Chapter 122
Chapter 122
Mahmud da ya ga yadda bulalar ta kwanta a kafada zuwa gadon bayan Mk ta tashi sosai wani wuri har ya yi baki tabbacin ya fara fashewa jini ya kume a ciki. Ya tattaro dukkan alhini ya yaba a fuskar sa yana faman fadin "sannu Bichi ashe haka ta shige ka wlh mancewa na yi ta dukan doki ce ba bil'adama ba" Mk ya ce "idan ban yi hakuri ba na Yi Yaya da kai?" Ya nisa ya ce "Ya zan yi ne 'Karfi? da gaske yarinyar nan so take sai dukkan rauni na ya bayyana, ga dai idanuwanta cike suke da soyayyata amma bakinta sai ambaton kiyayya yake, bayan na san abin da nake gani a idonta akwai ninki ba ninki a zuciyarta, Ni kuma ba zan bata damar da zata ja ni a kasa ba, wahalar da na sha akanta bana jin nan kusa akwai namijin da ya shata, ko da na ki dawowa da ita na tabbatar na fita shiga tagayyara akan rabuwarmu! Yanzu kuma naga Shirin shayar da ni wata azabar take yi, bata daukan wayata, jiya kuma 'kaddarar zan yi gamo da ba'kin ciki ta kawo ni shago, kawai sai ganinta na yi da wani dan guntun halitta sun zo tare a motarsa, a gaban motarsa fa ba mayafi sai wannan rigar da hular lauyoyin da basu rufe kwalliyarta ba, gaban rigar bai rufe komai ba". Ya fada yana dukan sitiyari, Mahmud shima ya ji kishin yaron ya kama shi, amma ya daure ya ce "Kai ka bada kofar da zata yi hakan da ka mayar da ita tuntuni da bata zo tana sake shayar da mu wannan ba'kin cikin ba". 'Karfi ya shanye dukkan yadda zuciyarsa take bugawa ya ce "Mk tsakani fa da Allah tsananin rabo ne zaisa yarinyar nan ta saurare ka, ka yi mata zunubin da 'ya'ya mata basa yin sassauci a cikinsa, ka tsaurara kwarai da gaske. Ka yi tsam da ranka wallahi ko Baffah kawai dan zuciyar sa irin ta mutanan da Allah ya zaba ya musu alheri da ha'kuri ne. Banda hakan da tuni gaba ne a tsakanin gidanjenku, amma ko ni din nan Baffah ya na mutuntata ni adalilin ka! Barah gaf da zaka dawo ranar juma'ah ya mini waya akan idan ba damuwa na zo washagari asabar dan Allah. Na taho cikin wasi-wasin menene ya faru, ina zuwa sai ce mini ya yi Daurin aure zamu je Bichi, za'a yi auren cousin dinka, baka nan bai kamata bamu halarta ba, muje mu wakilce ka, a hanyarmu ta dawowa ya ce mini ya ji dadin tafiyar mu domin na debe masa kewar ka kwarai da gaske. Wlh da na dawo gida sai da na yi hawayen tausayin bawan Allahn nan, sonka yake irin son da babu algus, gefe daya kuma na dinga jin kunyar matakin da ka dauka akan jininsa, matu'kar da gaske son Sa'adah kake yi sai ka na'de kafar wandon jure dukkan borenta har mu samu ta zo hannu". 'Karfi ya zarce da fadin "Ka gama da ita, ka sha da ita, ba abin da zata yi maka ta huce tarin takaicin da ka cusa mata". Jikin Mk ya yi sanyi yana ayyana ina ma zai iya fitowa ya fa'di irin abin da ta yi masa da ya tabbatar an gane shi din adali ne na gaske, domin aure ba adadi ya mutu a irin wannan matsalar sannan kuma zubewar mutunci shi ya biyo baya, tunda duk macen da aka saka adalilin tana mu'amala da wani namiji komin kankatar muaamalar kuwa mutane da yawa zasu mata hukuncin babbar mu'amalar take yi. Basu zame ko ina ba sai gaban Hajiyar Bichi suka fa'da mata abin da Alh Isa ya ce. Ta yi jugum ta ce "Ashe kuwa Allah ne ya so ni domin wlh ni kaina kunya ce ta sa nake ta jan kafar zuwa gidansu Sa'a, yanzu kuwa na fasa ba zan iya ba, maganganun Babanku akan turba suke, yanzu ne kake so mu shige maka gaba alhalin a farko ka nuna musu baka da iyaye". Hankalin Mk ya yi tashin gauron zabi. A hankali ya ce " Amma Hajiya da bakin ki kika ce zaki rarrasar mana ita". Ta ce " eh na fa'da amma yanzu na gane bai kamata na shiga ba, domin a lokacin da yarinyar nan take cikin tasku ai baka yarda na yi iko irin na uwa da kai ba, ka ga kuwa bai kamata ace yanzu ita na yi mata karfa-karfa ba, tunda na san da dukkan zuciyarta tana sona tana girmama ni, ku je Mahmoud ya taya ka, zan biku da addu'ar dacewa ubangiji ya huci zuciyarta, amma ni kaina ban jin zan iya yafe irin abin da ka yi mata idan aka yi mini irinsa". Idonsa ya ka'da ya ce "wai har me na yi ne haka Hajiya? Saboda na zabi na bar abin da ta mini a zuciyata shine kuma sai aga ni na zalunceta, na san dai laifin bai wuce kawai dan na yi aure ba". Daga 'Karfi har Hajiya suka hada baki wurin cewa " Ai kuwa ya fi karfin ace kawai, kai yanzu ka barta ta auri wani mana indai kawai ne". "Bana son haka 'Karfi bana son wannan kwatancen" "A a ba da Mahmoud kake ba, da ni kake, ni kuwa ba yadda zaka yi da ni, domin ko yanzu Sa'a za ta yi wani auren da kaina zan jagorancin kaita dakin mijinta". "Dan ka ji irin ciwon da ta ji alokacin da ka tura ubanta ya nemo maka aure". Da rawar murya ya ce "Haba Hajiya! Haba mana! ni ban tura Baffa ba, kawai na fa'da masa zan yi aure, shikuma saboda yana mini kallon Ni 'da ne a gunsa ya shiga cikin harkar tsundum, amma menene laifi na anan?" Hajiya ta ce "Baka da laifi ko kadan, yanzu na gane kawai sanin ya kamatansa ne ya yi yawa. Bai kamata kuma ka ji haushi dan nima zan nuna irin nawa ya kamatan ba". Tashin hankalin da Dr 'Karfi ya lura ya fara bayyana a jikin Mk yasa shi cewa "Ha'kuri dai zaki yi Hajiya, dole a samu Babban da zai taya mu nema da rarrashi" Hajiya ta ce "To sai kuje ku laluba a wani gurin ko za'a dace, sai ku tafi Bichi ko 'Karfi ku samo ai hidimar dan dangi bata lami". Daga haka ta ce "Na sallame ku sallar walaha zan yi". Kwanaki biyar Mk ya na fama da matsanancin kishi da damuwa domin ya kasa ganin Iyah sannan idan zai kwana yana kira ba zata dauka ba, ya lura idan bata ganinsa ta fi jarumta sabanin idan idanuwansu suka sarke da na juna zuciyarta take kasa boye sonsa da yake cikinta. Har gidan Sumayya ya je amma bai Samu ganinta ba adalilin ta cewa mai gadin ya ce bata nan, tunda ta san ba su yi da Alh Mamman ko Anwar wani zai zo ba. Ranar juma'ah bayan masallaci ya samu Baffa a shagonsa a kuma ranar ya dawo daga Gogel. Da sakakkiyar fuska Baffah ya ce "Ina fatan zuwa yanzu ka shawo kan mutumiyar taka ta daina fishin kun shirya kanku?" A raunane Mk ya ce "Ai sam ta'ki saurarona Baffah, jiya har Bichi na je
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157