Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 100

Chapter 100

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,197 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

muma nan kasar ai ana bu'katar irin ku" Hajiya keta wannan fa'dan yayin da Mk ya yi shiru, ita kuma so take ya mayar da matarsa ko sati guda suyi tare sai ya yi tafiyar sa tunda ba zai yiwu ta bar karatunta ba. Amma tana fara maganar ya hade fuska iya fuska, jikinta yayi sanyi, daga karshe ma sai ga Alh Isa ya zo mata da maganar ai ya samu yarinyar da zai aura, za'a daura auren kafin ya tafi, daga baya zata bishi idan Jawad ya samu visa. Girman Alh Isa ya hana Hajiya cewa komai saboda kawaicin kar ta nuna masa iyaka akan Dan amininsa, wadda tunda maigidan nasu ya kwanta dama , Alh Isa Bai taba juya musu baya ba, yana tsaye akan almarinsu dana 'yayansu. Ba'kin ciki a zuciyar Hajiya tamkar ta fashe kan dole Alh Isa ya hakurkurtar da ita tare da nuna mata aure kaddara da rabo ne, shi kansa Mukhtar din har ya dira a kasar bai san zai yi aure ba. Al'amarin ya faru ne, da ya samu labarin rashin lafiyar Farida a bakin aminyar ta Rukayya Mustapha. Bai yi kasa a guiwa ba ya je asibitjn data ke kwance da niyyan dubata, ai kuwa mahaifin ta yana asbitin suka gaisa, Farida ta gabatar da shi tare da cewa "Dadi yau ga Uncle Mukhtar a gabanka". Ai kuwa budar bakin Dadi sai cewa yayi "madallah da Mukhtar ganin ka yau na ji ka shiga Raina Kamar yadda ka shiga ka kwanta a zuciyar 'diyata, na gode da alherin ka, ka turo mini waliyyan ka, na baka auren Farida ba tare da neman komai daga gurinka ba". Daga Farida har Mk abin ya zo musu tamkar saukar aradu, barin Mk da yaji tamkar mummunar kaddarace ta kawo shi asibitin, ba dan ba ya son Farida ba, sai don bai shirya aure a yanzu ba, bai shirya aurenta ba, a yanzu da ya gama sanin kansa ya fahimci mata masu duhu sunfi burge shi fiye da farare 'Kal, yana jin tsoron kar ya kasa yi mata adalci, tunda yasan ba karamin so take masa ba. Cikin hikima irin ta manya Alh Nasir ya tisa Mk a gaba ya bashi lambar Alh Isa a matsayin Babansa dan su Baba umaru sama sama suke da shi adalilin sakin da ya yiwa Sa'a sun kuma lashi takobin matu'kar ba Sa'a zai dawo da ita ba, ba za su sake neman masa aure ya kunya ta su ba. Cikin cire girman kai mahaifin Farida ya gaisa da Alh Isa ya zarce da cewa "yaron ka na bawa matar aure amma na ga tsoron tunkarar ku da maganar ya ke yi, shiyasa Ni na gabatar maka da maganar, na fada maka cewar nutsuwar danka ta sa na bashi kyautar 'yata mafi soyuwa da fatan zaka karbar masa". Matu'kar mutum yasan daddako wa za'a yiwa haka ya ce ba zai karba ba? Jikin Alh Isa ya mutu ya ce "kyuatar dan mutum ba mahalu'kin da za'a bawa ya tankwabar mun gode zan zo in sha Allah da kaina zan zo na karbar masa na kuma yi godiya. Washagari Alh Isa da Mk suka tarar da Baffan Sa'a suka masa bayanin Halin da ake ciki, idan ya ce bai ji rashin da'di ba ya yi 'karya, idan ya ce bai so Iyah ce zata koma 'dakinta ba yayi karya, hakan nan idan ya ce mahaifin Farida yasan ciwon kansaa Nan ma bai yi karya ba. Amma ko dan ya ramawa Mk kadan cikin alherin da tunda yasan shi yake masa ba gajiya har yau yasa shi cewa "madallah jibin idan za ku tafi ku biyo ku dauke ni da ni za'a je neman aure tare da godiya ina fatan alheri tare da fatan ta kasance abokiyar arzikin ka ce". Kafin jibin kuwa sai da Baffa ya siyar guda cikin filayen nan wadda kudin daya ya zarta kudin duka biyun sadda aka siya, sosai gurin ya yi daraja adalilin anata gine gine. Dubu 'dari uku da talatin aka siyar. Da daddare ya Kira Mk ya danka masa dubu dari biyu akan ya bawa Alh Isa dan akai gidan su Farida. Kunya ta kama Mk ya ki karba, ai kuwa Baffa ya rantse sai ya karba sai idan ya raina me ko yana ganin bashi da arzikin da zai masa alheri. Da sauri Mk ya sa duka hannunsa ya karba yana cewa "Haba Baffa, mahaifana ne kawai suka mini alheri sama da kai, har yau kuma banga dattijon arziki sama da aki a idona ba gani na yi na doara maka nauyi mai yawa Baffa! Ina rokon na raba biyu na dauki rabi". "Duka na baka Mutari sadaki ne haka nake so ka bayar dan su san iyayen ka sun san alheri, ko da sunce basu bu'katar komai daga garemu dole ka bada sadaki, burina ace na biya maka fiye da haka, ban son Alh Isa ya gane ni na bada kudin shiyasa na baka a hannunka da sai munje zan bayar, sannan shine wakilinka dole shine mai bayarwa". Zuciyar Mk ta karye ya yi kasa da kansa yana jin hawaye na Shirin zubowa. Haka kuwa! Da Baffah aka kai kudin auren Mk akasa 'daurin aure sati mai zuwa, tunda ba tarewa zata yi ba, sai sun dawo, can ingila zasu tafi. Har zuciyar Alh Isa yake jin rashin da'di, har jinyar kwana biyu ya yi adalilin kunyar Malam Basiru da takaicin Mukhtar. Haka kuma Mk da yake jin tamkar 'kasa ta tsage ya shige dan tsananin kunyar Baffah. *SURAYYA DAHIRU* ✍️✍️. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 Na *SURAYYA DAHIRU GWARAM*. •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_Dokɑr hɑkkin mɑllɑkɑ me lɑmbɑ tɑ 68, tɑ nunɑ cewɑ sɑtɑr fɑsɑhɑ bɑbbɑn lɑifi ne dɑ yɑke dɑidɑi dɑ sɑtɑr dukiyɑ._* *Comments din ku na sani nisha'di kwarai da gaske! Na gode muku ubangiji ya bamu damuna mai albarka*. *Gaisuwa da fatan alheri ga dukkan yan KUNGIYAR LAFAZEE WRITERS*. *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR* 85-86. Murna wurin Farida tamkar ta zuba ruwa a kasa ta sha, ta godewa Allah, ta godewa mahaifinta Ashe da gaske yake da ya ce sai inda karfinsa ya kare wurin nemo mata farin cikinta. Ta tuno sadda Mk ya auri Sa'a irin kukan da ta yi a kirjin mahaifin ta, yana lallashinta da kalmomi masu da'di, tare da al'kawarin matu'kar yana raye sai ta auri wadda ya fi Mukhtar, ko kuma shi Mukhtar din kansa. A wanccan lokacin bata gasgata ba, kawai ta dauka saboda ya kwantar Mata da hankali ne. "Wa yake da uba irin nawa?" ta furta a fili, hawaye na zirarowa wadda ta tabbatar sune na karshe akan rashin Masoyi. Sa'a kuwa ba tasan me yake faruwa ba, har sai da auren ya rage kwanaki uku, Zainab ta gano musu a group, da farko bata gasgata ba, amma da yake Rukayya Mustapha aminyar Faridan suna dan gaisawa da Zainab sama sama tunda duk class mate ne, anan ta tabbatar jibi Uncle Mk Bichi zai angwance da Farida Torondi. Hankalin Zainab ya kasa kwanciya, a gigice ta tafi gidan su Sa'a amma da ta lura

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});