Chapter 97
Chapter 97
kina son magana da ni ki kira Ni a waya, Ni Kuma zan zo!amma wannan ya zama shine zuwan ki na karshe if not, zan fa'dawa Baffah". Da kuka sosai ta isa gida, ta wuce Inna, ta fa'da dakinta, ta kwanta tana rusar kuka mai tada hankali. Ada Inna ta 'kudiri aniyar duka zata mata, tunda ta fita bata sani ba, to kuwa zata nuna mata dan ta yi aure ta haihu ba ta fi karfin ta ba, bata wuce ta zaneta ba.😀 Amma ganin yadda ta shigo a kidime ga kuka tana yi na fitar hankali sai wanccan alwashin ya bi iska, ta ajiye lagwanin rishon da ta ke gyarawa, ta bita dakin. Ta shiga! ta zauna kusa da ita, ta sassauta murya ta ce "Iyah Ina son ki gane gaskiya, ki gane sunnar rayuwa, ba komai ne kake samunsa a lokacin da kake so ba, mata da yawa basu sami nasarar auren wanda suke so ba, amma sun yi ha'kuri da wanda 'kaddara ta za'ba musu, suna cigaba da rayuwar su tamkar basu da damuwa. Sa'banin ke da kin samu cikar burinki, sai dai *HALIN YAU* yasa kin tankwabar da dukkan daukakar da minjin ki ya miki, Ni na haife ki, ko Baffanki bai fini sonki ba Iyah". Wannan maganganun na Inna ya sake karyar da zuciyar Sa'a, ta kasa daina kuka. Yayin da Inna ta cigaba da cewa "Sai dai duk soyayyar da nake miki ba zan 'ki fadar gaskiya ba! Na tabbatar ke kika 'kullawa kanki wannan salalar tsiyar, ke Kika biyewa'kawar zuciya da shedanun 'kawaye suka jefa ki a kogin nadama, na shaida Muuutar mutum ne har da rabin mutum! Abin da nake so ki fahimta 'daya ne, A yanzu dai bae zai mayar da ke ba, na tabbatar da zai mayar da ke da sauri haka, da ya ha'diye abin da kika shuka masa ko dan mahaifin ki! Ki fuskanci rayuwar ki ta gaba, kin rayu a duniya shekaru goma sha shida zuwa Sha bakwai babu Muutar a cikinta, yanzu ma kuwa dole ki rayu babu shi, idan mutuwa yayi ai dole ki ha'kura bare yana raye, kuna sha'kar numfashi a duniya 'daya". Cikin rarrashi Inna ta sake cewa"Zan fa'da miki wani abu ki ri'ke shi da kyau, Wannan bibiyar da kike masa ita take sake sawa Yana nesanta da ke, kin yi laifi, kin bashi ha'kuri tamkar yawun baki zai 'kafe, kin yi nadama, nadama ta gaskiya, to ki barwa Allah lamarinki ya miki za'bi, zabin Allah kuwa gaba yake da son ranmu, idan Kika ha'kura kika yarda da kaddarar da ta afkoiki, kika gamsu idan kin samu wata damar baza ki sake maimata kuskuren ki na baya ba, kika gane darasin da rayuwa ta koya miki, ina tabbatar miki Allah ba zai barki haka ba, ko dai ya dawo miki da Muutar da kansa ta yadda zaki fi 'kima da daraja, ko kuma ya baki wani mafi alherin". Da sauri ta fada jkin Inna tana cewa "na gode Inna dan Allah ki dinga mini addua, ki mini adduar dangana ji nake zan mutu, Ina cikin kunci da ba'kin ciki mai yawa". A tausashe Inna ta ce kin bar Allah ne, shiyasa ya bar ki, ki yawaita addu'a, ki lazimci istigifari, duk tsaurin damuwa istigifari na wanketa. ki daure zuciyarki,ki daina rokon Muutar akan ya zauna da ke a dole, fadawa Allah damuwar ki yana jin ki". Da kuka sosai ta ce " To Inna". sai kuma ta dinga fadin Astagafirillah da karfin gaske hadi da salatin Annabi. "A hankali za ki yi Iyah, ko a zuci kike yi Ubangijinki ya ji ki" Bata daina ba, haka bata rage ba, ganin da Inna ta yi tamkar ba a cikin hayyacinta take ba yasa ta fita ta 'kyaleta, tun tana jinta har ta daina ji, ta leka ta ga barci ne ya mata shigar sauri, a fili Inna ta ce Allah ka dawo wa da yarinyar nan nutsuwar ta, Allah ka tausaya mata". Kwana biyu kullum Inna ke tausarta, hakan kuma ya taimaka gurin rage kaso mai yawa na damuwar ta, dama kuma ganin da Farida ta mata, tana tsugunne gaban Mk ne ya susuta ta, sannan ta sa a ranta soyayya yake da ita. A 'ko'karin Inna na son ta 'kara nesanta Iyah daga tunanin Mk yasa ta roki Baffa akan ya barta ta tafi Gombe ta yi ko wata 'daya ne, ko hankalin ta ya 'dan kwanta idan tana tare da yar'uwarta. Ai kuwa Baffa na bude baki yace "Eh ita ta'ki zaman aure sai kuma taje ta zauna gidan SUMAYYA, arasa gane wacece matar gidan a tsakanin su, wata'kila kuma idan ba sa'a aka yi ba, ta koyawa Sumayyan iyashege tunda tana ganin ita wayayyiya ce kuma me ilimi ce, sa'banin Sumayya da tasa Allah da Ma'aiki a gabanta! Ba inda za ta je nan ne dolenta, ba gidan Sumayya ba". Da 'kyar Sumayya ta roki Baffah ya amince Iyah ta je Gombe amma da sharadin sati biyu zata yi. Zuwan ta Gombe ya sake sa mata hakurin rashin Jawad da Babansa, duk da dai kullum dare sai ta ji'ka filonta da hawayen takaici da kewa mai yawa. Daga sati biyu sai da ta shafe wata uku a Gombe, wadda yayi dai-dai da wattanni bakwai da mutuwar aurenta. Ranar wata lahadi Mk da Mahmoud suka je wurin Baffa, suka gabatar masa da takardar admission din da Mk ya samowa Sa'adah A Aminu Kano college of legal studies (LEGAL KANO). Inda zata yi diploma a fannin Sharia tsawon shekaru biyu. Kai tsaye Baffah ya ce "Mutari ba zai yiwu ba, ka sani tun tana 'karamarta ban barta ta tafi babbar makaranta ba, aurar da ita na yi, sannan kaima tsawon shekaru bakwai ba ka'dan da ta yi a hannun ka, ba ka sata a makaranta ba sai yanzu?" Ya girgiza kansa alamun bai amince ba. Mk ya yi kasa da kai ya ce "Allah shine shaida tuntuni na so ta fara, to makarantar da take so bata samu ba, sai na mata sha'awar F.C.E KANO. Ashe mun makara sai muka bari sai bana, to ga yadda banan ta zo mana ba yadda muke zato ba. Dan Allah Baffah ka mini wannan alfarmar, ka barta taje ta yi ilimi ai yanzu ta yi hankali ba kamar da bane da kake jin tsoro". "Mutari ka bar wannan maganar dan kuwa bata shiga kunne ba, ba kuma zata shiga ba". Sai lokacin Mahmoud ya ce " Hakuri zaka yi Baffah! Idan ka gamsu da gaske Mukhtar bai rabu da Sa'a da nufin tozarci ba, to ka bashi dama ta shiga makarantar nan, yadda ya dauke ka, wallahi ko aure bai gitta a tsakanin su ba, shi me yin alheri ne ga ahalinka. Sosai su Mk suka matsawa Baffa da roko har suka shawo kansa ya amince, zata yi karatun amma da zarar mijin da ya cacanta ya fito neman aurenta to zai katse karatun, domin kuwa yafi bu'katar auren akan karatun. Jikin Mk ya yi sanyi tubus adalilin kalaman Baffah, na farko da Baffa yace ya fi bu'katar auren sai ya ji tamkar gugar zana ya masa, sai kuma kishin da ya ce idan ta sami miji zai yi aurenta. A satin ta dawo kasancewar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157