Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

don haka kar ki sa a ranki cewar za ta dawo, azo kuma abu bai yiwu ba, ki zo ki sake shiga damuwa kinsan dai kullum girma 'kara kama ki yake" Shiru ta yi can ta nisa, "Shin kai a wurinka magana ta wuce ta 'bacin rai ba tashin tashina?" Ya yi jim, yasan dole sai sun sake baje tashin hankalin da ya gitta a tsakaninsu, kafin a manta shi gaba'daya! Amma sai ya amsa mata da cewa "Babu Hajiya! amma wallahi bazan ta bin kanta ta amince ba, don na lura yanzu wani iya shege ta ke ji" Da sauri Hajiya ta 'daga mishi hannu,"Kai da'dina da kai ba ka fahimci yarinyar nan ba, kishi ne ke 'dawainiya da ita, ka duba mana kafin ka yi auren nan wanne irin bibiya ne ba ta maka ba? har kowa ya gane ita ce mai laifi a tsakaninku, duk da ba ku cewa kowa ga yadda abin yake ba". Ta yi 'kasa da murya, "Yanzu fa duk girman laifinta, kama ta hukuncin da yanzu kai ne mai laifi a tsakaninku tunda ka mata kishiya, abin da nake so da kai, kar ka yarda wani borinta yasa ka yi 'kasa a guiwa, ka lallaba ta ka'dan, ni kuma sai na lalla'ba mana ita da yawa" Dariya ya dinga yi,"Oh Hajiya saboda Allah ni da Sa'adah wa kika fi so?" "Ai kai ma kasan ita na fi so! nan kusa za a dade ba'a samu mai girmama uwar miji da 'yan uwanshi irin ta ba. Ina fa ji ina kuma ganin yadda she'danun yaran yau suke wa iyayen mazan su iyashege kala-kala, har sunaye suka la'kaba musu, wai uwar miji ce Ulcer, BP, ciwon kai, da sauran sunaye na tsiya, amma Sa'a bata a cikin wannan layin". Dariyar ya sake yi tare da cewa, "kun yi dace ne kawai ke da ita wasu laifin iyayen mijin ne ai, da basa 'dauke kai ga harkar gidan ya'yan su maza, sannan basa jan surukan nasu a jiki, basa kuma yi musu sassaci da uzziri. Wasu kuma tabbas laifin *Matan Yau* ne da suke ganin uwar miji tamkar wata 'yar katsalandan ga rayuwar su sai afara zaman Allah ya kawo maraba. Allah dai ya rufa asiri kawai, amma Hajiya ita Farida fa?" Da sauri ta ce, "Ita ma ba ta da laifi tana da irin nata alherin, amma..." Ya katse ta da cewa "Ba kamar Sa'a ba ko??" Dariya ta yi tana cewa "Yaushe zaka je gun nata?" "Zan je In sha Allah!" Jin yadda ya sau'ko ya kuma amince da maganar Sa'adah a karon farko tun bayan rabuwarsu, yasa bata matsa mishi da yawa ba, sai ta ce, "To ka mayar da hankali don Allah, a yi a gama komai cikin 'kan'kanin lokaci ku dai yanzu ba yara ba ne" Mi'kewa ya yi yana gyara sakun hularsa tare da cewa, "Ke da kika ce za ki lallaba mana ita, ai ni ba sai na yi komai ba." Cikin sauri ta furta, "Ai ko tilas kai ne mai magana a farko" Murmushi ya saki tare da yi mata sallama ya fita yana fadin, "Sa'a ta same ki sosai Hajiya" Gidansa ya nufa, a falo ya tarar da Farida cikin kwalliya ta burgewa tana zaman jiran shi, ta hau hidimar kawo mishi abinci, da abin sha, sai daya kammala, ta kwashe komai sannan ta dawo ta zauna tana tambayar Hajiya. ya amsa da cewa "Tana lafiya! ta ce a gaishe ki." Murmushi ta yi tare da fadin "Na gode!" Hannunta ya riko ya janyota sosai kusa dashi, "Ina son mu yi magana mai mihimmanci, ki nutsu ki ji me zance miki, ki kuma fahimce ni" Idanuwanta masu sheki ta zuba masa tana jin a jikinta abin da ta dade tana jiran ya tabbata ne yake neman faruwa a wannan karon, kai ta gyada tare da cewa, "Ina jin ka." Sai kuma ya kasa cewa komai tsawon lokaci, ita kuwa da ke ba mai gaggawa ba ce ba ta ce masa uffan ba. Har ya gaji ya nisa don kanshi sannan ya ce, "Ba sabuwar magana ba ce mun sha yin ta, sai dai ta yau 'din ta sha banban!" Nan ma cewa ta yi, "Ina sauraron ka!" Abin mamaki sai ya ji shakkar furta maganar yake. Cikin dauriya ya ce, "Maganar Sa'adah ce zan fara magana da ita, idan Ubangiji bai 'karar da zaman namu baki 'daya ba, zata dawo " Gabanta ya fadi duk da a kullum cikin tsammanin faruwar hakan take, amma sai da ta kadu matu'ka da gaske, amma da yake tana cikin jerin matan da Ubangiji ya ba su ha'kuri mai yawa da sanyin hali, da kuma ha'diye damuwa sai ta ce! "Ai da ma ka sha fada mini a kowanne lokaci idan 'kaddarar zamanku ba ta 'kare ba za ka dawo da matarka, ni kuma na sha fada maka cewa ba zan baka matsala ba hakane?" Ta tambaye shi, kai ya 'daga mata, "To a yau ma ina tabbatar maka baka da matsala da ni. amma zan ro'ke ka abu daya, na san kana son ta sosai, ni kuma ina son ka sosai, don Allah ka yi mini adalci" Wani abu ya ji ya tsirga mishi tun daga kanshi har zuwa 'kafarshi. Gaba'daya ya janyota jikinshi yana jin tausayin ta na tsirga mishi a zuci da gangar jikinsa gabadaya. Cikin murya marar amo ya ce, "Farida a tsayin zamana da ke kin san ina son Sa'adah amma abin mamaki ba ki san ina son ki ba?" Luf ta yi ba ta amsa ba, saboda yadda take kokawa da zuciyarta da numfashin ta. "Kai, kishi, bala'i!" Ta fa'da a zuciyarta, ban da haka abin da take da tabbacin zai faru ne, don yana neman faruwa kuma sai ya dame ta? kamar ba ita ce take ta mishi kau'din ya dawo da matarsa ba? Amma a yau da ya amsa, har ya zauna yana fa'da mata da bakinshi akan zai dawo ita sai ta ji kishin da ba ta yi tunanin zai taso mata ba, ya taso da wani irin 'karfi mai gigitarwa. Jin ta yi shiru yasa shi fadin, "Ban aure ki akan wani dalili ba sai don ina son ki, ina zaune da ke saboda ina son ki, ina kuma jin dadin zama dake, don haka ba wani abin dazai raba ni da ke matu'kar ba ke ce kika bijire mini ba. Ina son ki Farida irin son da zan iya sadaukar miki da komai, ba abu mai da'di a soyayya irin a so ka da kai da dukkan matsalarka, a mutuntunta ka, a kuma yarda ka isa koda kuwa a zahiri baka isan ba. Ba abin da baki mini na kyautatawa ba, ba kuma zan manta ba, kar ki yarda ki sa a ranki wai zan juya miki baya akan Sa'adah, kar ki ji a ranki na fi son ta akan ki, ni ban san wacce na fi so ba, wacce duk ta kiyaye mini 'bacin Raina, ta zauna da ni lafiya cikin aminci, ta yarda bazan musguna mata da gangan ba, ba shakka itace zata jagoranci zuciya ta. Idan kuma kina da matsala akan dawowarta fada mini zan iya fasawa, idan har hakan zai fi zama masalaha." Rungume shi ta

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});