Chapter 12
Chapter 12
yi kai ka'dai." Shi kuwa ya ci gaba da dariyar shi a sake yadda yake so. Ta idar da sallar Maghrib ke nan tana zaune tana tasbihi, zuciyarta cike da farin cikin fara gyaruwar al'amuranta, wayarta ta hau kuwwa, ganin sunan Baban dady yasa ta jin wani farin ciki ya 'kara kama ta, ba ta yi azarbabin 'dagawa ba har ta katse. Kafin ta yi wani yun'kurin, ya sake 'kira, haka ta gama yau'kinta, ta dauka hadi da yin sallama,"Ranki ya dade ai na zaci ba za ki dauka ba ne" 'Yar dariya ta yi, "Akan me? Sallah na idar." "Ya mutanen gidan to?" Ya tambaya, ta amsa mishi da, "Duka lafiya Lau" "Ina son ganin ki wanne lokaci zan same ki?" sanin mutuncinsa da karamcinsa ya sa ta fadin ko yaushe "Ina gida!" "To ki saurare ni anjima kadan zan iso." "Sai ka zo." Ta fada tana jin wani irin nisha'di na tsirga mata. Wanka ta shiga ta fito ta shirya cikin lallausan yadi ruwan hoda, mai shegen tsada ba shi da adon komai haka yake plane sai yauki yake da 'daukar ido. Doguwar riga ne aka 'kawata da shudin stones masu sheki matu'ka, don haka ta yane jikinta da matsakaicin mayafi blue, mai da roll on kawai ta shafa, kasancewar turarukanta sun kama kayanta sosai kuma ma'abociyar yin turaren kaya ne irin na barebari (garam). Duk da dare ne, sai da ta shafa powder ta kuma zagaye le'banta da jan baki ruwan hoda. Yanayin jikinta irin tauraruwar wasan kwaikwayon nan ce Hafsat Barauniya, duk da Hafsar ta fi ta shekaru, ta kuma fita hasken fata, kasancewar Sa'adah mai duhu ce, ba kuma ta yarda ta shafa man da zai canja mata launin kalarta ba, illa tana 'batar da kud'a'de masu yawa wurin siyan tsadadden man dake fitowa da ainihin kalarta, ta goge ta yi tas da ita, ta yadda ko mace sai kin yi sha'awar launinta shi yasa idan akwai tambayar da a rana ana mata ya kai sau biyar, ita ce wanne mai ki ke shafawa, wanne mai ki ke amfani da shi? wani lokacin ta fa'da, wani lokacin kuma ta yi murmushi wushiryarta ta sake 'kawata ta tace "Vaseline" Tana tsaye jikin Shoe Rack (ma'adanar takalman)ta ta fito da wani Tom's blue, Innarta ta shigo ta kalle ta ta ce, "To 'dawisu sarkin ado a wannan daren kike wannan kwallliyar anya Iya baza ki rage wannan 'kyale-'kyalen ba? Shi yasa ai da yawa mazan suna son zuwa gunki amma gani suke kin fi 'karfin su" "Inna tunda ba ni na fa'da ba ai shi kenan, idan mutum da gaske son nawa yake ya zo mana idan mun daidaita ai zan aure shi ne" "Yanzun kuma mai za ki yi da takalmi, da na ga kina gogewa? Na san dabi'ar ki ce ca'ba kwalliya ba sai za ki fita ba, amma wannan takalmi ai na fita ne, kuma kin san ba inda za ki a wannan daren" "Kai Inna don Allah!" Ta fa'da cike da shagwaba, "Ni fa ba fita zan yi ba, ba'ko zan yi" "Kin fa'da wa Baffanku za ki yi Ba'ko?" Kai tsaye ta ce, "Na fada masa kafin ya tafi sallar Isha" "Shi kenan amma don Allah Iya ki daina bata wa mutum lokaci kina kuma karbe mishi abin hannunsa alhalin kin san ba auren sa za ki yi ba, yaudara ba kyau. Alhaji Mamman din nan ni ban ga laifinsa ba, mutum mai mutunci mai nagarta ga shi babba ne ya mallaki hankalinsa amma kina tasa 'kafa kina shure shi, kuma kina kar'be mai dukiya" "In sha Allah, Inna ko mai ya kusa zuwa 'karshe, ki 'kara 'kaimi wurin yi mini addua" Dadi ya kama uwar tata kusan yau ne Sa'adah ta bude baki ta yi magana mai kyau akan aure. Nan da nan ta hau fa'din, "Addu'a kam ai kullum yin ta nake, mantawa na ke da ko mai sai ke idan ina addu'a, Allah ya miki zabin alheri" Ta fita tana sake cewa, "Ba abin da ke raina irin in gan ki a 'dakinki kin nutsu wuri daya" Har sai da ta yi sallar Isha sannan ya mata waya ya iso. Fararen kujerun da ta tanada saboda zuwan wanda tabawa izini, ta 'diba ta fita dasu zauren gidan nasu da ke da yalwar fili, tana zuwa shi ma yana 'karasa shigowa, da sauri ya karbe kujerun yana cewa "Ai da kin sani kin jira na zo na 'debo, wannan ba aikin uwargidanmu ba ne" Dariya ta yi, "Za ka fara ko?" Shi ma dariyar ya yi, "Zan fara fa'din gaskiya ba" komawa ta yi ta ha'do mishi ruwa (pure water) da kuma kunun ayan da Inna ke yi akan faranti tare da Tumbler, ta ajiye mishi tare da cewa "Ga ruwa" Ya yi godiya ita kuma ta hau gaishe shi tare da tambayar iyalinshi, ya ba ta amsa da cewa, "Ai ta yi fishi da ke tace rabon da ki taka mata tun barkan haihuwar Kausar, ga Kausar tana gudu ko Ina." Ta ce, "Hidimar makaranta ce ta 'boye ni amma yanzu kam na gama za ta gan ni, a ba ta ha'kuri" Sai da ya bude ruwa ya sha sannan ya yi gyaran murya ya ce, "Zuwan fa na mussaman ne, tare da albishir din abin da muka dade muna nema ya samu, takanas MK ya same ni ya ce mini ya kira ki, amma kin kashe mishi waya haka ne?" Kai tsaye ta ce "E ai ban san shi ba ne" "Ban gane ba ki san shi ba ne"? "To bai gabatar da kansa ba, ya fara maganganun da ban fahimce su ba". Shiru ya yi tare da cewa "Amma ba ki da lambarsa ne?" "Ban da ita" "Ba ki da ita?" Ya tambaye ta cike da mamaki. "E!" Kawai tace ta ja bakinta ta tsuke. Kamar zai bar maganar sai kuma ya ce, "Amma aikin haddace a kanki" Nan ma ta ce, "Na manta" Ya yi dariya, "Sa'adah wai yaushe kika cire mu a ranki har haka ne?" Murmushi ta yi ta ce, "A lokacin da na fahimci ba komai ne idan ka rasa yake dawo maka ba, ba kuma komai ne kake so yake zama alheri ba" Da sauri Dr. 'Karfi ya ce, "To mu dai alheri ne kuma mun dawo mu sake daukar ki a karo na biyu." "Amma bai kama ta, ya manta cewar aure ya 'kare a tsakanin mu ba?" Ta fa'da cikin 'daure fuska. Alkalamin SURAYYA DAHIRU ✍🏼✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·• 17-18. " A a ban sani ba bai kuma fa'da mini ba." 'Karfi ya fa'da cikin yanayi na rashin gamsuwa, tare da zuba mata ido yana ta a uziya saboda yadda shaidan ke 'kawata mishi ita, ya riga ya binne wannan abin a ransa har abada ba zai yi tarayya da MK akan mace ba, macen da ya tabbatar amininshi yana mata son da bai yi wa kansa ba. Ya numfasa ya 'kira sunanta, "Sa'adah karki wahalar da ku, da ke da Mukhtar kuna son junanku, nan duniya ba
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157