Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 102

Chapter 102

Halin Yau Book 1 Complete Hausa Novel 1,199 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

suka fa'da miki Ni 'din banza! sai kika karba, mussaman da suka nuna miki idan ma na rabu da ke ga wadda ya fini 'kuriciya da kudi yana son ki ko?" Ganin yanayinsa ya sake tada hankalin Iyah, saboda rikici ne zallah cikin idanuwan sa irin wadda bata ta'ba gani a tare da shi ba. Da sauri ta ce "Wallahi Malam.." Ta yi shiru sakamakon harar da ya watsa mata ya ce "Idan kika 'karyata ni wallahi zan miki duka, ki kiyaye ni". Ta yi shiru sai kuka kawai ta ke yi wadda Mk har cikin zuciyar sa yake jin kukan, ya yi shiru yana sauraron kukan, sai ya dinga jin ashe har da kukanta cikin abubuwan da yake kewar su a tare da ita. Tana rerewa yana tuna sadda take tisa shi a gaba tana masa kukan iyashege ko na shagwaba. Tsawon mintina biyar kafin ya yi karfin halin cewa "Kinga idan iyakacin maganar kenan tashi ki tafi tunda kuka kika zo yi mini". Ta shiga goge fuskar ta kafin ta yi 'karfin halin hadiye kukan ta ce "Kai ka ce duk sadda na shirya fa'da maka gaskiya, zaka saurare Ni fa". Ya zakudo yace "eh na fa'di haka, amma ai ke yanzu bansan gaskiyar ki ba, sau nawa kina canja mini baki, da me zan dogara har na gamsu?" Ta zube a gabansa kan guiwowinyata ta ce "Billahillazi iyakar gaskiyar kenan ubangiji shine shaidata". Ya yi shiru! Bai ce komai ba illah fama da yake da zafin zuciya. Cikin rawar murya ta ce "Ina ha'da ka da girman Allah da Ma'aiki ka yafe mini, ka mayar da auren mu, gobe kafin ka 'daura da wata jibi, na yarda na amince, ka yi auren har ma ka tafi da ita, Ni ka barni anan zan jiraka, na cigaba da amsa sunan matarka shine kwanciyar hankali na! Wallahi tunda ga ranar da ka sake ni Malam har yau ban sake barci da Ido biyu ba, me yasa ba zaka gasgata ni ba?". "Sa'a ta ya ya zan gaskata ki alhalin ke baki gaskata kan ki ba? Ke ce kika janyo komai, ke kika cusa mini rashin aminci game da lamarin ki". Murya na rawa ta ce baka aminta da Ni ba fa ka ce?" Kai tsaye ya amsa "kwarai da gaske Sa'adatu, menene alakar ki da Khalil da zai baki Agogon gold? kin tattauna da kawayen ki na kasa siya miki wayar da kike so, ke kika san tsiyar da kuka yi , ya mallaka miki kayayyaki masu daraja tamkar ke din yantacciyar mace ce". Ta rushe masa da kuka tare da ru'ko kafarsa ya kwace da sauri. "Kar ka zarge ni da abin da baka da tabbaci, kar 'bacin rai yasa ka daukarwa kanka zunubin da ba zaka iya daukarsa ba". Ya mike da sauri, a fusace ya nuna ta da dan yatsa ya ce "ke kika haskaa mini kofofin zargin ai, akan wanne dalili zai baki Agogon gold?" Da waya mai tsadar gaske?" Murya a dakushe saboda da kuka ta ce "English gold ne Malam! Bai kai darajar Dubai gold ko Saudi ba" "Amma dai me daraja ne? tunda a lokacin ai ba zan iya siya miki ba. Bayan haka me ya hana ki bu'de mini wayar? Me kuke yi da ba kya so na gani, ha'inta ta kawai kike yi Sa'adatu, dama ance yanzu mata ta waya ma suna tura tsaraicin su ga shedanun mazan da basu san darajar mace da kuma aure ba, bare wannan 'Dan iskan yaron da bani da tabbacin aure ne ya kawo shi duniya". Ya yi shiru saboda yadda kirjinsa ke masa ciwo. Ido Sa'a ta zuba masa, ta jima tana kallon shi, tana jin wata irin jarumta na shigarta, ido cikin ido tace "wannan dalilin ne yasa ka kasa mini afuwa, ka kasa kallon nadamata, ka kasa yi mini alfarmar cigaba da zama matarka da kuma rayuwa tare da Jawad?" Ba ja in ja ya sake cewa "kwarai da gaske ai dama na ta'ba fa'da miki, ba zan sake miki uzziri akan dan'iskan yaron nan ba, ashe a lokacin ma abin na ku da tsabta". Ya zarce da fa'din "dama yanzu ai anfi lalata da matan aure saboda kome aka kwaso kai-tsaye za'a likawa mijinta ya yi ta wahala da abin da ba nasa bane, ko ayi ta masa sharing matarsa hankali kwance, tunda darajar aure ya bata dukkan kariya daga jifan da zai ta'ba mutuncinta dana ahalinta". Wani irin abu mai tsananin nauyi ya tokare a wuya da zuciyar Sa'a, hawaye mai zafi ya balle mata, ta mike tsaye, ta sake zuba masa ido ta ce "Na gode da dukkan dawainiyar da ka yi da ni har ya zuwa yau, ina maka fatan alheri a sabon aurenka, Ina fatan ko wacece ta kasance abokiyar arzikinka ce". Kuka ya nemi subuce mata, amma ta sa dukkan dauriya ta danne shi, ta yi shiru, na dan sakwanni goma, sannan ta dora da cewa "A yau na tabbatar komawa gareka ba alheri bane, domin cikin shekaru hudu ba yan waattani kullum a cikin sallar dare nake, ba abin da nake ro'kar ubangiji sai ya 'kaddara ka mayar da auren mu, duk satin duniya sai na yi azumi biyu, idan na zo buda baki ba abin da nake ro'ka irin na koma dakin ka". Anan kuma sai kukan ya gwada mata fin karfi ya kwace ta sunkuyar da kanta 'kasa tana kukan sosai, a zuciya kuma sai ambaton*Hasbunallahu wa Ni'imal wakil* take yi! Ai kuwa ta sami sau'ki sosai . Yana tsaye yana kallonta yana jin tamkar yasa ruwa da omo ya goge tsatsar da ta yiwa zuciyarsa, Amma ya kasa, ya tabbatar kishi ne ya rufe masa ido, fasa wayar nan da ta yi means a lot to Him. Kanta na kasan ta bude murya ta ce "Na yarda da kalaman ka na cewa mu kan so abu alhalin sharri ne, haka nan muna kin abu alhalin alheri ne, na gamsu sosai tunda har Kai da ka tabbatar kaine mutum na farko da ya fara taka ta, amma ka kasa kubutar da ni daga sake saken zuciya da na shaidan. Idonta a soye ta ce "shin ka gamsu Jawad 'danka ne ko kuwa kana tantamar li'ka maka na yi kake ta wahala da shi alhalin ba jinin ka bane?" Da rawar jiki ya dunfare ta ba zato ta ji ya faskawa bakinta mari mai zafin gaske har sai da jini ya fara fitowa tabbacin ya fasa mata shi. Cikin gajiyawa da neman sulhu ta ce "wannan shine kawaicin da zan maka na karshe akan 'daga mini hannu da kake yi, kuma dole na tambaye ka, idan shima a Ballagazancin da ha'incin na samo shi, sai ka dawo mini da 'dana ni zan cike masa gurbin uba, tunda dama ai mutum baya rasa uwa sai dai uba, to ka bani shi kawai, domin ba 'danka bane! nawa ne". Kallonta kawai ya ke da tsananin mamaki, can ya nisa ya ce " Ashe kaifin harshen ki yana nan, ashe rashin arzikin ki na nan fal a zuciyar ki? No wonder na kasa yarda da gaske kin canja, yanzu na tabbatar da na mayar da ke din ma kina wartsakewa zaki 'dora da dibar albarkar da

Table of Contents

Chapters

157 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
  32. 32 Chapter 32
  33. 33 Chapter 33
  34. 34 Chapter 34
  35. 35 Chapter 35
  36. 36 Chapter 36
  37. 37 Chapter 37
  38. 38 Chapter 38
  39. 39 Chapter 39
  40. 40 Chapter 40
  41. 41 Chapter 41
  42. 42 Chapter 42
  43. 43 Chapter 43
  44. 44 Chapter 44
  45. 45 Chapter 45
  46. 46 Chapter 46
  47. 47 Chapter 47
  48. 48 Chapter 48
  49. 49 Chapter 49
  50. 50 Chapter 50
  51. 51 Chapter 51
  52. 52 Chapter 52
  53. 53 Chapter 53
  54. 54 Chapter 54
  55. 55 Chapter 55
  56. 56 Chapter 56
  57. 57 Chapter 57
  58. 58 Chapter 58
  59. 59 Chapter 59
  60. 60 Chapter 60
  61. 61 Chapter 61
  62. 62 Chapter 62
  63. 63 Chapter 63
  64. 64 Chapter 64
  65. 65 Chapter 65
  66. 66 Chapter 66
  67. 67 Chapter 67
  68. 68 Chapter 68
  69. 69 Chapter 69
  70. 70 Chapter 70
  71. 71 Chapter 71
  72. 72 Chapter 72
  73. 73 Chapter 73
  74. 74 Chapter 74
  75. 75 Chapter 75
  76. 76 Chapter 76
  77. 77 Chapter 77
  78. 78 Chapter 78
  79. 79 Chapter 79
  80. 80 Chapter 80
  81. 81 Chapter 81
  82. 82 Chapter 82
  83. 83 Chapter 83
  84. 84 Chapter 84
  85. 85 Chapter 85
  86. 86 Chapter 86
  87. 87 Chapter 87
  88. 88 Chapter 88
  89. 89 Chapter 89
  90. 90 Chapter 90
  91. 91 Chapter 91
  92. 92 Chapter 92
  93. 93 Chapter 93
  94. 94 Chapter 94
  95. 95 Chapter 95
  96. 96 Chapter 96
  97. 97 Chapter 97
  98. 98 Chapter 98
  99. 99 Chapter 99
  100. 100 Chapter 100
  101. 101 Chapter 101
  102. 102 Chapter 102
  103. 103 Chapter 103
  104. 104 Chapter 104
  105. 105 Chapter 105
  106. 106 Chapter 106
  107. 107 Chapter 107
  108. 108 Chapter 108
  109. 109 Chapter 109
  110. 110 Chapter 110
  111. 111 Chapter 111
  112. 112 Chapter 112
  113. 113 Chapter 113
  114. 114 Chapter 114
  115. 115 Chapter 115
  116. 116 Chapter 116
  117. 117 Chapter 117
  118. 118 Chapter 118
  119. 119 Chapter 119
  120. 120 Chapter 120
  121. 121 Chapter 121
  122. 122 Chapter 122
  123. 123 Chapter 123
  124. 124 Chapter 124
  125. 125 Chapter 125
  126. 126 Chapter 126
  127. 127 Chapter 127
  128. 128 Chapter 128
  129. 129 Chapter 129
  130. 130 Chapter 130
  131. 131 Chapter 131
  132. 132 Chapter 132
  133. 133 Chapter 133
  134. 134 Chapter 134
  135. 135 Chapter 135
  136. 136 Chapter 136
  137. 137 Chapter 137
  138. 138 Chapter 138
  139. 139 Chapter 139
  140. 140 Chapter 140
  141. 141 Chapter 141
  142. 142 Chapter 142
  143. 143 Chapter 143
  144. 144 Chapter 144
  145. 145 Chapter 145
  146. 146 Chapter 146
  147. 147 Chapter 147
  148. 148 Chapter 148
  149. 149 Chapter 149
  150. 150 Chapter 150
  151. 151 Chapter 151
  152. 152 Chapter 152
  153. 153 Chapter 153
  154. 154 Chapter 154
  155. 155 Chapter 155
  156. 156 Chapter 156
  157. 157 Chapter 157
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});