Chapter 95
Chapter 95
ta ta'ba jikinta. Zafi zau ta ji, ruwa ta samo da tawul ta dinga goge mata jiki. ta taimaka mata ta canja Riga, ta zubo mata kunu a kofi ta matsa mata ta shanye, sai dai tana gama shan ta amayar da shi tas. Haka Inna ta sake gyara mata jiki, da kuma wurin, tana fatan inama ace ciki ne da ita wata'kila hakan yasa mijinta ya mayar da ita. Baffah da bai fita ba, shi ya nemo Usaini mai chemist ya duba ta, ya kawo mata magungunan da zata Sha. Tafi kwana uku tana mukurkususu, kafin ta fara warewa, saboda yanzu Inna ta sassauta mata, damuwar ta dan yi sauki. Sati biyu da kammala Iddarta, tana tsakar gida tana wankin kayansu dana Inna sai ganin Jawad suka yi ya shigo a guje kamar yadda ya Saba. Kai tsaye ya nufi uwarsa ya rungume ta, ita kuma idon Inna ya hana ta rungume shi, sai ta bige da fa'din wa ya kawo ka? Yana jikinta yace " Malam ne, kullum sai na yi kukan gurin ki zan zo shine yau Hajiyar Bichi tace sai ya kawo ni, tunda jiya anyi hutun boko". Inna da ta ke zaune tana fere doya tace "wato Jawad ba ka ganni ba ko, Anya kuwa za ka yi al'kawari?" Kafin ya yi magana sallamar Hajiyar Bichi ta cika kunnuwansu tare suka shigo da Baffa, Inna ta mike da azama tana fa'din lale da Hajiyar Jawad, ashe tare ku ke tafe?" Falo suka shiga! Inna ta gabatar mata da ruwa ta zauna Don gaisawa, sai taga Hajiyan na share hawaye Baffa na cewa "to ya za'a yi, sai ha'kuri, komai rubutacce ne, idan rabo bai 'kare ba za su koma, idan kuma ya 'kare sai duk mu yi ha'kuri, mu bisu da addu'ar fatan alheri! fatana dai ki cire damuwa a ranki. Wallahi bamu 'kullace ku ba, Ni ko Mutari har yau ban ga laifinsa ba, Allah shine shaidata, kawai dai zan so ace sun shirya kansu ko dan rayuwar 'dansu ta inganta". Murya a dakushe Hajiyar ta ce " Nima abin da nake ta hango musu kenan ban da dole yaushe za'a raba yaro da uwarsa! kome za'a masa ba zai gamsu ba idan ba uwarsa yake gani ba. Haka nan ba kowacce mace bace zata ri'ke'dan da ba nata cikin adalci da kyautatawa ba, akwai su amma sun yi 'karanci 'kwarai da gaske". "Allah ya musu za'bi mafi alheri" Baffa ya fa'da yana barin falon. Hajiya da Innah suka ha'da baki wurin cewa " AMEEN". sannan suka shiga gaisawa tare da jajanta 'kaddarar da ta fa'dowa yaran su. Jikin Hajiya a sanyaye yake sosai, tunda abin nan ya faru take son zuwa, amma kunya da nauyi sun hanata, sai yau ta yi shahadar zuwa, ha'kuri ta bayar yafi cikin kwando, karbar da ta samu daga iyayen Sa'a yasa ta sake jin nauyinsu ainun, karamci a jininsu yake, tabbas Mukhtar ya yi asarar irin zuri'a me yakana da alheri. Ganin Baffah ya fita ya Sanya Sa'a dauko Hijabinta ta saka ta shiga falo Jawad na binta tamkar jela. Daga gefe ta tsugunna, ta gaida Hajiya kanta a 'kasa. Hajiya ta hau fa'din taho ki zauna kusa da ni Sa'a. Da rarrafe ta karasa kusa da Hajiyan, amma kanta a 'kasa tana Jin kunyar Hajiya na kamata irin wadda bata ta'ba ji ba. Sosai Hajiya ke kallon yadda ta lalace ta yi ba'ki sosai, 'kwalla ta cika idonta a sanyaye ta ru'ko ta jkinta, hawaye ya gocewa Sa'a ba tare da ta shirya ba, tana yiwa kanta jajen rashin suruka irin Hajiya! Ta tabbatar samun uwar miji irinta a Yau zai yi matu'kar wahala. Itama Hajiyar kukan take yi, tausayin Sa'a da Mukhtar da tilon dansu na matu'kar sa ta zubar da hawaye. Wacce irin ba'kar 'kaddara ce ta afka musu haka? Mussaman yanzu da taga irin bibiyar da Jawad ke yi wa uwarsa, duk inda tasa 'kafa nan yake mayarwa, duk irin gatan da take masa, duk yadda ubansa yake masa siye-siyen kayan wasa da na ciye-ciye kala kala, bai hana ya yi kukan neman uwarsa ba, yanzu da ya ganta kuma ita ka'dai yake bibiya duk kuwa da yasan ubansa na 'kofar gida a zaune. Duk dabarar Hajiya dan Sa'a ta fa'di musabbabin rabuwar ta su ta 'ki!kuka kawai ta ke yi mai tada hankali, Jawad kuma na ta goge mata kamar yadda ya saba yi mata idan tana kuka. Tausayinta ya sake cika zuciyar Hajiya, ta dinga rarrashinta da kalmomi masu da'di. Da zasu tafi Hajiya ta kalli Jawad taga ya ri'ke Sa'a sosai, sai ta yi nufin tsokanar sa ta ce "to zo mu tafi Jawad". Ai kuwa nan da nan yasa kuka yana nuna dukkan yatsun hannuwansa yana cewa "Malam fa ya ce kwana haka zan yi?" Hajiya ta yi gaba tana cewa "yi shiru da bakinka wasa nake maka". Har zaure ta yi wa Hajiya rakiya, Mk na bakin kofar gidan a jingine yana waya, take zuciya ta ayyana wa Sa'adah da Farida yake waya a kofar gidansu. Hawaye ya sake kwace mata, Hajiya da ta zaci ganinsa yasa ta kuka ta hauta da fa'da sosai tana cewa "wanne irin sakarci ne wannan Sa'a? Kina bada ni, banda bayar da kai menene ba zaki warware ki saki ranki ba, kina kallon kanki a madubi kina ganin irin lalacewar da kika yi?" Ita dai Sa'a kuka kawai take yi 'kasa 'kasa, Hajiya ta nisa ta cigaba da cewa "ki kwantar da hankalin ki, kin ji!komai zai wuce kamar ba ayi ba, so nake nan da wata daya na ga kin dawo Sa'adatun nan mai birge yara da manya, Allah ya shiga lamarin ki, ya baki miji nagari, da zai wanke miki dukkan ba'kin cikin da kika kwankwa'da". Wani irin kishi da Mk bai yi zaton zai sake ji akan Sa'adah ba, ya kama shi, takaici yasa shi barin bakin 'kofar ya nufi mota ya shiga yana ta a'uziya, saboda yadda ya ji takaicin Hajiya ya kama shi matu'ka da gaske. Yana tuki amma zuciyarsa tamkar ta fashe, a gabansa Hajiya ke wannan fatan. ita kuma da ta lura da yadda yake ta 'dacin rai, tunda ta shigo motar ta gane kishi ne ya turnike shi, dan ayiwa matar da ya saka, ya ki mayar da ita fatan samun wani mijin. Ta dinga kallon yadda ya fusata tamkar kububuwa, Hajiya ta tsinci kanta da mamakin kishin maza, ka saki mace, kace ba za ka dawo da ita ba. Sannan baka son kowa ya aureta alhalin tana cikin shekarun da take bu'katar auren. Itama haushinsa ya kamata da ya kasance cikin masu son kansu, sannan har ita zai yi wa wannan fishin?. Dan haka Yana shan kwanar layin 'Dan Hassan da shine layinsu amma a ciki suke sosai, sai an hau abin hawa. Murya a dake ta ce samu wuri ka tsaya! Bai yi musu ba, ya gangara ya yi parking. Ba jinkiri Hajiya ta fito cikin sa'a kuwa ta tsayar da dan adaidaita da zai shiga ciki, ba 'bata lokaci ta shiga suka tafi. Ba'kin ciki ya sake kama Mk idonsa ya yi jawur, ji yake tamkar ya hadiyi zuciya ya mutu, Hajiya da Sa'a su huta da ganinsa. Yasan Jawad kawai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157