Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 146

Chapter 146

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

irin ta tare tun kafin a ankara da halin da take ciki. Ta dinga tunanin yadda zata sanarwa Mk tana son tariya da wuri, ta tuna ranar da ya sameta gidan Sumayya kafin ya yi tafiyar, da muradinsa na son su tafi tare, Amma ta kekasa kasa ta 'ki. Ta nisa tana sake tuno sadda suke yiwa juna gatse, inda ita ta ce a bari sai nan da shekara guda. Zuciyarta ta harba idan kuwa hakane har sai ta haihu, da kusan wata hudu. "Tirkashi" ta furta a fili, tun yanzu kunyar Innah take ji, gashi dai a gabansu ta yi ciki, sa'ar da aka yi, ba cikin gaba da fatiha bane kamar yadda Inna ta gani a mafarkinta. Kwanaki uku da zuwan Sa'a asibiti ta kasa daurewa saboda yadda kullum take Samun sababbin alamomin da Za'a fahimci halin da take ciki. Da daddare tana kwance a dakinta, ta kalli agogo, ta ga lokaci ya fara ja, amma hakan ta kasa hakuri ta 'kira layin Mk. Ringing biyu ya dauka, Yana ayyana zuciyarsa da ta Sa'aadah tare suke bugawa, domin kwnaciyar da ya yi ba abin da yake tunani sai ita, yana mamaki yadda bata neme shi ba, gashi har ya doshi kwanaki ashirin, amma ko ta 'Kira ta ji ko ya Isa lafiya. Ya dauka! Amma ta yi shiru, ya nisa tare da cewa "Ina Jin ki, ta jima tana zumbure zumburen baki tamkar Yana gabanta. Da kyar ta ce "Ina yini?" Ya amsa da cewa "lafiya kuwa?" Ta 'kulu amma ta daure ta ce "sai ba lafiya zan neme ka?" "To na ga tunda na yi tafiyar nan ko Kirana ki ji yana isa baki yi ba. Ni kuma na kira ki ba adadi kin ki picking, saboda kawai ki nuna mini da gaske kike ba kya sona, ba kuma wani abu na alheri a tsakaninmu da cin arzikinsa" Ya fa'da a dan tunzure ka'dan. Ta yi shiru tsananin sonsa na ratsata mussaman cikin jikinta idan ta tuna bai yi gaggawar kaita auren wani ba, sai ta tsatson Mk ya fito sai ta ji kawai tana ambaton Alhamdulillah! Babbar matsalarta kishin auren Farida , ta tabbatar da wata ya aura ma zata ji kishin amma ba kamar na Farida ba, domin shi ka'dai me dalilin da yake sawa ta ji tsanarsa da tsanar cigaba da kasancewar a doron 'kasa. Hawaye ya cika idonta sosai, ta daure ta kuma cije bata bari kukan ya kwace ba, da rawar murya ta ce "yaushe zaka dawo?" "Inace na fa'da miki sai na cinye kwanakin wata?" Ta yi shiru! Ya nisa ya ce "fa'da mini menene tunda na san haka kawai ba zaki nemi ni ba tunda kin ringa kin jefa ni sahun Marasa adalci da daraja a duniyar ki". "Ni ni bani da lafiya ne". Ta fa'da a rarrabe kuma a shagwabe. "Me ya same ki?" Ta yi shiru, ta kasa cewa komai. "Na san dai ba kewata kike yi ba, tunda tuni kin cire ni a masoyinki". "Dama zan fa'da maka ne, Anty Sumayya da Umman Fanshekara suna son zuwa su ga gidan da zan zauna". Ya murmusa ya ce "Na san ki tamkar tafin hannuna, fa'da mini dai gaskiyar magana. Kawai ki ce kin fasa yin rabin shekarar kina son tarewa dan kar abin da kike boyewa ya bayyana a gaban su Baffah". Zuciyarta ta tsinke, da sauri ta ce "me nake boyewa?" Ya waske da cewa "Tarin Sona mana na zuciyar ki, bayan bakinki yana ta jifana da kiyayya". Ta saki ajiyar zuciya mai nauyi. Ni ai dama ban ta'ba cewa bana sonka ba, sai dai na ce da aure ne bana yi, saboda kaima ai ba ni kake so ba". "Fahimtar ki ce hakan, kuma Wallahi ina taya ki jin kunyar ace kin rayu da ni shekaru bakwai, amma baki ki san wannene Mukhtar ba". Ta katse shi ta hanyar cewa "Ni yanzu me zance wa masu son zuwa ganin gidan?" Kai-tsaye ya ce "ki ce ban kammala gyran gidan ba, sai nan da wattanni shida lokacin ya yi dai dai da kammaluwar na ki Shirin". A mugun shagwabe ta ce "Bana son haka, bana so, ka daina daukar hakkina haka Nan". Wani irin farin-ciki ya mamaye Mk ya ce "fa'da mini me na yi miki na daukar hakki?" "Ni kawai ka fa'da mini gaskiyar abin da zan fa'da musu". "Ki fa'da musu saboda kin ce sai kin gama shiryawa, ya sanya nima na shiririce. Da gaske ban tanadi inda zaki zauna ba". Hakan da ya fa'da ya sa ta fashe masa da kuka sosai. Ya matse dariyar da ta so subuce masa ya ce "Share hawayen ki kin ji my dear, ki bari idan na dawo sai mu yi maganar a nutse, ki fa'da musu bana gari, Amma da zarar na dawo, zamu tattauna". Da yake son tariyar take yi a kwanakin nan yasa ta biye masa, suka rabu kalau. Yana ajiye wayar ya dinga dariya yana fa'din Ubangiji ka kaddara addu'ar da nake yi ne ka karba, ubangiji ka kaddara hasashena ya zama gaskiya. Ya yi shiru yana murmushi a zuciyarsa sai fa'dawa Ubangijinsa yake yi idan har ya tabbata ciki ne da ita azumi uku zai yi na godiya ga Allah, abin da ya da'de yana son ayi masa kenan haihuwa! yana son ya ga Jawad ya na da mahadi, yana son 'kananun yara. Ya tuna lokacin da ya matsu Sa'a ta sake haihuwa amma kawayenta suka zugata wai zata tsufa da wuri. Ya fesar da zazzafar iskar bacin rai, a fili Kuma sai ya ce "Na yafe komai, na manta komai". Sati biyu Mk ya dawo, zuwa wannan lokacin cikin yana shiga sati na bakwai, ta fara wani irin fari, sai kuma ya canja salon ba komai zata ci ba, asalima bata isa ta sha tsurar ruwa ba. Sai dai ta sirka ya dai canja launi. Ga miyau bai tafi ba. Kullum cikin Hijabi take da safa, saboda yadda kafafuwanta suka yi fari, suka yi fresh, da zarar Baffah ya tafi Gogel zata tafi gidan Sumayya, saboda kada Innnah ta ganota. Washagarin dawowar Mk ya iso wajen Sa'a da tarin tsarabar manja da kuma kwakar manja. Da rawar jiki ta kai ta zubo a bowl ta dawo ta hau ci tamkar nama. Ya zuba mata ido yana ganin sauyuka a tare da ita karara. Zuciyarsa ya gama gasgata zatonsa. Ya dinga Hamdala a ransa. Lafiya Lau suka gaisa, ba bacin rai. Ganin Bai sako maganar da ya ce sai ya zo ba, ya sa ta kawar da fuskarta gede ta ce " Ya maganar da na yi maka?" "Wacce?". Ta tura baki gaba ta ce "su Anty sun matsa mini akan zasu je su ga yanayin windows da kofofi saboda maganar labule". Ya cije ya ce "idan dan wannan ne ba matsala na riga na tanade su". "Kar ku damu". Ta juyo ta ce "Na damu ni na gama shiryawa ranar juma'ah zan tare". Dariya ta kwace masa sosai, yayin da itakuma ta hau kuka marar sauti. Ya kalleta sosai sai fahimci kuka take tunda ga zuciyarta ba wai na shagwaba bane. Ya hadiye dariyarsa ya ce "menene kuma amma dai kinsan ban son irin wannan kukan ko?" Ta kasa magana. Sai da

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});