Chapter 156
Chapter 156
cewa "Allah ka bawa Farida haihuwa ko wannan tausayin da yake neman zame mini barazana ya yi sau'ki". Haka ya lallabata. Haka da Farida ta dawo, ya ja kunnanta da cewa "da bakin ki, kin ta'ba cemin kina fakar idon mutane kina tsokanarta, to ki bari tunda bata so, Nima bana so, ki kiyaye bana son muna samun sabani". Ta tsiri fishi! Ya tattara ya watsa da ita, ya shareta, dake bame yawan fishin bace da kanta kuma ta dawo hanya. Haka rayuwar take gudana yau fari gobe tsumma kowa ha'kuri yake yi da abin da rayuwa ta zaba masa. A haka Allah ya sauki Sa'adah lafiya! Ta haifi danta lafiyayye mai kama da Jawad sak, kenan Mk shima ya biyo. Kwananta'daya a asibiti aka sallamota bayan an tabbatar da lafiyarta da ta jariri. Tana zaune a dakinta ta tsurawa jaririn ido tana ayyana abubuwa masu yawa, bai zo da wuri ba a lokacin da Mk ya matsu ta haihu, haka bai yarda ya fito a jikin Farida ba, bai kuma fito a jikin wani namijin ba, tabbas kudurar Ubangiji yawa ne da ita, duk tsawon shekarun nan sai da ya jira ya fito ta tsatsonsu a lokacin da ba a yi zato ba, Wannan ka'dai ya isa aya ga mai hankali. Dai dai lokacin Mk da Farida suka shigo. Dukkansu suka isa gareta cike da kulawa suna yi mata sannu. Farida ta rungume yaron da tun jiya da ta 'dora ido akansa ta ji son yaron ya shigeta tamkar ta sace shi ta gudu. Sosai ta rungume shi, karon farko das tausayinta ya kama Sa'adah! Mk ya dinga tambayarta ko abin da take so ko bu'kata? Ta ce "Ba komai so dai nake yi na je gida ko kwana goma ne! Ka ga Umman Fanshekara bata jin da'di ba iya zama mini zata yi ba". Ya girgiza kai da sauri ya ce "ba zai yiwu ba, abar maganar". Ta yi shiru tana cewa "An barta". Mamamki ya kama Farida ada kallon mijin ta ce take yi masa indai akan Sa'adah ne, ashe ba ita ka'dai yake hana yin wasu abubuwa ba har da tauraruwar tasa. Tsawon lokaci sannan Farida ta mike da nufin basu guri ta ce "Tamkar na tafi da shi, tamkar na dawma ina kallonsa". "Tafi da shi mana Farida ai d'anki ne". Sa'a ta fàdi hakan a tausashe sannan ta mike da kyar tana janyo akawatin kayan yaron, Mk ya ce karfa ki fa'di". Ta dire a gaban Farida ta ce "Ki tafi da shi, ki dauwama kina kallonsa,ya dauma a 'danki, ina miki al'kawari ni dai a bakina wani mai rai ba zai ji ni na haife shi ba, ke din masaniyar magaganganuwa ce, kin san wadda zaki sha ya taimaka ruwan nono ya zo miki, na shayar miki da shi na kwana 'daya da yini, ubangiji ya taya ki tarbiya da juriyar raino, ina kuma yi miki fatan ki samar masa 'kanne ta tsastonko masu yawa". Mk ya mike da sauri ya rungume Sa'a yana jin sonta yana sake tumbatsa. Da rawar murya ya ce"Tunda kika yi sa'a Baffah na ya haife ki, na sani zaki yi abin da yafi haka na karamci! Na gode miki sosai Ina tabbatar miki har yau din nan ke ta dabance a cikin duniyata. Allah ya miki albarka! Idan har aljannarki tana 'damfare da yardata ne, wallahi daga yau na yarje miki, daga yau din nan Ubangiji ka shaida komai Sa'adatu zata mini na kuskure, har zuwa karshen zaman mu na yafe mata, na yarda da ita, Ubangiji ka yarda da ita". Farida tana tsaye tana kallonsu tana Jin inama itace Sa'adah! Ta matsa kusa da ita ta kalleta cikin ido ta ce "Wallahi Sa'adah kin fini kirki, kin fini hakuri, na tabbatar a yanzu da nake jin 'kaunar yaron nan ba zaan iya yin kyauta da 'da ba, koda na haifi guda goma. Ba abin da zance miki, sai fatan alheri, Ubangiji ya fini yabawa". Ta saba 'danta ta fice da shi, sai lokacin Sa'a ta fashe da kuka, tana jin girman 'karfin halin da ta yi. Ya dinga rarrashinta. Ta ce "shikenan Farida ta haihu, ta sami 'da Kamar Jawad! Sai ka daina takura shi sai ya je wajenta ya kwana, sai ka daina wannan tausayinta da yake neman zame mini barazana". Ya sake rungumeta tsantsan yana gasgata dinbin sonsa take yi, ya sani ba macen da take sonsa a doron 'kasa irin Sa'adah, idan aka cire Hajiya. Ya sani saboda tausayin Farida da yake yawan yi ne, ya sanya ta bada abin da yasan ba kowacce mace ce zata iya yin hakan ba. A fili ya dinga "cewa Madallah da ke Sa'adatu, a yau na sake ganewa ke din jarumace, mai kuma 'kaunata ce, zan sake maimata miki abin da na ce ba zan sake fa'da ba. Wallahi ban taba son wani abu a duniyata kamar ke da 'Yay'anki ba, Wallahi kune farin-cikina, kune duniyata, har na daina numfashi kece jagorar zuciyata. Ya rasa mai zai yi mata, sai ya ce ki shirya Gobe na kai ki gida, ki yi sati uku Inna ta sake gyara mini ke, kafin ba'di ina fatan ki haifo na ki wadda zaki ri'ke a hannun ki, a dakinki". *Wattanni shida a gaba* Zuwa lokacin Sa'a na dauke da wani cikin na wata biyar, yayin da yaron Farida mai sunan Mahaifinta Nasir(Amir) ta yi masa alkunya, yake wattanni shida. Yaron ya yi wani irin girma gashi fari kwal saboda farin Mk ya yi, sannan yana shan nonon farar mace, sai ya sake zama tamkar dan larabawa, irin ku'din da Farida take narkawa akan yaron abin tamkar a littafi, albashinta akan yaron yake karewa, haka Mahaifanta duk fitar da zasu yi sai anyi masa akwati guda, hatta Sa'a dalleliyar mota mahaifin Farida ya aiko mata a matsayin tukuicin sanya farin-ciki a zuciyar diyarsa. Shayarwa ba karamin karabar Farida ya yi ba, idan Sa'a tana ganin status din Farida da 'danta wani lokacin har kusan shidewa take yi tsabar kishin yadda suke daukar ido, domin komai designer take masa amfani da shi, yaron ya zama one in town. Haka fita goma shiga goma zata ganshi a kafadar Mk. Idan ya shigo da shi ta mika masa hannu sai ya ki, 'kiwa yake yi mata ba Yar kadan ba, tunda ko wurin aiki da shi Farida take tafiya da mai rainonsa. A wannan lokacin Mk ya kalallame Sa'a ta ajiye aikinta, ta zama lauya mai zaman kanta, a lokacin kuma tafiya zuwa kasar Amurka ta taso masa inda zai yi kwas na wattanni shida. Ya tisa Sa'adah ya tafi da ita. A can ta haihu still dai boy, ta saka rai girl zata samu sai dai Ubangiji ba hakan ya so ba. Sun more sosai a a zamansu na wattanni shida a U.S. Ta dawo da d'anta mai kama da ita wadda Baffah(Bashir) aka yiwa takwara Jawad ya ce *Jadid* za'a dinga ce masa. *Shekaru biyu a gaba*. Hankali kowa ya kwanta arziki da cigaba sai sauka yake yi a gidan Mk! Mussaman da ba'a yi masa tashin hankali, duk da kuma basa shiri. Dan hatta Amir har yau bai wani sake da Sa'a ba, idan Mk ya zo da shi baya yarda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157