Chapter 136
Chapter 136
ta iya shu'umanci indai akan kishi ne? Yau ya gasgata hakan domin ko kaffara ba zai yi ba, idan ya yi rantsuwar saboda Sa'adah ta 'ki tafiyar. Dan haka ya yi kicin kicin da fuska, ita kuma sai kokarin yi masa fifta take yi. Yayin da Sa'adah da Zainab suke ganin ikon ubangiji na yadda Farida ta kankane komai, Zainab da Mk ne suke mamakinta. Yayin da Iyah ta san dama Farida zata yi abin da ya fi haka. Abbas ne ya leko daga bakin kofar ya ce "Farida ina ta faman jiran ki, so nake na yi maza na kai ki na dawo, kafin su tafi kar abar shi ba kowa, Hajiya ta tafi tun dazu, zan biya na dauko su Anty Amina Kuma". Ai kuwa ta ce "je ka dauko su kawai, idan Akil ko Ahamad sun zo, sai je su dauko mini motata, ko kuma na fita na hau adaidaita sahu". Abbas ya yi sakare yana mamakinta a ransa tare da cewa "Ah adole ita ba zata basu damar ganawa ba, duk da dai bata nuna bacin rai ko damuwa ba. Sai a lokacin Mk ya ce" amma kin san ban son Ahamad yana hawa motar ki saboda ba ya tuki da nutsuwa, Akil kuma yana shago sai dare ya fara jah yake zuwa". Ta marairaice ta ce "Ba damuwa sai na hau adaidaita sahu". "A a bana so kin sani, bana so". Ya sake sassautawa "ya ce ki je ya kai ki, ana idar da Sallar isha ki rufe gidan, sannan ki taimake ni ki sha maganin ki please". Ya fa'da cikin sigar rarrashi da kulawa. Amma ta yi mirisisi ta ki tafiya, lamarin da ya sake dagula lissafin Sa'adah, wai yau a gabanta wata macen take nunawa ta fita son Mk, ta fita kusa da shi. A gabanta shima ya ke nunawa wata macen tattali da kulawa? Wannan shine duniya rawar yanmata. Shirun da Farida ta yi ya tabbatarwa da Mk bata amince bane, ya kalleta a tausashe ya ce "Ban son ki wuce lokacin shan maganin ki ne, gobe idan zaki taho, ki taho da shi, sai ki yi ta zamanki, amma yanzu taimake ni ki je ki kular mini da lafiyar ki". Nan ma ta yi shiru, Mk ya ce "shikenan ai, tunda so kike mu kwanta gaba'daya". Dakin ya yi shiru na mintina uku, Zainab na mamakin irin wannan al'amarin, ta kasa cewa komai duk da bakinta cike yake da tarin maganganu, da suke bu'katar fashin ba'ki. Irin kallon da Farida take yiwa Mk da idanuwanta masu maiko ya sa nan da nan zuciyar Sa'a ta hauro, ta kalli Abbas dake bakin kofa yana tsayawur jiran Farida, amma ganin Sa'adah yasa ta fasa tafiyar dan kar ta samu damar 'dagawa mijinta hankali 😀 Ta ce "Uncle Abbas" "Na'am Anty Sa'adahtu". "Tafiya zan yi, kuma akwai sakon da zan fa'da masa, zo ka ri'ke mini shi zuwa waje na mintina kadan". Da sauri Abbas ya shigo yana cewa "daga nan ma na zagaya da shi, dazun nan likita ya gama ce mini kwanciyar ta yi yawa, ya dinga yin atisaye ko a cikin dakin nan ne". Ya isa jikin gadon ya mikawa Mk hannun, ya dago shi. Ya sunkuya ya janyo masa takalma a a kasan gadon ya saka sannan ya mikar da shi, suka fita a hankali. Zainab ta dinga jin wani irin farin-cikin iyakar da Sa'a ta nunawa Farida. Sun Jima da fita sannan Sa'adah ta dauki handbag dinta zata bisu, Farida ta ce "Gogel ko zaki fitar masa da kujera, jikin nasa ba kwari har yanzu". Da sauri Sa'adah ta saki murfin kofar, ta dawo ta zuba mata ido, sai kuma ta sassauta fishinta tace "Da a ce Sa'adatu Kika kira ni da shi, da ko kula ki ba zan yi ba, sai dai na ce miki to, ko da ba zan yi abinda kika ce din ba, sai dan na nuna miki am matured now. Amma tunda Kika 'Kira ni da Gogel zan tabbatar miki har yanzu waccan Gogel din ce dai da kika sani, Billahillazi ki fita a idona, kada ki sake yun'kurin shiga tsakani na da shi, ko ki nuna mini ga yadda zan yi masa, if not kin dai sani. Ba zai zamewa Iyah Basiru komai ba wajen nuna miki har yanzu ina cikin shekarun da ba a mini kan kara ban yi na ice ba". Daga haka ta juya tana cewa "Zainab zo muje, idan na gama sai mu wuce ba sai na dawo nan ba". Suka fita bayan Zainab ta cewa Farida Allah ya Kara lafiya. Sun zo inda su Mk suke zaune, Zainab ta yi masa addu'ar samun lafiya mai dorewa ta yi gaba, haka Abbas ma ya mike suka basu wuri. Sa'a ta zauna tamkar gaske magana zata yi masa, amma ban da cika tana batsewa ba abin da take yi. Ta tabbatar Farida na hango su ta windo, shiyasa ma da ta zata zauna sai ta juya baya ta yadda ba zata ga fuskarta, ba haka ma Mk bayansa zata hango. Banda son ta nunawa Farida dan taki tafiya ba shine dalilin da zata hanata magana da shi ba, da bata tsaya kula Mk ba, tunda agabanta yake nunawa Farida soyayya har ya na lallaba ta. Dukkansu kowa fishi yake da dan'uwansa, domin ganin ta da ya yi da Khalil ba karamin kidima shi yake yi ba, dan haka, ya danne zuciyar sa ya ki mata magana. Amma dai a kasan ransa sun bashi dariya ita da Farida kwarai da gaske. Mintina ashirin na cika ta tashi ga mamakin Mk ya ga ta mi'ke tana murmushi ta fito da wayarta ta Kira Zainab tana fa'din idan Abbas na kusa ki ce masa ya zo mun gama". Aikuwa sai da Abbas ya zo, ta tafi bata ce da shi uffan ba, sai Abbas ta yiwa sallamah da fatan samun lafiya ga marar lafiya. Mk ya bita da ido yana ganin yadda take tafiya, sai ayyanawa yake yi ko sai yaushe zata daina rikicin gan-gan? Ban da karfin halin Sa'a ya zata zo ta tarar da mace da mijinta, sannan ta ce sai ya fito waje sun yi magana alhalin ba maganar zata yi ba, kawai son rikici ne da son nunawa Farida karfin da take da shi a zuciyar sa. A mota Zainab ta ce "Tabdi yau na ga kishi, ashe haka abin yake?" Sa'a da dama kiris take jira sai kawai ta fashe da kuka. Jikin Zainab ya yi sanyi sai kuma ta ce "Menene abin kukan kuma? Duk irin jarumtar da Kika yi". Ta kasa magana illah kukan da ya ki yankewa, tana ta hararo hannun Mk a cikin na wata a gabanta kuma, tabbas har ta mutu ba zata daina kokawa ba. Da kyar Zainab ta shawo kanta, "kin samu labarin auren Halima next week?" Murya a dakushe ta ce " a a" Zainab ta ce "to ai ke ce kinki shiga cikin group din mu na old girls a WhatsApp". A sanyaye sosai ta ce "Bar ni kin ji, inace ga abin da biyewa 'kawayen ya janyo mini, kina kallon yadda wai magana da Malam ya zama sai an mini iyaka. Ta rushe da kukan da ya sanyaya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157