Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

'Karfi. "Ka shirya gobe muje mu same ta, kada Hajiya ta tambaya ta ji ba ka fara kafa tubalin kome ba ta yi fishi" Ya 'karasa maganar cikin zolaya. "Hmmm!" Kawai MK ya yi tare da cewa "Na gode sosai sai mun hadu gobe idan Allah yaso" * Sa'adah tana shiga a dakin mahaifiyarta ta ci burki, "Inna na dawo" "Zo ki zauna magana zamu yi" Ba ta musa ba ta shiga ta zauna daf da ita,"Waye ya zo?" "Ba wani daban ba ne Baban Dadi ne" Tabe baki ta yi tare da cewa "Waye hakan, kar ki ce mini Mahmoud abokin Muutar? Cikin shagwaba ta rungumo uwar tata ta ce "Shi fa mene ne Inna?" Ture ta ta yi tana cewa "Ashe baki daina bibiyar yaron nan ba ko? 'dazu amsar da ki ka bani na komai ya kusan 'karewa akan maganar aure, ashe kina nan kina zawarcin Muutar ne? Wannan shi ne al'kawarin da ki ka mini? Tunda kin zabi son ranki sama da nawa to ki je ki ta yi, amma ki sani ba da yawuna ba, ba kuma da son raina ba, sai don kin fi 'karfina, don kin san zaki samu goyon bayan mahaifin ki ne" Ta nisa sannan ta ci gaba da cewa, "Tunda na ga kina ta hanzarin shiryawa tare da 'doki na tabbatar ba kowa kike wa wannan rawan jikin ba sai shi" "Inna ba fa yadda kike zaton lamarin ba ne wallahi ban karya al'kawarinmu ba, amma don Allah ki yi hakuri ki gafarce ni ba na son kina damun kan ki akan wannan maganar" "Ai dole na damu tunda na gane ke da Baffanku, ba ku da burin da ya wuce ki koma gidan Muutar, ni kadai na san ba'kin ciki da wahalar da na sha kafin na samo ki a dalilinsa. kuma yanzu da komai ya wuce sai ya lallabo ya sake dama miki lissafi, saboda ya mai da ke marar zuciya, wacce ba ta san ciwon kanta ba" Cike da tausasa murya Sa'adah ta ce, "In sha Allah Inna ba zan sake shiga halin da kike jin tsoro ba, ni ma nasan abin da kike guje mini, tuni na cire shi a raina." "To idan dai haka ne ki ba wa Alh Mamman ko yaron nan Anwar dama wani cikinsu ya fito, ki yi aurenki idan ba haka ba, hankalina ba zai kwanta ba." Ta fada tana goge hawaye da hannun zaninta. Jikin Sa'adah ya yi sanyi ashe dai da gaske Inna take akan ba za ta koma wa Malam ba? Ashe haka ta zafafa lamarin? Wannan wacce irin ba'kar 'kaddara ce ke bibiyar ta ne? Bayan doguwar wahalar da ta sha akan komawarta 'dakinta, sai da abu ya zo a lokacin da ba ta yi tsammanin zuwansa ba, kuma mahaifiyarta ta yi bara'a da lamarin, hankalinta idan ya kai dubu to ya tashi. *_Wai mene ne ke faruwa a tsakanin ma'auran biyu? Mene ne ainihin labarinsu? Mene ne ya raba su duk da matsananciyar soyayyar da ke tsakaninsu? Mu je ga mafari don jin wacce irin waina suka toya?_* Al'kalamin SURAYYA DAHIRU ✍🏼✍🏼 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. 19-20. *MAFARI* Malam Basiru Ado Gogel, haifaffen garin Gogel ne, wani gari a 'karamar hukumar Warawa. Karatun Allo ne ya kawo shi cikin garin Kano, ya sa himma har Allah ya taimake shi, ya haddace al'kur'ani, sannu a hankali kuma ya fara sana'ar tura kura a kasuwar Singa Da damina zai tafi gida yayi aikin gona gadan-gadan kasancewar al'ummar garin Gogel manoma ne, duk da ya ta so ba uba, domin ya na da 'karancin shekaru mahaifinsa ya rasu, dan haka ya yi birgimar ta shi fa'din rayuwa a tsakanin mahaifiyarshi da 'yan uwan mahaifinsa. Da haka ya hada jarin sa ya bude 'yar tireda a cikin unguwar da ya ke hayar 'daki, a unguwa uku, a shekarar kuma aka masa aure da Salamatu 'diyar 'kanin mahaifiyarsa wadda asalin mahaifiyar ta shi 'Yar asalin gamawa ce ta jahar Bauchin Yakubu, aure da rabon haihuwar sa ne ya kawo ta Gogel, kenan Salamatu ma, da ga Gamawa aka ba shi ita. Ya taho da ita cikin kano, suna zaune lafiya, cikin rufin asiri. Yarinyar su ta farko da suka haifa bayan shekaru uku da aure, sunan ta Sumayya, ba sunan kowa taci ba, illa sunan Nana Sumayya, macen farko da ta yi shahada a musulunci. tare da fatan yarinyar ta sami albarkacin mai sunan. Haka sukaci gaba da rayuwar su cikin rufin asirin Allah, dukkansu sun da ce da juna, masu ha'kuri ne, masu kuma wadatar zuci ne. Sai da Sumayya ta yi shekaru takwas sannan aka haifi Sa'adah wadda sunan mahaifiyarsa ta ci (Sa'adatu). Daga shi har Innar su Salamatu su ke kiran ta Iyah, kamar yadda ake kiran mai sunan nata. A shekarar kuma mahaifiyarshi ta rasu, shi yasa ya tattara ko mai da ya ke dashi a Gogel ya siyar illah gona 'daya da ya bari, wadda zai dinga noma wa, sai kuma 'dakin mahaifiyarsa da yake cikin gidansu ya rufe shi saboda idan ya je Yana da gurin zama. ya zo kano ya si yi madaidai cin gida anan cikin unguwar gidan akan titine a kuma babban layin na Unguwa Uku. Haka rayuwar su ta ci gaba da tafiya cikin ha'kuri da godiyar Allah, har Sumayya ta kammala 'Karamar sakandire manema suka mata ca kasancewar ta doguwar mace fara sol irin fulanin Gamawa. Idris shi yafi kwanciya a ran Malam Basiru dan haka ya ce ya bashi, ba kuma ya bu'katar komai a gunsa sai sadaki da musulunci ya wajabta, komai zai ma ta idan ta je gidan shi sai ya yi. Wannan karamcin da iyayen Idris suka ga ni ya faranta ransu ba ka'dan ba, suka girmama lamarin Sumayya da iyayen ta, kullum cikin jan kunnen shi su ke, akan ya ri'keta cikin aminci. Haka aka yi auranta ba wani hidima, ya 'dauke ta zuwa ogshobo ta jihar osun inda yake aiki da babban bankin Nigeria (CBN) reshen jahar osun. Dan haka Sa'adatu ita kadai ta taso a gidansu domin kuwa, ba ta wuce shekaru takwas ba, aka aurar da yayarta kasancewar mahaifinsu bai wani damu da karatun boko ba, muhimmi dai a gunshi a haddace alkur'ani. Tun kuma akanta basu sake samun haihuwa ba, shi yasa sha'kuwa mai yawa ce tsakanin ta da iyayenta biyu har tana rasa gane waye yafi sonta a cikin su. Yau da gobe aka ce ba ta bar komai ba, Iyah ta kammala 'karamar sakandire, amma ganin yadda ta k'wallafa rai a boko da kuma yadda ba ta sauraren ko wanne saurayi yasa Malam Basiru barin ta ta tafi babbar sakandire, kamar wasa aka zabe su, su biyar a makarantar su, ta GGC U/Uku, su rubuta jarrabawar shiga sakandire ta gwamnatin tarayya ta Kano (FGC KANO). jarrabawar na fitowa kuwa sunanta ya fito cikin mutum uku da suka yi nasara, ita kanta ta yi mamaki tunda duk ragowan da suka fa'di sun fita 'ko'kari. Ganin ku'di tsululu da za'a kashe a hidimar makarantar Malam Basiru

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});