Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 125

Chapter 125

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wani namijin kamar yadda ka ke dandana Balarabiyar Yemen". A sanyaye ya ce "Sa'a ina jiye miki tsoron kar ki zama ajalina, domin kuwa banda lafiya, duk sadda na ganki sai kin yi mini fami a akan jinyar da nake yi". Kai tsaye ta ce" Tunda bakin cikin ka bai mayar da ni gawa ba, na tabbatar kaima ba zaka zama ba". Cikin gajiyawa ya ce "Next week Jawad zasu yi hutu, gaba'daya zai yi hutunsa a gurinki". Maimakon ta ji dadi saboda ta san dan ya faranta mata ne yasa ya yanke wannan hukuncin, sai ta yi nufin gwasale shi. Ta ce "bana bu'katar ganinsa ma bare ya mini hutu, inace saboda kar ya zo na zuga shi yasa ka kai shi makarantar kwana? Saboda kana son sai ya so Farida sama da ni yasa ka hana ya kwana a gidan nan sai dai ya zo ya yini? To shima na barka maka shi ban bu'katarsa, Ni kuwa a duniya me zaka mini na huce, ka zalunce ni iyaka". Kafin ya yi magana sai ganin Innah suka yi, a ladabce Mk ya sunkuya ya gaishe ta, ta amsa babu yabo babu fallasa, daga gaisuwar bata ko tambayi Hajiyarsa ba bare matarsa, ta juya tana cewa "kin dora girki kin barshi zai kone, daga cewa zaki karbo sako?". Wannan shagulatin bangaro da Inna ta yi masa ya matu'kar dukan zuciyar sa, yana ganin rashin nasarar sa a fili, Bai ga laifinta ba ko kadan, domin ya fahimci tana kan fahimtar su Baba Isa da Hajiyar Bichi ne. Wato Baffah ne kawai hoope dinsa. Akwai gumurzu kenan dan kuwa sai inda karfinsa ya kare, yanzu ne zai yi dambar jefa alkalamin sa cikin Tawada. Domin ya ga maneman nata dukkansu basu da makusa, shine ma mai tarin kalubalen rashin samun goyan baya a wurin iyaye da Sa'adatu sa'ar Mata. Surayya Dee ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 NA *SURAYYA DAHIRU*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *_Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha babban laifi ne da yake dai da satar Dukiya._* _*A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba.*_ *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *GAISUWA GA* *HAUWA BELLO GANDI*. *MUM KHADY*. 98-99. Har sati ya zagayo Mk bai da nutsuwa, Farida kanta bata da sukuni adalilin halin da take ganin Mk a ciki, duk yadda take jin kishin Sa'adah sai take yin jarumtar boyewa. Take ta hadiye sauyin da take gani a tare da shi, gefe daya ma sai take hilatar sa da bashi labarin fa'dansu da Iyah a FGC, idan kuwa ta yi hakan sosai ta ke samun walwalarsa ya yi ta dariya, hirar kuma ta yi tsayi. Ranar dauko Jawad da wurwuri Mk ya tashi yana ta saurin tafiya, wani irin zumudin dawowarsa yake yi domin shine tsani na biyu da zai taimaka wurin shawo kan Sa'adah. Ya tuna yadda Jawad ya matsa mata ta gaishe shi ranar visiting. Ya sake tuna rokon da ya mata akan ta yarda su taho Kano tare, dalilin da ya zama sanadin da ta doke shi. Ya dinga murmushi yana jin kwarin guiwa na shigarsa. Tun jiya kuma Farida take ta faman hada masa snacks din barka da zuwa. Domin a harkar Baking ta yi zarrah, abinci wahalar sarrafawa yake yi mata amma idan ta yi za'a ci cikin dadin rai ba wai iyawa ne ko kadan bata yi ba. Amma harkar cake da su meatpie hadi da su samosa tafi karfi anan. Wannan karon har wani cake ta yi masa na mussaman, tamkar na murnar zagayowar haihuwarsa saboda girmansa da kyaunsa. An rubuta welcome to Home Dear Jawad!. Lamarin da ya farantawa Mk rai ba ka'dan ba, ya dinga gode mata, tare da yabawa. Yana futa ta zube kan kujera, tana son ta ga dame Mk ya rageta? Ta gama tunaninta ta gamsu bai rageta da komai ba, ko a harkar auratayya kuwa, anan bangaren ma ta lura yana daga mata kafa soasai saboda lalurarta, amma bu'katar sa ta zarta yadda yake mu'amalantar ta saboda rauninta da yake gani. Tsananin son Jawad da yake yi ne kawai yake dan mintsinin zuciyarta, domin ta gane son uwarsa ne ya shafe shi. Ta kuma amince ba laifi bane yin hakan, sai dai zuciya da bata da kashi, yasa take jin rashin da'din soyayyar, duk da kuma zata shaidi soyayyar Jawad bata rufewa Mk ido ya kasa tsawatar masa ba, yana iyakar kokarinsa wurin saita yaron, ko akan al'amarinta ma ba ya yi masa ta Da'di. A bangare 'daya ne, take ganin raunin Mk akan 'dan nasa, matu'kar suka fita shopping, indai ya ga ta zabi kaya to kuwa sai ya daukarwa uwarsa irin kayan sai banbancin kala, Mk kuma baya iya hana shi, ko cewa ya yi ya rage, da zarar ya bata rai shikenan zai ce ya dauka. Ta dinga jin sha'awar haihuwa na mamayarta, ta daga hannu ta ce "Na sani sarai baka manta da ni ba ya Allah! Idan ka tashi bani, ka bani mai lafiya, mai jin kai, mai kuma albarka. Ina neman tsari da wadda zai gigita zaman lafiyata da ta mutanan da suke kewaye da shi, Ina neman tsari da marar lafiyar da jinyar sa zata shagalar da ni yin ibada da yawan tuba da godiya bisa ni'imomin da ka mini marasa adadi". Hawaye ya ziraro mata ta sa tissue ta goge idanuwanta, ta sake cewa"Allah kar ka bari na kunyata, kai ka halattawa maza yin mace sama da daya, albarkacin yarda da hakan da na yi Allah kar ka bari na wulakanta akan wata da muka yi tarayya a jinsi guda". Kuka sosai ya kwace mata saboda kishin Sa'adah na neman hanata sukuni a zuciya. Ta Dade kafin ta tashi ta yi wanka, ta doro alwallah ganin takwas har da rabi sai tada sallar walaha, tana ta rokon a sau'ka'ka mata kishi, a kuma karawa Mijinta sonta da tausayinta. Ta rufe addu'ar da yiwa Mk fatan samun cikakkiyar lafiyar da zai gamsar da su, da kuma budin arziki, ta sake rokar masa ikon yin adalci, tana kuka take cewa Allah ka hana shi zaluntata, Allah ka bashi karfin zuciyar da zai yi adalci na gaskiya. *Ko mata nawane masu irin wannan dabi'ar?* *Shin kina sallar Duha kuwa?* *Idan ba kya yi maza ki fara domin Allah ya yi rantsuwa da lokacin, sannan kin yiwa gabbanki sadaka a yinin gaba'daya*. Sun iso Wudil, Mk ya ji bari ya ziyarci tsohon amininsa da suka yi F.C.E. Bichi tare. Ya laluba ba lambar wayarsa, ya dai dinga shiga hanyar ya gano gidan. Ai kuwa a kofar gidan ya tarar da shi yana alwalar sallah juma'ah. Da wata irin murna ya kar'bi Mk! Ganin lokacin sallah ne kawai sai suma suka yi alwalar suka zarce masallaci. Suna dawowa aminin nasa ya baibaye su da abinci tamkar dama yasan da zuwansu, Mk ya dinga tsokanar su da cewa wai har yanzu baka kara aure ba? Kullum uwargida na office?" Dai dai lokacin matar gidan ta dawo sanye cikin uniform tabbacin Ma'aikaciyar lafiya ce. Mk ya tasa ta gaba yana fa'din "

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});