Chapter 44
Chapter 44
kama Sa'adah ta na jin ita ta janyo wa kanta rashin yarda a idon iyayenta. Tana karbo sakon ta juyo, duk da yadda Anty Walida ta yi nacin ta zauna ta karasa yi mata yinin, ita kuma ganin biyu da rabi ta yi yasa ta gaggauta fitowa dan ta zartar da kudirinta na son ganin Mk a yau. Kai tsaye FGC Kano ta sauka, sai dai ba makarantar ta shiga ba, gangare can gefe ta tsaya inda suka ta'ba tsayawa da shi, ta san kullum ta nan ya ke bi. Cikin sa'a kuwa ba ta dade tana jira ba ta hango shi, yana doso inda take, a kafa yake tafiya. Ta ce, "Ko ina ya baro dan mashin 'din?" Sanye ya ke cikin 'kananun kaya yana rataye da jakar da yake zuba takardun shi, ya mata kyau sosai duk da ta ga ya dan zube kadan. Sai da ya wuce ta sannan ta bi bayansa, jin ana ta bin bayansa yasa shi jiyowa, ba zato idanunsu suka sarke, ya hade girar sama da ta kasa tamkar bai ta'ba dariya ba, ya juya ya ci gaba da tafiyarsa tamkar bai gan ta ba. Sai lokacin ta yi magana "Uncle na yi kewar ka, idona sun yi kukan rashin ka!" Ya ji ta sarai, bacin ransa ya dawo sabo, ya rasa wane matakin zai ajiye Sa'adah, duk inda ya ke ajiye ta, yau ya tabbatar masa ta kere gurin!har ta san ta bi saurayi gun aikinsa? Ita kuma ganin bai kula ta ba har sun fara hango titi sai ta fara masa kukan da babu hawaye tana kuma fadin "Zuciyata ba za ta iya daukar fishinka ba, ka kalle ni ka ga yadda fishinka ya ramar da ni, ba na iya barci, ba na iya cin abinci, kamin afuwa, don Allah ba don halina ba!" Ta fada cikin wani irin yanayi mai motsa ZUCIYA. Ya juyo ya zuba mata ido tabbas ta rame, ta birkice amma hakan bai yi tasiri a zuciyarsa ba, musamman da ya tuno kallon rainin da Khalil ya yi masa, ya sake hango yadda ta fito a gaban motarsa, sai kawai ya juya ya ci gaba da tafiyarsa ba tare da ya ce mata uffan ba. A kidime ta ru'ko hannun jakarsa murya na rawa ta ce, "Na san na yi ba daidai ba, na ba ka ha'kuri, ka yi hakuri mana!" Bacin rai sosai a fuskarsa ya dube ta sannan ya ce, "Ke ba na son ballagazanci, a titi za ki ri'ke ni?" Ba'kin ciki ya kama ta ta fara kukan gaske ta ce, "Ni ka kira da ballagaza?" Kishi ya rufe mai ido sosai, ba wani ja-in-ja ya ce, "E, idan akwai sunan da ya fi haka muni ma ki hada da ballagazar, don kuwa sunayenki ne, dabi'un da kike yi irin nasu ne. Yanzu kuma kin nuna mini kin saba cu'danya sosai da maza, har kike ganin za ki iya cakuma ta a titi." Ba'kin ciki ya turnuke ta, ba a taba yi mata tozarci a rayuwarta irin na yau ba, kuka sosai take yi wanda ya matu'kar taba shi, kawai waskewa ya yi. ba tare da ta sake fadin komai ba, ta yi gaba da sauri ba ta ko sanin inda take jefa kafarta saboda tsananin 'bacin rai. Al'kalamin *Surayya Dee* ✍🏼✍🏼✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *A guji taba ko sarrafa labarin nan ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *TALLAH*. _Akwai ingantaccan maganin🌴🌴 gyaran nono na hausa, ga wanda yake da bukatar maganin zai iya tuntubar wannan number...... 08089965176 domin karin bayani, maganin ya samu lambar yabo saboda ingancinsa, yana amfani sosai domin yana ciko da nono yana kuma sanya k'iba dai misali, babu almundahana babu cuta babu cutarwa sahihin magani ne, idan kin shayar sau goma, ina mai tabbatar miki da cewa daga ranar da ki ka fara amfani da maganin zaki ga sauyi, domin yana gyara mace, zawarawa da 'yan mata kuma kada a barku a baya za ku iya mallakar naku maganin domin in ganta kanki, bahaushe yace idan kana da kyau ka kara da wanka!...ga masu bukatar sari ko sayan d'aya muna KANO muna turawa kowane gari 2k kacal zaki mallaki naki kafin ya kare wallahi sai kin ga sauyi.......*SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA*! Idan matsalar nono kike fama da ita kukanki ya 'kare da ikon Allah._ 47-48 A gigice ya ga ta nufi titi gadan-gadan tamkar zararriya, zuciyarsa ta buga, da azama ya bi ta ganin da gaske tsallakawa za ta yi ba tare da ta duba ba. A ki'dime ya fuzgo ta, ganin mota na shirin yin wasan-kura da ita, amsa-kuwwar motoci sun cika gun, har sai da mai motar ya tsaya ya fito ya dinga zazzaga mata sababi, yayin da ita ko kallo bai ishe ta ba illa fizgewa da ta yi daga ri'kon da MK ya yi mata, ta koma gefe tana hawayen ba'kin cikin maganganun da ya gasa mata. Sai da ya ba wa mai motar hakuri ya tafi sannan ya tsayar mata da Adaidaita Sahu, juyin duniya ta ki hawa, har mai Adaidaitan ya ji haushi ya yi tafiyar sa. Ya kalle ta ya ce, "Watau da ma zuwa kika yi ki sake tayar mini da hankali ko?" Yana rufe baki ta ce "Kadai so hankalin naka ya tashi ne, ha'kuri na zo ba ka, ka ki ha'kura. Ka bi ni da kalaman muzanci, to ai sai ka yi tafiyarka tunda da ma ba kai ka kawo ni ba balle ka ce sai kasa na koma dole." Ya kalle ta ya ga tana cikin fishi irin wanda bai taba ganin ta yi irinsa ba, sai ya sassauta ya ce, "Na ji ba ni na kawo ki ba, amma kin ce gurina kika zo, idan kuwa haka ne to ba na son zuwan. Ki koma gida ni zan zo." Kamar ta ce "Ba na son zuwan naka ni ma!" Sai ta daure ta kalle shi ta ce, "Nasan ba da gaske ka ke ba." "Zan zo mana da gaske nake." Ta yi shiru tana rantsuwa a ranta ba za ta yarda da maganganun da ya yi mata ba. Dolensa sai ya janye ko ya ga tashin hankalin da ya ke kirari. Ya kalle ta ya ga ta turo bakin nan gaba, mamakin yadda ta ke son mayar da laifin da ta masa ya koma kansa ya ke yi. "Kin yarda na tsayar miki da abin hawa?" Shiru ta yi masa alamun ba ta yarda ba. Ya kalle ta ya ce, "Magana nake miki." A gajarce ta ce "Ban yarda ba!Yawon ballagazan ci zan wuce." Ji ya yi kamar ta wasta masa ruwan dalma a zuciyarsa, ya hassalo sosai ya nuna ta da yatsa ya ce, "Ni kike yi wa magana kamar kina yi da sa'anki? Saboda ba kya ganin girma da mutuncina?" Ta yi mai shiru ta kasa cewa komai. Ya sake cewa "Ki dinga sanin
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157