Chapter 2
Chapter 2
turaran Escada sentiment, turare na mussaman mai sau'kar da nutsuwa ga duk wadda yake shakar shi, sai kai wa hancinsa ziyara yake yi. Ta sake zamowa yar yarinya, ta fi kama da 'yan shekaru ashirin da biyar ba wadda ta ba wa talatin baya ba. Jawad ya mi'ke yana cewa, "Malam Ina zuwa.'' Kai kawai ya kada masa, kai tsaye uwarsa ya nufa, gabanta ya tsugunna ya ru'ko dukkan hannayenta, "Mami ki zo ku gaisa da Malam mana" Kai ta girgiza masa alamun ba za ta ba. "Haba Mami gaisuwa kawai?" Kan ta sake girgizawa a karo na biyu, tana ci gaba da latsa wayarta a cikin manhajar WhatsApp inda abokan tafiyarta suka ce mata ya kamata su ta fi haka nan, kar su yi dare. dan haka ta fara tattare warmers din da ta zo da su, tare da mi'ka masa ledojin siyayyar da ta kawo masa, tana sake jaddada masa ya kula da karatu ya kuma kula da ibada, muryarsa na rawa alamun zai yi kuka ya ce mata, "Ba fa ki gai da Malam ba". A dan tunzure ta ce "Dole ne?" Ganin kwalla a idonsa sai jikinta ya yi sanyi ta dauki handbag din ta tare da basket mai dauke da kulolin ta ce "mu je to." Karbar basket din ya yi suka nufi Malam din da tazarar su bai fi taku biyar ba, don haka a kan kunnen shi duk yake jin tattaunawarsu. Ba ta isa daf da shi kamar yadda Jawad ya yi ba, ta tsaya daga dan nesa ta ce, "Ina yini?" ji ya yi kamar ba zai amsa ba tunda a wulakance ta yi gaisuwar, Irin gaisuwar je ka na yi ka, amma ganin Jawad ya zuba musu ido, sai ya amsa har ya na tambayar Inna, wanda ta ji shi, amma sai ta yi kamar ba da ita yake ba. Hannu ta mikawa Jawad akan ya ba ta basket din, no'ke kafada ya yi tare da cewa! "Mami, Malam fa Kano zai wuce, don Allah ki bari ku wuce tare." Wani malolon ba'kin ciki ya sa ke turnuketa, bayan ya tilasta ta, ta gaishe shi, ya kuma sake baro wata magana. Ba ta ce masa komai ba ta fincike basket din tana cewa, "Na gode ba sai ka kara gani na zo ba bare ka yi mini wannan iya shegen!" Ta juya ta fara tafiyarta mai cike da nutsuwa, da sauri Jawad ya bi bayanta, yana cewa, "Haba mana Mami kar mu yi haka da ke!" Kawai sai ta saki basket din hannunta da jakarta ta riko shi ta ringa zuba masa rankwashi tare da dundu, a sukwane Uban ya taso ya karbe shi yana jin takaicin ta na sake kama shi, wai a makaranta ma cikin jama'a ba za ta fasa halinta ba? Sa'arsa daya ma, wajen ba mutane kusan duk an watse sai tsirarru. Ta sunkuya ta debi kayanta ta tafi tana huci, ganin haka Jawad ya fincike daga hannunsa ya bi ta yana fadin,"Ina zuwa Malam!" Da gudu ya cim mata ta baya ya rungeme ta yana fadin, "Am sorry Mami, very sorry!" "Ai ni kuma ba ruwana da kai Jawad, tun da dai kai ba ka jin magana, na hana ka wannan manyancen naka, na hana ka shiga abin da bai shafe ka ba, amma ka 'ki, to ka je ka yi ta yi." Ya marairaice yana ba ta ha'kuri har dai ya samu ta ha'kura ya ga murmushinta. Malam yana zaune yana kallon su har suka ba ce ma ganinsa, a ransa yana mugun tausaya wa Jawad, tun da shi burinsa a ce Mamansa na tare da su, wadda faruwar hakan sai ikon Allah. Yana zaune, ya dawo ya tarar da shi yana ta tunani, "Ni ma ai zuwa zan yi na tafi. Mu je mota ka kwaso kayanka." Daidai lokacin wayarsa ta dauki ruri, yana dubawa yaga matarsa ce Farida ya amsa, tambayar Jawad ta yi, wayar ya mi'ka ma yaron tare da cewa, "Karbi!" Ba wani karsashi ya karbi wayar har ita ma ta ji babu dadi tana tambayar shi ko lafiya ya ce mata, "Lafiya lau!" Bana son Malam ya tafi ya tafi nee, sannan baku zo ba ke da Hajiyan Bichi". ta shiga bashi hakuri cike da murna ganin ya fara dawo mata tamkar farkon zamansu. Suna tafe yana masa nasiha tare da nuna masa ba ayina uwa ba a yin musu da ita, dole a bi ta yadda take so, sannan ya daina shiga matsalar da ba tashi ba, hawaye yake gogewa tare da cewa, "Ni dai Malam ka dawo da ita gidanmu ni ma in dinga ganin Mamana a gidanmu, kamar yadda nake ganin na friends dina, kowa Mamansa da Babansa tare suke zuwa masa amma banda ni!" Ya 'karasa cikin kuka sosai, janyo shi jikinsa ya yi yana dan bubbuga bayansa alamun rarrashi yana cewa "Ina ce ni ma tare da Antinka nake zuwa maka?" "Amma ai ba da Mamana kuke zuwa ba!" "To ka kwantar da hankalinka, ka dinga mana adddu'a sai ka ga very soon ta dawo har ma ka zama Yaya Jawad kana so?" Ya daga kansa tare da sa hannu yana goge hawayen da ya'ki tsayawa. "To in dai kana son haka, ka daina damuwa ka kuma daina yiwa Mami maganar bare ta dake ka, kawai addu'a za ka na yi, ni kuma ka dinga tuna mini, wataran sai dai ka dawo hutu ka ganta a gidanmu." "Malam da gaske?" ya tambaya cike da zumudi. "E Mana indai ka daina kuka, ka daina damuwa, ka daina damunta, kana addu'a to ina tabbatar maka ba abin da ya fi addu'a juya lamura!" Murmushi ya shiga yi yana goge hawaye da handkerchief din hannunsa yana 'fadin, "Ai ko Malam ban san murnar da zan yi ba,, kuma har da kai zan 'dauka a jirgin nawa". Dariya Mk ya yi tare da cewa "Ai kuwa dai nima naji dadi tunda albakacin Mami zan shiga jirgin Jawad" Kunya ta kama yaron yace "Ai dan ita bata taba shiga bane" Ya sake cewa, "Malam ka gai da Hajiya, kuma ina zuba idon zuwanta, tunda ba ta zo yau ba, ina bin ta bashi!" Alkalamin Surayya Dahiru ✍️ [5/11, 17:15] ~fatieshak🌹: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ *Tukuici ga* *FADILA LAMIDO* *BINTA UMAR ABBALE* *ZAINAB MAZAWAJE* *Nagode da Shawarwarinku da 'karfafa guiwa, Allah Ya saka muku da alheri, Ya 'kara daukaka.* *GODIYA GA MAKARANTA* *Na gode da yadda kuka 'karbin wannan labarin, ha'kika jiya na ga ruwan masoya, ban yi zaton a 'kankanin lokaci littafin zai 'karade duniyar karatu haka ba, na gode muku sosai, in sha Allah ba za ku yi NADAMAR bibiyar wannan labarin ba!Heart U all* 3-4 A sanyaye ya fito wa da Jawad kayayyakin provisions din da ya kawo mishi, tamkar wanda zai yi rabin shekara bai je gida ba, yana sake jaddada mishi ya daina damuwa ya kuma ci gaba da karatunshi. Ya shiga mota Jawad na 'daga mishi hannu har ya fice, bai yi nisa sosai ba don kuwa bai gama barin garin Kiyawa ba, ya hango su Sa'adah da wasu matan a waje, gefe kuma an bude motar bakanike sai tabe-tabe yake, ga dukkan alamu motar ce ta lalace musu, kamar ya wuce sai kuma
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157