Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 111

Chapter 111

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kuma wadda yake karba na gwamnatin kasar ingila. Bugu da kari ya na kasuwanci sosai, ya sake fadada shagunan askinsa, ya bude na shagon saida kayan maza masu daraja da kyau. Dan haka ya kammala katafaren gidansa da yake ginawa akan hanyar zuwa sabuwar Jami'ar Bayero, fenti kawai ya rage da Yan kananun abubuwa da sai a shiga gidan za'a fi bu'katar su. Gida ya yi kyau sosai, ya tuna Sa'a ce ta tsara yadda gidan zai kasance, a ransa ya gamsu Sa'adah tana da baiwar fashion and design hadi da creative. Cikin abubuwan da Mk yake yawan tunawa ya Sha mamaki akan lamarin Jawad shine wani lokaci da yake daf da barin kasar ingila, ya fita da su shopping, shagon kayayyakin Mata da kananun Yara na alfarma suka je, Farida ta zabi dogayen riguna na alfarma da suka amsa sunansu, guda biyar ga turarenta designer na Amour amour, ta hada da wani dan kunne mai kawanya da alamunsa daham ne. Kasancewarta bata amfani da kowanne irin mai sai veseline ta cakude shi da gilasirin, tafi bada karfi a shower gel. Jawad na tsaye yana kallonsu. Mk ya juyo ya ganshi a tsaye bai dauki komai ba, ya kalleshi ya ganshi tsaye ya rungume hannunsa a kirjinsa. "Jawad baka dauki komai ba". Ko sai mun je wani mall din?" Ya girgiza kai ya ce "I thought Anty ce kawai zata yi shopping yau". "Kaima ka duba duk abin da kake so ka dauko" Suna tsaye suka hango shi rungume da dogayen riguna irin na Farida sai banbancin kaloli guda hudu, sai takalma na mata masu tsananin tsada kafa biyu, dukkansu kirar kasar itali, ya ajiye gurin buga kudi, ya wuce ya dauko zobe guda daya da ya kusan ninka Dan kunnen Farida. Mk ya kalle shi ya ce "Me zaka yi da wannan kayan? " Ya shagwabe fuska ya ce "Malam so nake yi ba kai ka ce na dauko komai nake so ba?" "Na fa'da amma ai naka na ce ko?" "Malam ni wannan nake so a maimakon nawa, kaga rigunan Nan tsaraba zan yi da su, daya Antyn Lagos, daya Maman Gombe, daya kuma Anty Samira". Mk da Farida suka zuba masa ido domin kuwa wadda duk ya ambato zai bawa Mk bai isa ya ce komai akan su ba. Ya ce " Amma Jawad wadannan sunyi kudi da yawa". Ya kwakkwabe fuska ya ce Ni dai su nake so Malam" Mk ya ce "To wadannan ragowan rigar da takalman da ka kwaso fa, kasan ku'din takalmi daya ma kuwa?" Kai tsaye Jawad ya ce "Mami zan siyawa a kudina tunda bata zo ba". Mk ya yi shiru ya ce "to ai kudin naka ba zai isa ba, sai ka mayar da zoben". Ya ce "Ka cika mini ko ka ara mini ni dai ina son su". Kan dole Mk ya biya kudin kayayyakin nan, wadda ba karamin jijjiga asusun ajiyar sa yayi ba, hatta Farida sai da abin ya mintsine ta, ta lura kusan kullum idan suka fita siyayya irin haka sai Jawad yasan me ya siyo wa uwarsa, Mk kuma baya iya tsawatar masa, kafin su tafi ta san ba karamin kaya zai tara mata ba. Kawai shanyewa take bata ta'ba bari abin ya bayyana ba, Amma abin na tsaya mata a Rai, sai dai ana jimawa take kokarin mantawa. Mk bai sha mamakin Jawad ba sai da ya bishi dakinsa ya ga ya dauko katuwar ledar da yake tara kayan da yake siyowa da sunan Iyah kayayyaki ne masu tsadar gaske. Ya zauna a bakin gado ya ce "to kawo kudin da kace na ara maka, tunda ai kasan ciko mai yawa na yi maka" Haka kawai Mk ya fada Jawad ya fashe masa da kukan shi kudinsa Mami zai siyawa jirgi tunda antaho anbarta a gida kuma Baffa bashi da kudin da zai biya mata. Jikin Mk ya yi sanyi ainun ya kasa cewa komai, da kyar ya ce "Ai ba a haka Jawad! kenan wayo ka mini? Kullum ka yi ta fa'din jirgi za ka siyawa Mami ko zaka biya mata, amma ni ko keke banji kana cewa zaka siya mini ba, alhalin na fita sonka". Yana goge idonsa da rigarsa ya ce "Zan siya maka Malam amma dai ka yi ha'kuri na fara yiwa Mami, kai kana da ku'di, Baban Anty yana da kudi, ita kuma basu da kudi". Mk ya ji haushin Sa'adah ya cika masa zuciya na yadda ta zauna ta yi maganganu da yaro 'dan karami, gashi maganar ta shiga zuciyarsa ainun, ya tsinci kansa da fadin "me za'a yi da halin wannan yarinya". Jawad ya ce "wacece?" Ga mamakin Mk sai ya kasa cewa Sa'aadah, sai ya buge da fadin "wata fitananiyar student dina ce mai baudadden hali, mai wuyar sha'ani". Haka suka cigaba da rayuwar su har wa'adin da Mk zai yi a kasar ya cika. Ya tattara ya taho ya bar Farida da Jawad tunda ita saura wattani uku suka rage mata, Dan haka ya bar mata Jawad dan shima ya kammala third term dinsa. Duk juyin da Mk ya yi da jawad ya bashi kayan tsarabar sa da ya tara cikin katon akwati, baisa ya bayar ba, ya ce shi da kansa zai taho da kayansa domin ba ya so a kaiwa Sa'adah kafin ya dawo. Har Suka kammala watan ukunsu Jawad ba ya bata matsalar komai, sai duk sadda suke hira Rabin hirarsa kuwa ta uwarsa ne. Da azahar Suka sauka a Kano. Kai tsaye gidan Hajiyar Bichi suka zarce suka samu kyakkawan tarba daga Hajiya ga abinci ta tanadar musu ba karmin mamakin girman Jawad ta yi ba Ta kalle shi ta ce yanzu a shekaru biyun nan ka yi wannan uban girman wa zai ce shekarunka sha biyu?". Yamma na yi Mk ya dauki Farida zuwa gidansa da suka zauna da Sa'adah, bai san me yasa ya kasa shigar da ita wanccan gidan da Sa'adah ta tsara shi ba, sai ya gyara ainihin gidansa. gaba'daya gidan ya sha gyara na mussaman hatta fasalin ginin ancanza shi ya zama mai upstairs (bene) an mayar da shi na zamani kwarai da gaske , haka nan ba karamin jere na garari aka yi wa Farida ba. Duk wadda ya shiga gidan sai ya burge shi sosai saboda tsarin ginin tamkar gidajen turawa. Duk yadda Mk ya so ya tafi da Jawad Hajiya kin yarda ta yi ta ce "Ai dama daga nan gidan ka dauke shi, dan haka dauki matarka kuje ta huta gajiya, sosai Jawad ya yi murna da hakan domin yasan goben nan zata sa Uncle Ahamad ya kai shi wurin Maminsa. Leda guda Jawad ya ajiyewa Hajiya na tsarabar ta ta dinga murna tana fadin "Na san zaka yi Imani Jawad". Washagari kuwa Hajiya tasa Ahamad ya kai shi da katon akwatinsa da sai da ya nunawa Hajiya duka kayan ciki, ko kadan bata yi ba'kin cikin uban kayayyakin da Sa'adah ta samu ba, a ranta kuwa murna take yi tana fa'din "Haihuwa wadar sarari ko kana gudu haifi ka Yar". Murna soasai Sa'a ta yi tana fa'din "ai Ni ka yiwa tafiyar nan Jawad, ubangiji ya raya mini kai, ya maka albarka mai yawa". "Amin Mami" ya fada yana kwanciya a

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});