Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 76

Chapter 76

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,201 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

tsinci kanta da adduar ALLAH yasa su Halima ba su jefa ta cikin HALIN YAU na bin malaman tsubbbu, domin ta tabbatar tun shekarun baya da Halima bata gama sanin kanta ba, take zuwa gidan malamai, ko aiken uwarta ko na kanta. Har ta bar gidan tana jinjina wa Mk tana fatan Allah ya bata miji mai kwatankwacin halayyar sa. Manyan kudade Mk ya samu a zaben da aka gudanar, saboda karamar hukumar da aka kai shi, itace mafi yawan jama'a, ganin gwamnati mai ci zata sha kaye, sai ta hargitsa zaben wannan yankin, tare da kiran Mk har gidan gwamnati a sirrince, aka tura makudan kudade a asusunsa akan ya canja alkulluman zaben, ya karbe kudin kamar yadda aka sanar da su. bai canja alkulluman ba, amma sai sakamakon ya zama inconclusive, ma'ana bai kammala ba. Kwana biyu yana jin farin ciki, yana ayyana indai kayan 'kawa sune muradin Sa'adah zai mata su, zai kashe mata ko nawa ne dan zamansu ya dawo tamkar shekaru biyun farko na aurensu. Ba zato, ta ganshi da deep freezer, hankalinsa ya kwanta da ya ga Sa'adah ta yi murna, rabon da ya ga murmushinta sosai irin haka tun kafin su fara yar tsama. Tare suka fita, suka yi siyayya mai uban yawa da tsada, hatta Sa'adah da kanta sai da ta girgiza da irin manyan laces da atamfofi super, da kuma shadda getzner da Mk ya dinga dibar mata. matu'kar tace abu ya mata kyau zaice ta dauka. Barin takalma kirar itali da dogayen riguna rantsatsu, hatta turaren Escada da yasan tana so amma baya iya siyansa saboda tsadarsa, a wannan lokaci guda biyu ya siya mata, bayan kayan kwalliya na garari, suka zarce bakin asibitin Nasarawa, suka yiwa Jawad siyayyar hadaddun kaya masu yawa, hatta dan gidan Mahmoud da ya kasance jariri(Dady) sai da suka masa siyayya sosai. A hanyar su ta komawa ya bata labarin inda ya samo kudi, ya kara da cewa "Ina son na kewaye mana filinmu, a kuma fara ginin zuwa inda zai samu, a hankali kuma sai na dinga yi, har na kallama". Ya kalleta ya ga farin cikin ta ya kasa boyewa yace "ki nutsu ki fada mini irin tsarin da kike so a miki a ginin, nasan dai kina son garden?" Da azama tace "Da swimming pool, sannan upstairs nake so, irin wadda kafar benen zata kasance a tafken falo, a mini dining area, sannan kicin ya zama a cikin falon yake a fili, Ina fatan ka gane irin wadda nake nufi?" Cike da shauki yace "Na gane duk da bai gama zuwa mana ba, nasan kema a finan finan ketare kike ganin kicin din, ba damuwa za'a miki irinsa Ummu Jawad my dear". Ta rufe ido tana jin duk wani kunci na zuciyarta ya wanke mata tas. Shikuma yana ta barin jiki wirin sake sata walwala. Tafiya ya shirya musu zuwa Abuja, duk a kokarinsa na son dawo da amincin dake tsakanin su. Gidan Mahmoud da yake Goron Dutse, aka kai Jawad saboda makaranta, kuma yafi kusa. Ranar Alhamis suka tafi, sun Isa lafiya, karfe uku suna madaidaicin Hotel din da ya kama musu daki. Sallah suka yi, sai cin abinci ya biyo baya, wadda a hanya suka tsaya ya siyo, sai da suka koshi, suka yi wanka dan warware gajiya, sannan suka dora da sallar la'asar. Barcine ya gwada musu fin karfi, Mk ne yafara yi, Sa'adah ta zuba masa ido tana kallon kyakkawar fuskarsa, da yadda yake sauke numfashi a hankali cikin nutsuwa, wani irin shauki na mamayarta, tana jin sonsa na bin duk wata kafa ta jikinta. A haka itama barci ya wuce da ita ba zato. Sai daf da maghrib suka farka, suna mamakin lokacin da suka shafe suna barci. A gurguje, Mk ya dora alwallah ya fita neman massalaci, ai kuwa cikin sa'a bai yi tafiya mai yawa ba, ya samu. Kafin ya dawo Sa'adah ta ninke shimfidar gadon, ta dauko bedsheet din da ta zo da shi ta shimfida, ta sake dauko burner ta jona ta zuba turaren wuta, nan da nan daki ya dauki daddadan kamshi. Ganin lokaci ya tafi bai dawo ba ta gane sai ya sallaci isha lafin ya shigo. Ya dawo ya sameta cikin kwalliya sosai, ga sanyi ac da kamshin turarenta da kuma na turaren wuta ya cakude, dakin ya zama na mussaman. Da sauri ya yi wurgi da ledojin hannunsa wadda gasasshiyar kazace, sai kuma ruwa da yogurt masu sanyi. ya isa kusa da ita yasa hannun ya rungumeta tsantsan yana ta shin shinarta, ita kuma ta lafe a jikinsa tana jinta in a new world. Sun jima a hakan, kafin ya saketa, ya zauna a kasan kafet, idonsa ya kada, leda ta bude ta dauko plate da ta juye musu kazar, suna ci ta gabatar masa da shayi a dan karamin flask ga kuma cup da spoon a ciki, ya kalleta da murmushi yace "shiri kika yi haka?" Murmushi ta yi kawai. Suna kammalawa Sa'adah ta yo brush, ta hadawa Mk ruwan wanka. Kafin ya fito ta shirya cikin sabbin nighties masu daukan hankali. Ya fito daure da faffadan tawul, ya tarar da jallabiya da gajeran wando akan gado, ga kuma body spray dinsa na Malizia. Turaren kawai ya fesa ya dauke kayan ya dorasu kan side drower. Ya zauna sanyi dakin na ratsa shi, yana ayyana suna komawa zai sanya musu Ac. Tana tsaye tace "ba zaka sanya kayan ba?" Ido ya kanne tare da fadin "Ban bukatar su a yanzu". Kunya ta kamata, ta waske da fadin "Mai ba zaka shafa ba shima?" Maimakon ya amsa mata sai ware ya dukkan hannuwansa biyu alamun ta zo gare shi, ta tsaya tana kallon sa, ta kasa motsawa, yace "plz Dear come to me". Cikin kunya ta isa gare shi, ya zaunar da ita kan cinyoyinsa ya rungume ta tamkar zai hade su. Ta lafe a kirjinsa tamkar wadda zai shayar da ita, ya sunkuyar da fuskarsa daf da tata, numfashin su ya dinga haduwa, tsinin hancinsa akan nata, jikinsu ya dauki wani irin tsimi. Ya raba hancinsu, amma fuskokinsu a hade. Cikin wata murya da Sa'adah bata sanshi da shi ba yace "Ina sonki, ina son na rayu da ke! Dan Allah stay with me". Jikin Sa'adah ya yi la'asar, da murya marar amo tace "kana ganin zan iya barinka ne Malam?" "Matu'kar kina tare da su Halima, kina basu damar da suke cusa miki ra'ayinsu Ina tabbatar miki zasu raba ni da ke" ya fada cikin rawar murya. Kafin ta yi magana ya zarce da fadin "Ina miki son da zan sadaukar miki da komai, idan nace komai, ina nufin har rayuwa ta amma ke baki fahimci hakan ba" Ya sake ri'keta sosai, cikin wata murya irin ta karaya da lamari yace "Bana son kaifin harshe Sa'a, bana miki akan me zaki dinga mini? zan ro'ke ki! dan Allah fada mini inda na kuskure miki da ban cancanci ki zauna da ni lafiya da kyautatawa ba?" Ta yi shiru tana jin hawaye na cika mata idanuwa, haka kawai take jin tamkar wani abu na tashin hankali zai biyo baya. Jin shirunta sai ya zarce da fadin "ki bude baki, ki mini magana, ki fada min inda na gaza

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});