Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,202 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ra'ayin Sa'adatu ya kerewa mu'amala da irin su Zainab. Saboda haka sai yafi matsa mata, kullum da kalar tambayar da zai mata, wadda kesa ta muzan ta. Abin da ya lura dashi bawai 'ko'kari ne Sa'adatu ba ta da shi ba, illah mai da hankali ne ba ta yi. sannan kuma tana da (infiority complex). ma'ana rashin 'kwarin guiwa akan kanka, tunda ya gane tsoron kar a mata dariya yasa ba ta son yin magana da turanci. Wannan matsin da ya mata sai ya janyo tsanar shi a ranta, ta shiga fargaban zuwan period 'din shi, a haka har akayi jarrabawar gwaji(Test). ganin a kowanne darasi bata ta'buka ko mai ba sai shiririta, sai ya canja salo ya fara disgata a gaban aji, ta hanyar 'kiran ta da sunaye kala kala, da suke nuni da ba abin da ta sani sai dai ta wanke uniform, ta yi yanga, amma empty brain, har cema ta yake bata dace da wannan makarantar ba. Sannan kullum cikin bada misali da za'kwa'kuran dalibai masu azama yake, takaicin ta 'daya, yadda kullum misalin sa ba ya wuce da Farida Nasir Torodi , tun fil'azal ita jinin ta bai hadu da Farida ba, duk kuwa da ba ajin su 'daya ba, Farida a A, science class kenan, doguwa, siririya sosai, fara 'kal buzaye ne, gashin ta har gadon baya, farkon zuwan ta makaranta har nuna ta ake, na yadda ta ke tuma a cuci a kanta saboda idan ta tufke gashin yake girma, sai a hankali aka gane gashin ta ne. Mai sanyin hali ce ko kadan ba ta da kwarafniya, bata kuma harkar 'kawaye. 'Kawar ta 'daya wadda kullum zaka gansu tare Ru'kayya mustapha. Ga ilimi kamar me, dan kuwa tana cikin 'yan gaba gaba na 'dalibai masu haza'ka a duk fadin makarantar. Sannan iyayen ta ma su wadata ne, domin mahaifin ta ambasadan Niger ne a Nigeria. Wadannan abubuwan da Farida ta hada sai wasu cikin dalibai su ke mata kallon mai girman kai, da 'daukar ita wata ce yasa take ganin ta wuce kula su, shiyasa suma basa wani harka da ita ba ta da farin jini a tsakanin set dinta. barin ma da 4stars da suke ganin sai dai ta nuna musu kyan fuska amma ba dai na jiki ba😀. Yawan misalin da yake yi da Farida ya 'kara tsanar ta a zuciyar Sa'adatu. Cikin abubuwan da ba zata manta suba indan har za ta tuna rayuwar ta a FGC KANO, shine ranar da ya musu dictation wato yana fa'da suna rubutawa, ita kuma slow writer ce, kafin ta kammala rubuta wata kalmar, ya fadi ta gaba, kan dole ta ha'kura da bin, ashe yana lura da ita. Sai da ya gama ta ji ya kira sunanta"Sa'adatu Bashir where's your note?" Cikin daburcewa da tsoron yadda zai kunyata ta, murya na rawa ta tattaro kalaman da zai fahimce ta a gajarce ta ce "My pen stop" kafin ya yi magana anyi attishawa mai 'karfin gaske wadda ta iya shege ce, ba kowa bane illah Fahad Auwal! wadda shima haushin yadda ta za'bi Khalil ta barshi ne yasa yake jin da'din dizgin da ake mata. Hannu ya mi'ka yana cewa "let me see" zuciyarta ta buga amma hakan nan ta mi'ka mishi biron, ya duba ya ga lafiyar biro 'kalau ya watsa mata kallo tare da cewa "out of my class! I am tied of your manners" ta mi'ke sai kuma ta tsaya tace "Am sorry" cikin tsawa yace "don't sorry me, say sorry to ur parents who are keep westing their money". Jin haka yasa ta fita, hawaye ya cika idonta, a baranda ta tsaya amma sai ya le'ka yace mata "on your kneels" kuka sosai ya kwace mata . A ranta ta na tambayar kanta me ta mishi ne ya ke wula'kanta ta? mai yasa ya matsa mata? saboda ba ta da 'kokari ne dalilin? ta ke ta ji in dai 'ko'kari zai sa ta tsira da mutunci a idon wannan mutumin da ya yankewa tozarci cibiya to kuwa za ta nemo shi a ko'ina yake. Sai da ya kammala darasinsa sannan ya fito ya kalleta yace "I want you to borrow your boyfriend's note, and copy what you can't write by urself, if not u will be in.." ya girgiza kan shi ba tare da ya fadi mai zai biyo baya ba . Ya wuce ta yana sa ke fadin "useless girl, you can go back to ur class". Tsawon lokaci ta shafe a gun tana kuka tsabar ba'kin ciki zuciyarta Kamar ta fashe, har sai da ta hango Mr uche's wadda ya ke 'daukan su darasin tsumi da tanadi(economics). sannan ta mik'e ta na kar ka'de jikin ta, ta shige ajin ta na ganin wa'danda dama su na jin haushin su, ita da 'yan group din su, su na bin ta da wani irin kallo, mai kama da madallah. AL'KALAMIN SURAYYA DAHIRU ✍️✍️. [5/20, 16:04] +234 806 791 2288: 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 •·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·•·•·• *_LAFAZI WRITERS ASSOCIATION ®_* ✍️ ─────────────────────── ```{Kyakkyawan lafazi a cikin rubutu yana ɗamfare da bin ƙa'idar Adabin Hausa.``` ```Lafazi gidan karamci da mutuntaka, Harshenmu abin alfaharinmu.}``` ✏️✏️✏️ ____________(✪)______________ https://mobile.facebook.com/Lafazi-Writers-Association-104448621878916/ •·•·•·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·••·•·•·•·•·•·•·• *SADAUKARWA GA* *SADIK ABUBAKAR*. *Fatan alheri ga marubuciya* *Zainab Ilyas Mazawaje*. 23_24. Tsananin matsin da Uncle Mukhtar ya mata yasa ta zama shiru shiru, ta matu'kar rage kaudi da iyayyi. Kullum tana ri'ke da littafan koyon turanci, ire-iren su Teach ur self. Ta sake mannewa Safina Bunkure. kasancewar Safeena girman Lagos ce, mafi yawan maganarta turanci ne, dan haka ba ta yarda su yi magana da hausa tare da safina, itama kuma Safina ba ta gajiya da gyara mata a inda ta ji ta yi kuskure. Ba'a dauki lokaci mai tsayi ba,ta fara rage tsoron kar ta yi turanci a mata dariya, ganin ta na iya mayar da magana cikin harshen da ke mata nauyi, sai kuma ta mai da hankali akan ragowan darussan gaba 'daya. Ta matu'kar rage shiririta, yanga, da hirar soyayya, da duk wata sharholiyar da su ke, abu 'daya ne ba ta bari ba, kwalliya, wadda wannan kam a jinin ta ne. Su Halima cewa su ke basu ga Malamin da zai uzzura mu su, babu dalili basu yi maganin sa ba. Ita ko tsaki take ja a fili, ta yi shiru. A zuciyarta ko cewa take ai ku ya ga kun iya turanci, kuma yana ganin yadda ake zuwa 'daukan ku a motoci na garari, ni kuwa ya ga ba ko 'daya, ba dole kowacce shara ya debo ya juye a kaina ba. Tabbas tana takaicin yadda ita kadai ya ke gallazawa. Shikuma ganin yadda ta yi laushi ta kuma maida hankali kan karatun ta, sai ya sassauta mata, duk kuwa da zai yi wahalar gaske ya yi darasi bai ce ta tashi tayi bayanin yadda ta fahimci darasin ba, kawai dai kyara da disgin ya rage. A haka har suka yi jarrabawar mock wadda duk 'dalibi ya ke tsoro da fargaban kar ya fa'di. Ana yin hutu da kwana biyu mijin Sumayya ya turo takanas a dauki kannen shi 'yan mata guda biyu da yar autar dakin su, da kuma wadda suka hada uba yar amaryar Baban su, sai ya ro'ki Baffah! akan ya basu Sa'adah ta yi musu

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});