Chapter 34
Chapter 34
kika mini?" Ta san sarai a cikin fishi yake, don haka sai ta lankwashe harshe ta ce "Ka yi ha'kuri don Allah!" Da sauri ya cafe da cewa "Ni fa ba ki mini komai ba, laifina ne da na zo kai tsaye ban sanar da ke ba, sannan ai yaudarar kai ne na yi tsammanin ni kadai kike kulawa, ke allura ce a cikin ruwa don haka feel free you did nothing." Ta kasa gane inda ya dosa shin gatse ya ke mata ko kuwa da gaske hakan yake nufi a zuciyarsa? Don haka sai ta ce "To ka dawo na ganka dama ai na kwana biyu ban gan ka ba" Kai tsaye ya ce, "Ai ba na zuwa zance da daddaare" Shiru ta yi sannan ta ce "To gobe za ka zo?" Tana rufe baki ya ce "Ina da schedules masu muhimmamanci a gobe." Kawai sai ji ta yi kuka ya zo mata, cikin rawar murya ta ce "Har sun fi ni muhimmamanci?" Cike da rashin kulawa ya furta "Wadancan tabbas ne, ke kuwa gaibu ce." Ta yi shiru amma kuka take yi, yana jin yadda ta ke jan majina da shassheka, amma ya yi burus da ita, yana fatan ta ji a ranta cewar ita ba wata tsiya ba ce a gunsa. Cikin kuka ta ce "Ni ka ke kwatantawa da gaibu?" Ko dar bai ji ba wurin ba ta amsa da cewa, "E!" A gajar ce. Bai sani ba ko kishin dake cin zuciyarsa ne, ya sa bai ji kukanta ya taba shi sosai ba. Yayin da ita kuma bakin cikin yadda yake nuna mata rashin kulawa yake dada addabar ta. Duk da hakan sai ta daure ta ce "Jibi Juma'ar za ka zo?" "Zan zo idan ina cikin masu rai da lafiya idan kuma uzuri ya taso ban sami zuwa ba, to sai satin sama." Ta yi shiru tana jin ta rabu da wannan mutumin da yake nuna mata ita ba komai ba ce a idonsa, sanin ya gan ta da wani ta san dole zai ji ba dadi yasa ta ajiye komai ta neme shi. Har ha'kuri ta ba shi amma shi ya nuna ma ba laifi ba ne bai yi fishi ba, anya kuwa yana son ta, anya ba ita ke bankaura akansa ba? Jin ta yi shiru ya sa ya magantu da cewa, "Sai yadda ta yiwu." Ya katse wayar! Bakin ciki ya kama ta sai kawai ta kife kai a kan filo tana kuka. Shi kuma ya mike ya mayar da wayar aljihunsa, yana sake jin sau'kin radadin da zuciyarsa ke yi masa, tunda dai ya tabbatar ita ma ta shaki takaici. Washegari tun safe Sa'adah ke zuba idon kiran MK har aka yi sallar Isha bai kira ba, a lokacin ha'kurinta ya gaza, ta dauko wayar Inna ta shiga kiran sa, sai da ta gama ringing bai dauka ba, tana shirin sake kira sai ga kiransa ya shigo. Ba ta tsaya jan aji ba ta dauka da sauri sai kuma ta yi shiru ta ki yin magana. Sai da ya yi sallama har sau biyu sannan ta amsa ciki-ciki, mamakin ta ya kama shi amma ya waske ya ce, "Mura ki ke yi ne?" Nan ma ta yi shiru ya nisa ya ce, "Yau yini guda ban zauna ba, ina ta yunkurin kiran ki, sai wani al'amarin ya mantar da ni. Yanzu kuma na dauko wayar da nufin na kira sai kika riga ni, Ina fatan kin yini lafiya?" Haushin sa ya kama ta sosai ta kasa tanka masa, amma tana raya cewa wai ya manta da jin muryarta. Jin ta sake masa shiru sai ya kashe wayarsa. Ita ma ta ajiye wayar daga kunnenta, tana gaskata zarginta na zaton MK da gaske ba son ta yake yi ba. Kafin ta yi yunkurin yin wani abu kiransa ya sake shigowa ta yi kamar ba za ta dauka ba sai kuma zuciyarta ta kasa jarumta. Haka ta sa hannu ta amsa, ba tare da ta yi magana ba. "Kina jina?" Abin da ya furta ke nan, ta sake yin shiru! takaici ya kama shi cikin fa'da fa'da ya ce, "Kin san ba za ki yi magana da ni ba mene ne zai sa ki kira ni?" Sai kawai ta saka masa kuka mai tsananin gaske irin mai cin rai! Ya yi shiru yana jin kukan nata wanda yake rasta dukkan sassan jikinsa musamman yadda take yi tana ajiyar zuciya. Jikinsa ya yi sanyi sosai sannan kuma hankalinsa ya tashi, duk da ya san ma'abociyar kuka ce ita din, amma wannan ba na zallan shagwaba ba ne, da alamun damuwa sosai a cikin kukan. Ya yi kasa da muryarsa sosai ya ce, "Me ya faru, fada mini mene ne yasa ki kuka haka?" Jin ya karya murya yana tambayar ta sai wani kukan ya sake kwace mata sosai wanda ya tayar da hankalin MK sosai. A gigice ya dinga fadin "Don Allah ki yi shiru ki fada mini me ya faru, kin tayar mini da hankali." Ta kasa magana saboda kukan ya ci karfinta ita kanta so take yi ta daina amma ta kasa sai shesshka da ajiyar zuciya ta ke yi. Ya yi shiru yana jinta, yana jin shi ma tamkar ya rushe da kukan ko ya sami sau'kin yadda zuciyarsa ke bugawa. Ya lankwashe murya ya ce, "Sa'adah! so ki ke ni ma na yi kukan ne? Don Allah ki taimake ni ki yi shiru haka nan , ko so ki ke kanki ya yi miki ciwo?" Cikin kukan ta ce, "Ka damu da ni ne da har kake gudar mini jinya?" Ya ce, "Haba Sa'adah wacce irin magana ce wannan! Ai ni gani nake yi Baffa da Inna ne kawai suka fi ni damuwa da ke " Ta yi fit ta ce "A hakan?" Ya nisa sannan ya ce, "Ke matsala ta da ke ba ki fahimce ni ba, har yanzu kin kasa gane manufata. Kowanne Dan adam yana da tsarinsa, don ina sonki ba zan miki karya ba, abin da nasan zan iya shi zan miki, amma tun ba mu je ko'ina ba, na gane kin raina kulawar da nake ba ki gaba'daya" Ya dan yi shiru sannan ya nisa ya ci gaba da fadin, "A farko tsakanina da Allah kamar yadda na fada mikil saboda jarrabawar da za ki yi yasa ban cika yawaita zuwa da kuma kiran ki a waya ba, sai ke kuma hakan ya zama dalilin da kika mini kishiyoyi, alhalin kin san har a gidanku na bayyana kaina ina son auren ki" Ya fada muryarsa da rauni sosai. Yayin da ita kuma kukan ya tsaya mata cak, tana jin wani irin abu na taso mata da ta kasa tantace mene ne shi. Ya sake cewa, "Sa'adah duk motsin ki akan idona kike yin sa, ta ya ya ki ke tsammanin zan saki jiki da ke alhalin na tabbatar zuciyarki tana rawa a kaina! Na dade da gane kin samu mai kudi, na dade da sanin kina tare da Khalil har yanzu, ba don ina son ki sosai ba ai kamata ya yi na janye kaina a cikin 'yan takara amma kullum ina karfafa wa kaina guiwa da cewa idan rabona ce ke zan same
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157