Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 131

Chapter 131

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ta binta tunda mu muke nema, sannu a hankali har mu samu mu damketa". Mk ya nisa, ya ce" tunda na rabu da yarinyar nan wani abu mai tsananin nauyi ya tokare ni a kirji da makoshi, har yau din nan bai fada min ba, sai kara girmama da abin ya yi a yanzu da nake ganinta da wasu, wai ya zanyi ne? Wallahi na fara debe kauna da rayuwa domin Ni ka'dai nasan azabar da nake hadiya mussaman ace dare ya yi lokacin da zan samu na huta, a lokacin ne nafi shiga tasku bana iya barci, yanzu kuma abincin ma baya shiga". 'Karfi ya nisa ya ce "ka daina damuwa komai zai wuce, idan ka ga ka rasata, to kawai ka dauka babu alheri ne a kasancewar ku, ubangiji ne ya karar da zaman. Sai ka duba ai ka rayu shekaru bakwai babu ita, kuma baka mutu ba, idan har ita zata iya yin jarumtar hakuri da kai gaba'daya, bayan ta sha dukkan ba'kin ciki da tashin hankalin son komowa gareka, to kuwa kaine ka fi cancanta da irin wannan jarumtar". Mk ya yi shiru yana gasggata Sa'a ta fi shi jarumta, tunda har zuciyarta bata buga adalilin aurensa ba, don kuwa shi yanzu ya gama yin imanin duk ranar da aka daura aurenta da waninsa tabbas a ranar ajalinsa zai sauka adalilin bugawar zuciya, ko hawan jinin da ya zarce kima. A raunane ya kalli 'Karfi ya ce "Ai ita mace ce, ubangiji ya sanya musu wani irin karfin jure dukkan kalubalen tarbiya da kishi, amma mu ba a bamu wannan ba, namiji karfin gwagwarmaya aka bashi, da karfin tsayawa iyalinsa akan dukkan bu'katun yau da kullum". 'Karfi ya nisa ya ce "Hakane! Abin da nake so yanzu da kai shine, ka dora jarumtar gwagwarmaya a zuciyar ka, tunda ka gamsu muna da karfi da juriya anan bangaren, to idan kuwa hakane, zamu yi gwagwarmaya har mu samu mu kwato abin da yake namu ne". Tun daga ranar suka fara yiwa Iyah wani irin naci, mai cin rai. A Rana su kanje sau uku, kowanne lokaci zuwa suke yi, tun Inna tana ganin zasu gaji su daina, har ta fara ganin ba zasu gaji ba, domin kuwa kullum zaryar kara gaba take yi, ba baya ba. Haka gidan Sumayya, hatta Idris a yanzu tausayin Mk yake ji, shiyasa ya fa'dawa mai gadin gidan matu'kar Mk ne suka zo, to ya bude masa gate kai tsaye. Tsawon sati uku ana wannan zaryar bai fi kuma sau biyar suka samu nasarar ganinta ba, a cikin zuwa fiye da arbain. Duk inda hankalin Mk yake a tashe yake, yayin da Mahmoud yake ta karfafa masa guiwa duk da shima bai yi zaton kafiyar Sa'adah ta kai haka ba. Ranar alhamis da hantsi suka isa gidan Sumayya, sun shafe lokaci mai yawa a zaune, sannan ta fito, sanye da hijabi fuskar nan a daure, ta iso, da alamu tilas aka yi mata. Dr Karfi ya mike ya na fa'din barka da fitowa sarauniyar mata. Ta yi shiru tamkar ba da ita yake ba, domin ta lura shine jagoran wannan nacin da suke mata kamar ba'kaken mayu. Ya ce "Allah ya huci zuciyar giwa kuma gimbiyar Mata, ba zamu gaji da bada hakuri ba, ba kuma zamu gajiya ba, har sai kin dawo mana da walwalar da ta yi mana tutsu. Ki yi ha'kuri, ki zo ki haska mana zuciyar aminina da gidansa gaba'daya, Ina rokon ki, badan mu ba, sai dan ubangijin ki, ni shaida ne na irin tsananin son da yake Miki". A tunzure Sa'a ta ce "ka dinga jin tsoron ubangiji Baban Dady! Sai yanzu! Sai yanzu! Sai yanzu zaka tirsasa ni, me yasa a wanccan lokacin baka tirsasa shi ba, me yasa ka bari na wulakanta, na tabbatar ba zaka so ayiwa kanwarka abin da aka yi mini ba. Amma yanzu da yake farin-cikin abokinka kawai ne a gabanka, ka na'de 'kafar wandon yi mini dole, kasan ina jin nauyinka, akan me zaka takura ni irin haka, an ta'ba yin aure dole, to ko Baffah ma na tabbatar masa bana son wannan mutumin, kaima na fa'da maka, ka sakar mini mara, na ro'ke ka". Ta karasa cikin kuka sosai, Dukkan su sun yi laushi, mussaman Mk da yake jin tamkar ya hadiyi zuciya saboda yadda yake jin ciwon yadda take fadin bata sonsa, a gaban kowa. Mahmoud ya kalli Agogon hannun sa, ya ce "hakuri zaki yi, ba yadda zamu yi ne, ki 'kara hakuri, ubangiji zai baki ladan masu hakuri. Ya kalli Mk ya ce " ina da appointment nan da mintina talatin a makaranta, zan wuce, idan ka gama kawai mu hadu a gidanka bayan azahar". Daga haka ya fice da sauri, da mukallin motar Mk a hannunsa. Tana tsaye tamkar soja. A hankali Mk ya ce "zauna mana Dan Allah". Bata yi musu ba, ta zauna. Ya zuba mata ido yana kallon yadda ta ke cika tana batsewa ya saki ajiyar zuciya mai zafi ya ce "A gaban kowa kike fadin ba kya sona, Ni kike wulakantawa haka? Kada kishi yasa ki manta ke ce kika mini laifi?" Da kuka ta ce "Ni na maka laifi tabbas, ka kuma hukutan ni, to menene kuma ba sai a barshi a hakan ba, gaskiya kun matsa mini, tsakani da Allah kun shiga rayuwata, sau nawa zan fa'da maka bana sha'awar sake rayuwa da Kai? Na ha'kura, na bar mata, Ni ma ka bar ni, Dan Allah". Kafin ya yi magana ta sake cewa "kafin ka aure Ni ka kira ni Ballagaza, na yi hakuri saboda ina ta'kama da Budurci, yanzu kuma ka ce ina ha'intarka, fa'da mini dame zan kare kaina, tunda ba ni da Budurci a yanzu?" Da sauri Mk ya karaso kujerar da take zaune, ya zauna a hannun kujerar ya sassauta ya ce " Na da'de ina fada miki, bacin rai ne, ba ina nufin haka har zuciyata ba, ki yi hakuri. Na janye kalamina, wallahi tallahi ke din katangaggiya ce, ki bar wannan maganar, ko tunawa bana so, hankali na tashi yake yi. Na janye! Na janye! Na janye Dan Allah a rufe wannan maganar har abada". Ta dinga kuka sosai mai cin rai, ta kasa cewa komai. Ya nisa ya ce" kukan ya isa haka, ki yi hakuri ina fatan wannan ne kukan ki na karshe akan wannan matsalar". Ta kifa kanta a dayan hannun kujerar tana sake tsananta kukan sosai, Ta ce "indai baka rabu da ni ba, na tabbatar zan dauwama ina kuka ne, domin zan rayu ina raba ka da wata ne, Ni kuwa da haka gara na auri me mata uku na zama ta hudu". Mk ya rasa mai zai yi, ko ya ce, gaba'daya tunaninsa gaba'daya ya kulle. Ya tabbatar auren Farida ne cikas dinsa a gurinta, shine yasa ta kasa amincewa da shi. Ba yadda zai yi akan Farida kuwa domin bai aureta dan ya saketa akan wani 'karamin dalili ba. Ya sassauta ya ce "Yarda da 'kaddara na cikin sharuddan cikar imani, ki ture komai, ki kalle ni har yanzu ba abin da ya canja na soyayyar ki a tare ni, ki bani amanar kan ki wallahi ba zaki yi nadama ba". "Ko yanzu kika

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});