Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 69

Chapter 69

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,200 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wani iri? ke da kike kanwata nasan kina jin ba dadi, bare ni ki gatsa sunana gatsal" "Amma ai tun ranar ban sake fada ba". "Eh baki sake ba, sai dai kimin ta kurame, kiyi maganar ki ba tare da kin kama sunana ba". "Nifa Wallahi na tsani, waccan sunan da kake kulafacin sai na cigaba da kiranka da shi". "To shikenan zabo min wani, mai sweet, kika rufe ido kika cemin wai baki hada dangi da Ni ba ko?" Ta ce "eh mana ai ba karya na fada ba". "Ni Malamin ki, Ni Mijin ki,Ni Baban danki, duk wannan ha'din kin raina shi?". Ta tura baki gaba, ta ce "shikenan, ka zabi sunan da zan fada maka a cikin wadannan,Malam, Miji, ko Uban 'da" Dariya ta kwace masa sosai, cikin dariyar ya ce, "ke yanzu sai ki dinga cemin Uban 'da?" *Surayya Dahiru* ✍🏼✍🏼✍🏼 26/03. 🌺 *HALIN YAU*! 🌺 *Lafazi writers*. *A guji taba wannan labarin ba tare da izinin mai Hakkin mallaka ba* *Doka mai lamba ta 68 ta nuna cewa satar fasaha laifine da yake dai-dai da satar Dukiya*. *GODIYA* *Ina matu'kar godiya ga wadanda suka yi mini addu'o'in samun lafiya ga warwarewar lamura, tunda ga kan masu kira ta waya, da masu text, da masu yi mini ta dandalin WhatsApp, dukkanku na gode madallah, ubangiji ya fini yabawa*. 65-66. Ta yi murmushi ta ce " mai zai hana na fada maka idan kana so?" Ya bugi sitiyari ya ce "my sweet Sa'adah, sometimes you are so funny". Ta yi shiru ta kyale shi, ya sake cewa " ke yanzu ko inkiya da Jawad baza kimin ba, naga yanzu daga mace ta haihu take karawa Mijin ta matsayi ta hanyar yi masa alkunya da sunan yaronsu". Ta tabe Baki, ta yi shiru, sai kuma ta kasa hadiye maganar. "Akan mai zan maka alkunya da Jawad alhalin wadda ta fini cusa kai ta riga ni? Inace Farida Abban Jawad take kiranka? Kasan Ni kuwa har abada bazan bi ra'ayin ta ba, banda azarbabi, ba sai ta bari idan ta haifar maka nata sai ta yi komai ba, amma dan son sai ta nuna ita gwanace akan kayan da ba nata ba yasa ta ke yi mini katsalandan, ai na so ta yi kataborar ce min Iyah Basiru, wallahi da jikinta ya fa'da mata domin kuwa ba abin da zai hana na mata 'kamshin mutuwa". Ganin za ta tunzuro da yawa sai ya share maganar da cewa "Na zabi miji, amma Zauj za ki dinga fad'a maimakon miji". Yana rufe baki ta ce " duhun fata ta kadai, ya isa ka gane ni ba balarabiya bace, dan haka nafi kishin yarena". "Amma duk musulmi dole ya dau larabci yarensa ne, domin yaren kura'ani ne, duk sallar duniya kuma a larabce muke yinta". "Wannan daban" ta bashi amsa a takaice, daidai lokacin kuma suka iso gida. A gidan ma maganar ya yi ta ja, inda ita tace Malam ta zaba, dan haka Malam zata dinga fada. "Na fada miki ban son wani Malam, duk sunayen zamani, da na soyayya ki rasa mai zaki ce mini sai Malam sai kace tsoho ko wani Malamin zaure, duk yadda muke da ke darajata a iya ta Malami take a gurin ki?" Tana dariya tace "kololuwar daraja kenan, Malaminka ai tamkar mahaifi ne, ana canja Miji, amma ba a canja mahaifi da Malami, domin ko ka guje shi, ya dai koyar da kai abin da baka sani ba, sannan ya koya maka tarbiya, a wurina Malam is a jewel. Shikenan mafarin cemasa Malam tun yana ki, har ya fara amsawa, a lokacin da Jawad ya fara iya magana shima ya bi bakin uwarsa wurin kiransa da Malam. Juyin duniya ya yi da Jawad kar yace masa Malam, amma da ya fara cewa Daddy, idan yaji Sa'adah tace Malam shikenan shima zaice Malam. Sai ya fara cemata Daliba, ko abune sai ya bawa Jawad yace humm kaiwa Daliba, a kokarinsa na itama Jawad ya dinga kiranta haka😂 Amma sunan bai bita ba, sabanin shi da Malam ya zauna a bakinsa radam, ita kuwa Mami yake kiranta. Tun lokacin Mk yake yiwa Sa'adah mitar yasan Jawad yafi sonta da shi, itakuma dariya yake bata idan yana wannan rikicin nasa.wataran tayi dariya, wataran tace haba Malami na. Sai ya yi murmushi yace "A da nake Malamin ki". Tace "har yau Malami na ne, tunda har yanzu karatu nake yi a gabanka". "Wanne karatun kike yi yanzu?" Tace " da ka koyar da Ni, ilimi da tarbiya, yanzu kuma kana koya mini karatun kyankyansar jarirai". Tana fadin hakan ta gudu ta barshi, ya bita yana dariyar maganar ta karshe, wai kyankyansar jarirai? ya zauna kusa da ita yana cewa "ai kuwa dai kin yi gaskiya, Ni yanzu ma so nake mu zama mu hudu, ya kamata kije ki cire abinnan, mu fara sabon karatun kyankyansar jariran". Tana dariya tace "ka rufa min asiri kai da kace sai na fara karatu, na yi nisa, da ka sake yi min ciki?". Yana dariya yace "da bakin ki Kika fadi wannan maganar?" Ta rufe ido tana Jin kunya na kamata. Ya zauna kusa da ita yace "kisan dai kin yi jamb, kyau ne bata yi ba, nace ki cike F.C. E. Kin kasa fahimta ta, da yanzu za ki fara N.C.E, kinga yanzu dole ki sake zaman jiran wata shekarar, maimakon haka gara mu sami Baby, ai akwai masu karatun da goyo". Shiru ta yi, itama tana son haihuwar yanzu, mussaman idan ta tuno fuskar baby girl dinta da ta rasu mai kama da ita, sai ta ji ta zaku da ta sake haihuwa, tasan da ta rayu, da ta nan tana tafiyarta ko ina. " Ance mini idan Ina haihuwa rututu ba barina zaka yi na yi karatu ba?" "Ni kuma nace za ki yi, har sai kince ya ishe ki, shin maganar wa za ki dauka, tawa ko ta su?". "Shikenan zan cire, amma yanzu ka manta Jami'an lafiya na yajin aiki?" " Na manta, idan su koma bakin aiki sai muje a cire ko?" Ya fada cike da kulawa da rarrashi. Su Halima na zuwa ta fada musu, Malam yace ko da goyo zata yi makaranta, karatu har sai ya isheta. Safina ta kaikaice tace "wato ya ga kin yi kyau, kin bar Sa'ade kin dawo Sa'adah, shine zai sake dirka miki wani cikin? ke kuma har kin yarda da maganar sa?" Suka kwashe da dariya, Halima tace "na rantse miki da Allah karya yake miki, barinki ne ba zai yi ba, kar ki sake ki cire abin nan sai kin tabbatar kin fara makaranta, tunda shi son haihuwar yake, sai ki yi amfani da hakan ki cimma burin ki". Sa'adah ta yi shiru amma bata fahimci bitar Halima ba. Tace "kamar ya ya na cimma burina?" "Eh tunda so yake ki cika masa gida da Yara, sai ki kafe, ba za ki haihu ba, sai ya nemo miki admission, idan har da gaske zai barki, maki uku ne kacal ya hana points dinki su kai, da ya so, da tuni ya samo miki admission, lakcara ne fa, Yana da alfarma wallahi". Safina tace "Ai ni bansan wadda ya iya rainin wayo irin Man din nan ba, mugun

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});