Chapter 71
Chapter 71
suke yi. Kullum mitar ya siya mata waya take, rannan da ya gaji, ya zaunar da ita yace "kinsan za ki dame ni mai yasa za ki sani karban filaye biyu? bani da kudin siya miki wayar da kike magana akanta, Ni kaina ban ri'ke ta ba". Ai kuwa zamansu ya dawo wani iri, saboda ta kudire a ranta da gaske yanmatan banzan yake yiwa hidima, ita ya barta ko oho, mussaman da ya ki yarda ya kaita ta ga filayen nasa. Ranar wata juma'ah sai ga shi da sabuwar plasma TV 32 inch, ga mamakinsa ba ta yi wani murna ba, lamarin da ya bata ransa sosai. Haka ya daure, ya kira mai gyara ya hada mata har da satellite. Kallonta kawai yake yi, a zatonsa siyan tv zaisa zamansu ya dawo normal, amma sai ya ga sabanin haka, saboda ta riga ta yi nisa a son Black berry, ta samu shedanun kawaye na mata famfo. Haka suke ta gungurawa, yau fari gobe tsumma, mussaman da ya tsaya akan ra'ayinsa na ba zai siyi waya ta makudan kudade ba. haka jarrabawar jamb ta fito, a lokacin da F.C.E. ta fidda jerin daliban da suka sami gurbin karatu har da ita, inda zata karanta primary care education jiran lokacin fara daukan darasi take yi nan da yan wattanni. Hakan bai sa ta sauko ba, saboda ita B.U.K. take so, Safina sai cewa take "mijinki is very smart Ya rantse ba zai kai ki makarantar da yake ba, dan kar agane yana da mata". Yau da gobe akace ta fi karfin wasa, ya gaji da zaman rashin walwalarsu, ya kukuta ya siyo musu Android shi da ita, a lokacin bata jima da fitowa ba, dan haka itama mai tsada ce, ga mamakinsa ko Na gode ta gagareta fa'da wadda ko kadan ba halayyar ta bace, ko abu bai yi mata ba zata yi godiya ko a gajarce ne. Amma wannan ajiyewa ta yi a inda ya bata ba tare da ta duba ba, ransa ya baci da ita, irin wadda bai taba ji ba. Ganin idan ya cigaba da zama kusa da ita, komai na iya faruwa a tsakaninsu na rashin jin dadi, yasa ya mike ya fita zuwa shagon sa, bai dawo ba, sai shadaya da ashirin da bakwai 11:27pm. Ya sake tarar da wani 'bacin rai fiye da na farko, wato rufe masa gida, bugu ka'dan ya yi, ya hakura dan kar makwabta su fahimci abin da ke faruwa, ya dinga kiran wayarta ba kakkautawa, tana shiga amma taki dauka, karshe ma sai ta kashe wayar gaba'daya. Haka ya kwana a gate a cikin mota, ya yi kwanan zafi, da sauro, barcin kansa rabi rabi ne, wannan daren yana cikin jerin dare masu tsayi da ya fuskanta a rayuwar sa. Duk juyin da zai yi, tunanin irin hukuncin da zai mata yake yi, ya gaji da wannan bala'in, zai nuna mata, neman zaman lafiya ba shine lasisin da zata dinga wulakanta shi ba. Koda asuba kin bude masa ta yi, dan iskanci kuma ta kunna wayar amma taki 'dagawa. Ya Mata text yafi sau goma, har kurarin zai fadawa Baffa ya yi, amma ko gezau. Har taran safiya, yana harabar gidan. Takaicin sa daya, ba ya ajiye kaya a mota. Mahmoud ya kira ya fada masa halin da yake ciki. Da kyar Mahmoud ya shawo kanta ta bude masa, domin kuwa cewa ta yi, ya koma ya dauwama a gurin Farida. Yana jin lokacin da ta zare sakata, amma ba'kin ciki ya hana shi tashi, ya jima yana addu'ar samun sau'kin zuciya kafin ya samu sassauci. ya shiga gidan kai tsaye dakinsa ya shiga, ya yi wanka, ya fito ya shiga kicin, ya hadawa kansa Abu mai sauki, ya koma dakinsa ya rufe, yini guda bai fita ba, domin ramuwar barcin da bai samu ya yi ba. Itakuma tana zaune cikin shirin ko ta kwana, har sun yi waya da Halima ta fada mata abin da ta yi masa jiya, tace mata da kyau, gobe idan ya sake har gate din za ki rufe. Sai azahar ya tashi, ya fito da shirin fita masallaci, Jawad ya biyo shi, ya ri'ke hannun sa, suka tafi bayan ya masa alwala, suna dawowa, Jawad ya dinga Jan hannunsa, Yana cewa" Mami falo". Ya daka masa tsawa ya shige dakinsa ya daga murya yace "je ka wurinta kai, domin ita da babu duk daya ne a gurina" Jawad ya fashe da kuka saboda tsawar da bai saba da ita ba. Abin ya yiwa Sa'adah ciwo, a fili tace "Allah yasa yau ka sake yin dare, zaka san Ni da babu daya muke". Tsawon kwanaki biyu, zaman nasu ya sake yin tsami, domin shima fishi ya dauka sosai, ya dauke sabuwar wayar da ta bar masa a gurin, sannan ya karbe wadda take amfani da ita. Lamarin da yasa rikicin ya sake ta'azzara a tsakanin su. Ta dayan bangaren kuma sai shirin tafiya Abuja yake yi, saboda za su yi wata jarrabawar scholarship da gwamnatin tarayya zata tura malaman jami'oi karo ilimi a kasashen Birtaniya, Canada da kuma Rasha. Bai fada mata zai yi tafiya ba, har sai da ya kammala shirinsa, da zai tafi, ya tsaya daga bakin kofar falon yace " Zan yi tafiya, sai Allah ya dawo da Ni, ya bawa Jawad dubu uku yace "kai mata". Mamaki yasa ta kasa bude baki ta yi magana, ya juya ya tafi, Jawad na kukan zai bishi. A tunanin ta kwana daya zai yi ko biyu, amma sai da ya shafe kwanaki biyar ba shi ba alamun sa, a kwana na shida ne, idonta ya fara raina fata, mussaman da ta tabbatar da Mahmoud suka yi tafiyar, Amma shi ya dawo kwana biyu kawai ya yi. Kuka ta dinga yi, tamkar shine mafita, ga rashin waya dake addabar ta, ga rashin sa. Sai da yayi sati guda ya dawo, kallo daya ya mata yasan ta ji jiki, sakonsa ya daketa sosai, amma saboda Halinta na taurin rai, ko kallo bai isheta ba. Washagari da ya fita, sai da ya kai 11pm kafin ya dawo, domin ya jarrabata ya gani. A bangaren ta tana son rufe masa gida amma ta kasa, kwanakin da ya yi baya gida, sune mafi tsauri a dukkan rayuwar ta, tunda suka yi aure bai ta'ba yin tafiyar da ya kwana ba tare da ita ba. tasan rufe masa gidan da ta yi ne, yasa yayi tafiya mai tsayi ba tare da ita ba, ba magana mai dadi, ko na zai yi missing dinta. Ya dawo ya tarar da gida a bude, ya yi murmushi, yauma 'dakinsa ya zarce, wannan abin ya dameta, amma bata ji zata bashi ha'kuri ba, tunda ai ita ya zalunta. Washagari yana shirin fita, ta fito ta tsaya a tsakar gida, sai da ya fito sannan tace " Ina son zanje gida". Ba tare da ya kalleta ba, yace " Ba za ki je ba". Ya sa kai zai fita, taja tsakin da yasa shi juyowa da sauri, kafin yayi magana tace "dama idan mutum na cin amanar matarsa, sai ya yi ta boyeta a cikin gida, mai za'a yi da auren likitan mata, da mai koyarwa a Jami'a, aiki ne na yan iskan maza,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157