayar. Sa'adah na rakube a jigin bango, ta matso ta tsugunna guiwa biyu ta ce " Rashin samun sa alamun ubangiji bai son rabuwarmu ne, Dan Nabiyur Rahamati ka dauke ni mu koma gida". Ya kalleta sosai ya furzar da iskar bacin rai ya ce "wa ya siya miki Wannan Agogon da kuma waya?" Hawaye ya balle mata, ta rasa mai za ta ce. Ganin ta yi shiru ya sa shi cewa tashi ki shiga gidan zan je shago na jira dawowarsa. Ya fita da sauri, ya yin da ita kuma ta durkushe a 'kasa tana kuka sosai. Ta jima tana kukan da 'kyar ta tashi ta shiga gidan ta tarar da mahaifiyarta tana zaune tana Jin radio. Tana layi ta 'karasa kan tabarma sabon kuka na kaico iri iri na sake ku'buce mata. Tambayar duniya ba wadda Inna bata mata ba amma ta 'ki tankawa, lamarin da ya dagula hankalin ta. Kan dole ta 'kira wayar Baffah ta sanar da shi ga Iyah ta zo tana ta kuka, kuma ta ce mijinta ne ya kawota da kansa. Ya amsa mata da gashi nan ya juyo. Ta ajiye wayar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157