Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 60

Chapter 60

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da zarar mace ta haihu sai namiji ya canja mata, ita kam ba ta ci karo da wannan matsalar ba, ta dinga tunanin ko don ta sami kyakkawan gyara ne a wurin Innarta da Sumayya, ko kuma dabi'ar wasu mazan ce haka? Lafiya Lau suke zaune, har yanzu a cikin marararinta yake tamkar amarya, hakan ba karamin faranta ranta ya ke ba. Ya wadata su da komai daidai gwargwado, sannan da ya fahimci, ta fishi saurin fishi, sai ya ke kaffa-kaffa da abin da zai bakanta ranta, shi yasa zamansu lafiya, sai yan kananun sabani na yau da kullum da ba za a iya kauce masa ba. Kuma ba sa bari fishinsu ya wuce na yini daya. Watan Jawad uku, Sa'adah ta kasa gane kanta, yau zazzabi, gobe mura, jibi jiri, kullum da abin da za ta tashi da shi. Zazzabin hakori da rashin kuzarin Sa'adah, sai suka yi wa Jawad rubdugu, duk sun yi laushi. Ganin yadda suke yamushewa ya sa MK ya kai su asibiti, gwajin farko ya nuna ciki ne a jikinta, na tsawon sati hudu. Dankari! tun a asibitin take kuka, bakin ciki ya turnuke ta, da danyen goyo za ta sami wani cikin? kuka take yi sosai tana fadin sai dai a san yadda za'a yi, amma ita ba ta shirya sake haihuwa yanzu ba. Tun MK na rarrashin ta bari suje gida, har ya gaji ya kama bakinsa ya zuba mata ido. Suna shiga gidan ko zama ba ta bari sun yi ba, ta ce "To mun zo gidan fada mini yadda za'a yi". Ya kalle ta da tausayawa ya ce "Zauna ki nutsu, ki huta sai mu yi maganar, ba inda zani yau, ina tare da ke". Ba tavce komai ba, ta zauna tana huci, tana jin duniyar ta mata kunci. Shi kuma ya shige cikin daki ya shimfide Jawad da ya yi barci. Yana fitowa kicin ya wuce, ya zauna ya dafa musu indomie, ya juye a plate, ya kai gabanta ya ajiye, ya koma ya hado tea Sai da ya zauna sannan ya kalle ta ya ce, "Bismillah sauko mu ci." Hawaye na bin fuskarta ta girgiza kai tare da fadin "Na koshi". Ya kafe ta da ido, ya nisa ya ce "Me kika ci?" Ta kasa ba shi amsa, tunda dai ba su karya ba, suka yi sammakon fita. Ya sake kallon ta, sai goge hawaye take yi, har ransa shi ma bai so samuwar cikin nan a yanzu ba, amma tunda ya riga ya shiga, to ba zai ba ta kofar da za ta yi abin da take so ba. "Idan har na gama cin abincin nan ba ki ci ba, fita zan yi, ba zan yi maganar da zamu yi a yau ba kuma". Kan dole ta wanko hannu, ta fara ci, turawa kawai take yi, saboda gabadaya ba ta jin dadi, ga kuma bakin ciki da ya cika mata zuciya. Sai da ya hada mata tea, ta sha, ya ba ta magani, ya dauke plate da cups din ya kai kicin ya dawo! ya zauna kusa da ita sosai. Ya sassauta murya cikin lallashi ya ce, "Fada mini matsalar ki akan cikin nan, da kike ta wannan koke-koke da bacin rai". Cikin kukan ta ce "Har sai na furta matsala, sannan za ka fahimci matsalolin da suka dabaibaye ni?" "E fada mini mana wata'kila sai na fahimta a yanzu". Ta goge fuskarta da ta yi kozai-kozai, sannan ta ce "Ba ka ga Jawad har yanzu jariri ba ne? sannan wannan cikin ba irin waccan ba ne, yau kusan sati uku ban da cikakkiyar lafiya". Ta yi shiru tana jan hanci. Sai da ya ji shirun ya yi yawa sai ya ce "shike nan matsalolin?" "Ba shike nan ba, yanzu fa wannan lalacewar da Jawad ya fara yi, yana ta tsinkewa, cikin da yake sha ne, kuma bai isa yaye ba". Da azama ya ce "Duk na fahimce ki Sa'adah, har zuciyata kuma tausayinku nake ji musamman Jawad, amma tunda Ubangiji ne ya ba mu ya za mu yi? Sai mu raini abin mu cikin farinciki da godiyar Allah". Kukanta ya dan kara yawa ta ce "Yaye Jawad din za'a yi ke nan?" "Wane irin yaye kuma ba dadin ji? Ai kin ji bayanin likita, ga magunguna nan ya rubuto muku, ba abin da zai same shi". Maganganunsa suka haska mata sai ta haifi cikin nan dole, don haka ta dage ta dinga zunduma masa ihun kuka da ya yi sanadin tashin Jawad a gigice, shi ma ya cika dakin da kuka. MK ya rasa wanda zai lallaba a cikinsu, dole ya wuce daki ya dauko yaron ya fara jijjiga shi. Sai da ya yi shiru sannan ya kalli Sa'adah da take kuka irin na mutuwar Jahiliyya ya ce "Wane irin abu ne haka kike yi?" Ba ta kula shi ba ta ci gaba da yin kukanta hannuwa aka. Kan dole ya zauna kusa da ita yana cewa "Ki ga fa yadda kika sa Jawad kuka, don Allah ki yi hakuri, ke baki san baiwa ce Ubangiji ya yi mana ba?" "Ni ba na so!" Ta fada da karfi. "Shike nan na ji ba kya so, ni Ina so". Ya fada da alamun ya ji haushin maganarta. "Karbe shi, ki ba shi ya sha". Banda kuka ba abin da take yi, ko kallon sa, ba ta yi ba bare ta karbi yaron. "Kin ji". Ta kalle shi cikin ido ta ce "Na yaye shi". Ganin yadda ta rikice neman tashin hankali take yi da gaske, ya ce "To ba shi ya sha yanzu, kafin a jima na siyo masa abin da zai dinga sha". Nan ma a zafafe ta ce "Ba zan bayar ba". Kyale ta ya yi, ya ajiye shi ya hado masa shayi mai dan dumi, ya dauko sabuwar feeder ya wanke ta da ruwan zafi, ya zuba shayin a ciki, sai ya zauna sannan ya dauke shi, ya fara ba shi, cikin ikon Allah ya shanye har da gyatsa. Ya hada ruwa ya masa wanka, ya shirya shi tsaf, yana ta yi masa wasa, shi kuma yana ta dariya har barci ya sake awon gaba da shi, bai kwantar da shi a dakin Sa'adah ba, ya fita ya kai shi dakinsa don kar kukan uwarsa ya sake farkar da shi, ya rage masa karfin fanka sannan ya fita zuwa wurin Sa'adah, da har yanzu take yin kuka. A kasan da take zaune, shi ma ya zauna ya ru'ko hannun ta, ya kira sunanta, ta ki amsawa, ya sake tausasa murya ya ce "Yi hakuri tashi muje na taimaka miki ki yi wanka, ki ji dadin jikin ki. Yi hakuri kin ji my sweetheart". Da kyar ya shawo kanta ta yi wanka, bayan ta ce ba ta son taimakon nasa. Mai kawai ta shafa ta zura doguwar riga cotton marar nauyi, ta kwanta, tana ta ajiyar zuciya ba jimawa barci ya wuce da ita. Kwanaki uku ban da tashin hankali ba abin da Sa'adah take yi gaba'daya ta burkice, ban da kuka ba ta komai, ko wanka ba taki yi, bare aje ga hidimar gida, Jawad kuwa da tashin hankali take bashi nono sau biyu a rana duk kukan da zai yi kuwa. MK ganin ba

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});