Chapter 84
Chapter 84
a gajarce, sannan mafi yawan hirar sai dai ita ta kawo. Haka suke wannan zama har Jawad ya dawo daga gidan Samira, so take ya barta ta je Gombe amma tsoron tambayar ta ke yi, har mamakin kanta take yi, yadda take tsoron su yi rikici yanzu. Washagari alhamis da safe ta tura Jawad ya tambayo musu za su je su gaida Maman Gombe da ganin Baby boy, tunda sai satin sama hutun su zai 'kare. Jawad bai jima da zuwa ba, ta ji Mk na 'kwalla mata 'kira, gabanta ya fadi sosai da hanzari ta shiga dakin tana cewa" Na'am". Kallonta kawai ya yi, ta gane ba zai barta ba, ta tsugunna tana sauraronsa. Sa'a an 'kara kwas na respect 😁 "Kin aiko Jawad za ku Gombe, inace dama ban hana ki ba tun farko?" Ta yi sukuri tana jin fargaba na kamata, da 'kyar ta bude baki ta ce " ai kace ba zan ga alheri ba". "To yanzu na ce ki ga alherin! Aje lafiya, adawo lafiya shikenan?" Ta kalle shi ta ga yana daddana waya hankali kwance. "To kwana nawa zamu yi?" "Sai kin gaji da zama sannan ki dawo". Ya fada hankalinsa na kan wayarsa. Hawaye ya cika idonta tana jin tamkar ta sume. Murya na rawa ta ce "Malam yanzu fa ban yi maka komai ba, Allah shine shaidata, na yadda na ke gudun na 'bata maka, amma kai kwata kwata ka yanke mini kauna, ka ki ka yafe mini, kana zaune da ni akan tilas.." Kuka ya kwace mata sosai, cikin ko in kula ya ce "kin so yin kuka ne, kince za ki je Gombe, nace adawo lafiya, har da abin arzikin ki yi iya adadin kwanakin da kike so, shikenan kuma sai ki bare mini baki, to fada mini me kike so na ce miki?". Ta dago da manyan idanuwanta da suka yi ja ta zuba masa akan fuskar sa, tsawon lokaci idanuwansu a sarke, chemistry na aiki akansu, a sanyaye Mk ya janye fuskar sa gefe daya, yana kokawa da abin da ya taso masa. A hankali ta furta "so nake ka ce kwana kaza za ku yi". "To sati hudu ya yi miki?" Da mamaki ta kalle shi ta ce"ai zuwa wannan lokacin su Jawad sun ' dade da komawa school". Kai tsaye ya ce "Ba da shi za ki tafi ba ai, ke 'kadai za ki yi tafiyar ki, ki je ki yi abin da ki ka ga dama". Jikinta ya yi sanyi ta tabbatar ba barinta zai yi ba, sai kawai ta mike ta ce "Na gode". Ta fita zuwa kicin, ta hau aikin abincin rana, ta na yi tana kuka, bata ta'ba sanin Mk na da ri'ko ba sai a wannan karon. Haka tana ji tana gani har Inna ta dawo ba ta je ta gano su ba. Ko zuwa ta yiwa gidansu dan ta yiwa Inna barka da dawowa, da 'kyar ya barta, shima sai da la'asr lis da zai tafi shago ya tafi da ita, kafin su Isa magariba ta yi, amma dan son ya musguna mata bata fi awa daya ba ya mata waya shi zai tafi, idan kuma bata gama ba, ta taho idan ta kammala, alhalin yana kaiwa fiye da goman dare. Haka ta fito ta bishi yana ta cin magani, har suka iso ko uffan ba suce ba, wannan sabuwar rayuwar ta yiwa Sa'adah tsauri matu'ka da gaske mussaman da bata saba ba, ya riga ya sabar mata da wasa da raha, uwa uba kullum shine cikin rarrashinta da son ganin murmushi a fuskarta, shiyasa yanzu sauyin ya zo mata da tashin hankali. Hatta Inna sai da ta yi 'kwalla da taga irin ramar da ta yi, sai dai fa'da sosai ta mata tana fadin tasan itace duk ta jànyowa kanta komai take ciki. Cikin kuka ta ce "Ni damuwata 'daya yadda Anty zata ga rashin kirkin banje na gaishe ta ba". Da sauri Inna ta ce "ba zata ga laifinki ba ai tasan aure ki ke yi, ba zaman kanki ba, kar ki damu ta warware sosai, Ba ki ga Anis ba ya yi 'bul'bul da shi, ki bi mijinki a hankali kin ji". Haka suke rayuwar yau fari gobe tsumma, shi kansa Mk so yake ya manta komai amma maganganunta sun dasa masa wani irin ciwo a zuciyarsa, sun yi karfin da suka sababa masa hawan jinin da yake shan magani kullu yaumin, idan ya tuna sadda ta ke fada masa matan bariki na da daraja fiye da matan aure sai ya ji tamkar ya sume. Ranan asabar da safe suna karyawa da wainar shinkafa da miyar ganye da ta ji tantakwashi, sammako ta yi ta shirya masa tare da kunun farar shinkafa da danyar gyada, tasan yana son wadannan abincin, sai da ta yi wanka ta ci kwalliya sosai sannan ta gabatar musu. Suka kammala ta kwashe komai, ta zauna kusa da shi sosai, a ladabce ta ce "Malam ina son na je asibiti". Ya kalleta ya ce,"me za ki yi? Ta sunkuyar da kanta 'kasa ta ce " abin nan zan cire ". Ya zuba mata ido yana jin tausayinta na neman kama shi, yasan so take ta yi abin da zai sa shi farin ciki, dan haka sai ya sassauta ya ce "Inace tun a Abuja na ce ki bari mu gani tukun, ko abin da nake fata zai kasance, idan ki ka haihu kun zama ku uku lissafi zai canja". Ta dago idonta cike taf da hawaye ta kalle shi " Na dauka ka fasa tafiyar da ni, tunda yanzu ka canja mini akan komai". Ta fa'da hawaye yana zubo mata. take ya ji sonta ya dawo daga suman da ya yi, Ashe son ba raguwa ya yi ba, comma ya shiga. Ya bude mata dukkan hannuwansa biyu, a yau bata tsaya jan aji ba, da sauri ta fada masa, yasa dukkan hannuwansa ya rungumeta tsantsan ita kuma tana kuka kasa kasa. Baice komai ba, illah shafar bayanta yana jin sau'kin 'daurin da kirjinsa ya yi akanta. Tun daga ranar ya canja, ya daina 'daure fuska, sannan ya bu'de mata kofar nisha'di a tsakanin su, sab'anin satikan da suka shude da ya rufe ta rif. Saukowar Mk ya sa ta fara murmurewa, tashin hankalin da ta shiga yasa ta manta da wayar ta Bb, sai yanzu da ta sami nutsuwa take fitowa da ita, idan ya fita. * Tsautsayi* Ranar da ta zama 'bakar Rana ga rayuwar ma'auratan guda biyu, wadda tarihin rayuwar su ba zai cika ba, sai an sako ranar. Asabar ce cikin watan Augusta da safe bayan sun kammala karyawa cikin walwala, ya shirya ya mata sallama, zai je ta'aziya Baban Abokinsu ya rasu daga nan zai zarce gidan su ba zai dawo ba sai yamma, ta masa addu'ar dawowa lafiya,ya tafi tare da Jawad. Kafin ya fita ta nemi iznin za ta je kitso, bai hana ba, ya amince mata. Sai da ta gama komai na gyaran gida, ta yi wanka, ta tsaya jikin wardrobe tana nazarin rigar da zata sanya. Wata daguwar riga ta janyo data jima bata sa ta ba, garin janyowar ta hado da ledar kayan da su Halima suka kawo mata na tsarabar khalil, wadda ta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31
- 32 Chapter 32
- 33 Chapter 33
- 34 Chapter 34
- 35 Chapter 35
- 36 Chapter 36
- 37 Chapter 37
- 38 Chapter 38
- 39 Chapter 39
- 40 Chapter 40
- 41 Chapter 41
- 42 Chapter 42
- 43 Chapter 43
- 44 Chapter 44
- 45 Chapter 45
- 46 Chapter 46
- 47 Chapter 47
- 48 Chapter 48
- 49 Chapter 49
- 50 Chapter 50
- 51 Chapter 51
- 52 Chapter 52
- 53 Chapter 53
- 54 Chapter 54
- 55 Chapter 55
- 56 Chapter 56
- 57 Chapter 57
- 58 Chapter 58
- 59 Chapter 59
- 60 Chapter 60
- 61 Chapter 61
- 62 Chapter 62
- 63 Chapter 63
- 64 Chapter 64
- 65 Chapter 65
- 66 Chapter 66
- 67 Chapter 67
- 68 Chapter 68
- 69 Chapter 69
- 70 Chapter 70
- 71 Chapter 71
- 72 Chapter 72
- 73 Chapter 73
- 74 Chapter 74
- 75 Chapter 75
- 76 Chapter 76
- 77 Chapter 77
- 78 Chapter 78
- 79 Chapter 79
- 80 Chapter 80
- 81 Chapter 81
- 82 Chapter 82
- 83 Chapter 83
- 84 Chapter 84
- 85 Chapter 85
- 86 Chapter 86
- 87 Chapter 87
- 88 Chapter 88
- 89 Chapter 89
- 90 Chapter 90
- 91 Chapter 91
- 92 Chapter 92
- 93 Chapter 93
- 94 Chapter 94
- 95 Chapter 95
- 96 Chapter 96
- 97 Chapter 97
- 98 Chapter 98
- 99 Chapter 99
- 100 Chapter 100
- 101 Chapter 101
- 102 Chapter 102
- 103 Chapter 103
- 104 Chapter 104
- 105 Chapter 105
- 106 Chapter 106
- 107 Chapter 107
- 108 Chapter 108
- 109 Chapter 109
- 110 Chapter 110
- 111 Chapter 111
- 112 Chapter 112
- 113 Chapter 113
- 114 Chapter 114
- 115 Chapter 115
- 116 Chapter 116
- 117 Chapter 117
- 118 Chapter 118
- 119 Chapter 119
- 120 Chapter 120
- 121 Chapter 121
- 122 Chapter 122
- 123 Chapter 123
- 124 Chapter 124
- 125 Chapter 125
- 126 Chapter 126
- 127 Chapter 127
- 128 Chapter 128
- 129 Chapter 129
- 130 Chapter 130
- 131 Chapter 131
- 132 Chapter 132
- 133 Chapter 133
- 134 Chapter 134
- 135 Chapter 135
- 136 Chapter 136
- 137 Chapter 137
- 138 Chapter 138
- 139 Chapter 139
- 140 Chapter 140
- 141 Chapter 141
- 142 Chapter 142
- 143 Chapter 143
- 144 Chapter 144
- 145 Chapter 145
- 146 Chapter 146
- 147 Chapter 147
- 148 Chapter 148
- 149 Chapter 149
- 150 Chapter 150
- 151 Chapter 151
- 152 Chapter 152
- 153 Chapter 153
- 154 Chapter 154
- 155 Chapter 155
- 156 Chapter 156
- 157 Chapter 157